🎈🎀 *ZAMAN KISHI*🎈🎀
*WRITTEN BY*
*MOMYN MUSADDIQ/HYDAR*✍🏻*PAGE 16~20*
K'arfe biyar Kabir ya tashi a aiki ya wuce gidan su ya karb'o Ihsan sannan ya wuce gidan sa.
Tun a bakin k'ofar parlour ya fara cin karo da goran ruwa tsaki yayi ya shiga cikin parlour.
Plate da cukali ne a tsakiyar parlour sai ledan chocolates da tasha bata kwashe ba.
Nan ma baiyi magana ba ya shiga cikin d'akin ta.
Tana kwance da daurin k'irji ita kad'ai sai faman cika take tana batsewa.
Sallama yayi bata amsa ba hakan da tayi duk me dameshi ba idan dai zai samu ta karbi yarinyar nan.Zama yayi a bakin gadon yace
"Haba my Jiddah bansan ki da wannan halin ba fa,yanzu 'yar taki guda d'aya na tafi da ita Amman ko kira babu?"Tsaki taja masa still batayi magana ba sai gyara kwanciya da tayi ta juya mishi keya.
Murmushi yayi dakyar duk dan ya shanye b'acin ran sa.
Saman gadon ya hau ya kamo hannun ta yace
"Plss Jiddah kiyi hakuri ki karbi yarinyar nan sannan ki fad'i duk wani abu da kikaso zan Miki dan Allah ki kwantar da hankalin ki."Tunda Jiddah taji haka ta Mik'e zaune tace
"To abinda nakeso ka janye batun auren ka."
Murmushi yayi yace
"Banda wannan a ciki Jiddah kinsan bazaiyu na janye ba saboda auren kwana 28 ne ya rage ki kawo wani."Murmushin gefen baki tayi tunawa da safeeyah kawarta da tayi tace
"Ok kud'i kawai nake buk'ata."
"Indai kud'i ne bakiida matsala karbi yarinyar nan."Hannu tasa ta amsheta tana me sata a nono tace
"Sannan inason zaka chanza mun kayan parlour na."
"To Allah ya bani iko."Kallon sa tayi fuska a hade tace
"Bangane ba?"
Kallon ta yayi yace
"Kamar ya?"
"Kace Allah yabaka iko."
"Eh Mana sai Allah ya bani iko ai Jiddah""Ok yanzu kamun transfer ta acc d'ina."
Kallon ta yayi ya jijjiga kai sannan ya dauko wayar sa ya mata transfer kud'i 200k yace
"Na tura Miki 200k ki d'auki 100k 100 kuma kiyi siyayyan kayan akwatin ki gabaki d'aya akwaiti ne kawai bazaki siya ba nayi Ordern su."Bud'e baki tayi tana kallon sa sannan tace
"Kuttt me ka daukeni ne Kabir a 100k zanyi siyayyan nawa?
Chabbb wllh bazaiyu ba! Kaje Kai kayi siyyayan a 100k din mana, sannan me zanyi da dubu dari a bikin Nan wllh bazaiyu ba sai dai na maida maka kud'in ka."Tana gama fad'an haka ta cire Ihsan a nono ta gefata kan gado ta shige toilet.
Kabir dafe kanshi yayi Dan har ya fara sara mishi yace
"Oh God."Sai da ta d'auki kusan 30 mins a toilet sannan ta fito.
A inda ta barshi a nan ta sameshi zaune.
Kallon ta yayi yace
"Wai Jiddah me kikeson nayi miki ne dan Allah, meyasa bakida godiyar Allah ne Ina laifin 100k tsakani da Allah bayan kince zan chanza miki kayan parlour bakya tausayina ne Jiddah?"Mugun kallo ta watsa mishi sannan tace
"Kabir wannan fa duk kai ka saka kanka ni bai dameni ba, batun bana tausayin ka kuma bata tasoba tunda kai kaja aure to wllh sai kamun duk wani abu da nake da buk'ata.""Hmmm to Allah ya kyauta ya shirya mun ke."
A masifance tazo kusa dashi tana cewa
"Wato daman mahaukaciya ka daukeni Kabir ko duk rawar kan karin aure da zakayi ne?
To wllh ka kikayi bakin ka domin wata rana abin bazai maka dad'i ba!" tana gama fad'an haka ta fita tabar masa d'akin.Gaba d'aya Kabir shikam ya rasa me yake mishi dad'i gashi Maman shi ta bazata barshi ya wulakanta Jiddah ba saboda auren da zaiyi.
Haka ya kwana yana ta tunanin mataki d'aya da yakamata ya d'auka.
YOU ARE READING
ZAMAN KISHI
Genel Kurgulabarine akan gidaje uku wanda ko wanne cikin su nashi salon kishin, labarine me dauke darusa da dama ki nutsu ki karanta domin limintuwa da wannan k'ayatattacen labarin.