🎈🎀 *ZAMAN KISHI*🎈🎀
*WRITTEN BY*
*MOMYN MUSADDIQ/HYDAR*✍🏻*PAGE 36~40*
Sosai suke surutu a cikin gida dan mutane ne da yawan gaske suka kawo amarya.
Nida Anty sadeeya ne da Anty Azima Yar uwar Maman Waleed sai kuma matar abokin Waleed da muke kawance da ita Hafeezah.
Gaba d'ayan mu muna zaune a parlour suna jiran a kawo mun amarya sai su tafi.
Har k'arfe goma na'a shigo da amarya wajen uwar gida ba ganin haka ga dare yayi sosai yasa Anty sadeeya tace
"Kunga mu tashi mu tafi dan naga mutanen nan basuda niyar kawo amaryar nan yau maybe sai gobe."Ji nake kamar zanyi kuka haka suka tashi suka tafi Allah yasa suna fita suka had'u da abokan Waleed d'aya daga cikin su ya d'auke su ya kai kowa gida.
Suna fita nima cikin d'akin na na koma na cire kayan da ke jikina nayi shiga wanka bayan na fito kayan barci na saka.
Ina k'ok'arin kwanciya Waleed yayi sallama ya shigo.
Amsa mishi nayi Ina me tashi na zauna.
Gaidashi nayi ya amsa fuskan sa a sake sannan yace mun
"Daman nazo ne muyi sallama zan shiga wajen k'anwar ki da fatan babu wata damuwa?"Tunda ya fara maganar k'irjina yake ta faman bugawa da sauri,dakyar na samu na dai-dai ta nutsuwa nace
"Masha Allah mijina babu komai Allah ya tashe mu lafiya ka gaida mun da kanwa, sannan ka kulamun da ita."Har cikin ran sa Waleed yaji dad'in kalamai na,janyo ni jikin sa yayi yace
"Allah sarki 'yar aljannah yau zanyi missing din ki over Kuma......."rufe mishi baki nayi dan banason jin dad'in bakin irin ta maza bayan rawar kafar shiga d'akin amaryar sa yake amman zaizo ya cika ci da surutu ce mishi nayi
"Ba komai ai mijina tunda kana tare da k'anwata tashi kaje Kar ta gaji da jiran ka."Dariya yayi yace
"Au abin naki harda kora?"
"A'a ba korar ka nake ba kawai banason ka shiga lokacin ta ne."Ledan da ya shigo dashi ya janyo ya ajiye mun sannan ya mik'e yace
"To sai da safe."
"Allah ya kaimu."kawai na iya cewa domin wani irin kuka ne take son zuwa mun.Yana fita na k'arasa bakin k'ofa da gudu na saka key na dawo na fad'a gado Ina wari kuka da duk me sauraron na sai ya tausaya mun.
Waleed kuwa a parlour ya tsaya ya kurawa k'ofar d'akin idanu inajin shesshek'ar kuka na.
Sai da ya dad'e sosai a parlour sannan ya fita ya shiga d'akin amaryar sa.
Da sallama ya shiga d'akin,tana zaune a tsakiyar gado d'akin nan sai k'amshin turare yake ko Ina an gyara shi tsaf.
Bakin gado yazo ya zauna murmushi d'auke a fuskan sa yace
"Amarya bakya laifi Koda kin kashe dan masu gida."Murmushi Hafsat tayi ta yaye mayafin da ke kanta tace
"Sannu da zuwa Ango na."Mik'ewa yayi zai cire babbar rigar sa ta Mike da sauri tana karb'a tana tayashi cirewa tace
"Wannan aikin ba naka bane ango na, barshi na cire maka."
Haka ta cirewa Waleed kayan jikin sa baki d'aya ta barshi daga shi sai gajeren wando.Shikam mamakin Hafsat kawai yake dan kam Kubrah bata mishi a Daren su na farko ba Amman wannan harda cire mishi kaya, sai chan wata zuciyar Kuma tace mishi ai zamanin su ba d'aya bane dole yanayin wayar su ta banbanta.
Kallon sa tayi tace
"To Nima ka tayani cirewa man."Murmushi yayi mata ya shiga cire mata kaya sai faman turo mishi k'irji take a haka aka gama cire kayan gaba d'aya.
"Yauwa angona mu shiga wanka ko."
"Ok muje."
Haka suka shiga wanka a tare suka fito gaba d'ayan su da towel a kugun su.Wasu shegun kayan barci ta d'auko ta saka dan Waleed kam hankalin sa gaba d'aya ya gama tashi.
YOU ARE READING
ZAMAN KISHI
General Fictionlabarine akan gidaje uku wanda ko wanne cikin su nashi salon kishin, labarine me dauke darusa da dama ki nutsu ki karanta domin limintuwa da wannan k'ayatattacen labarin.