🎈🎀 *ZAMAN KISHI*🎈🎀
*WRITTEN BY*
*MOMYN MUSADDIQ/HYDAR*✍🏻*PAGE 66~70*
"Yauwa daman ba wani abu bane inason na sanar da ku halin da yarinyar Nan take ciki ne."
Gyara zama Baba yayi yace
"To likita muna jinka."
"Da farko dai yarinyar nan ta samu karaya biyu a hannun ta Amman alhamdullah mun samu nasarar gyara hannun, sai Kuma kanta da ya bugu wanda ya haddasa Mata zubar da jini sannan yasa ta dogon suma, alhamdullah mun shawu kan matsalar insha Allah zuwa wani lokaci zata farfad'o,Amman kafin Nan muna buk'atar jini za'a Mata kari."Tunda doctor ya fara magana babu wanda ya iya cewa komai a tsakanin su dan duk tausayin Humaira da Kuma son jin dalilin ciwon ta yake.
Baba ne yayi karfin halin cewa
"To alhamdullah mun gode likita bari muje mu nemo jinin." Ya k'arasa maganar yana karb'an wani farin takarda da likitan yake bashi.Mik'ewa sukayi suka fito Malam Abdullah wato mahaifin Waleed har yanzu ya kasa cewa komai, maganar doctor kawai yake nanatawa a zuciyar sa "karaya biyu a hannun Humaira garin yaya wannan mummunar abin ya sameta??"shine kawai tabbayar da keyiwa kansa.
Koda su Baba sukazo wajen mu Basu boye Mana komai ba suka fad'a Mana har ma da jinin da za'a sawa Humaira.
Tunda baba ya fara Mana bayani naji wani irin abu yana d'ibana na tun Ina daurewa har yakai da na fad'i na suma.
Nima wani d'akin aka shiga dani aka shiga bani taimakon gaggawa tare da wasu gwaje-gwaje.
Bayan sun gama duk wani gwaji da zasuyi mun allurar barci sukayi mun dan na swmu hutu Nima.
Abban Waleed ne ya d'auki waya ya kira Waleed yana d'auka yace yazo ya sameshi a asibiti yanzu ya fad'a masa sunan asibitin da suke.
Ba'a d'auki lokaci ba Waleed yazo asibitin.
Abban sa ne yace
"Ko kasan abinda matar ka ta aikawa 'yar ka?"Kallon sa Waleed yayi yace
"Me ya faru Abba bansan komai ba."
"Matar ka Hafsat ko kasan abinda ta aikawa Humaira?........"nan ya mishi bayanin duk abinda ya sani Wanda ya faru da Wanda likita ya fad'a.Daga idanu Waleed yayi ya kalli Abban nashi yace
"Abba yanzu kai ka yarda da Hafsat zata iya aikata wannan abin?
Wllh ba wani sharri ne kawai irin na mata Bata san sharrin da zatayiwa Hafsat bane shiyasa ta dauko wannan hanyar dan rabamu da ita to wllh bat......." A tsawace Malam Abdullah yace
"Dakata Waleed banason shashashanci!
Me kake nufi da hakan ?
Kana nufin Kubrah ce zata cutar da 'yarta dan kawai wani shirme!
To bari kaji banson nakarajin makamancin irin wannan maganar a bakin ka, sannan kayi maza kaje a dibi jinin ka a sakawa Humaira."Turo baki Waleed yayi yace
"Abba nifa gaskiya bazan iya bada jini na ba!
Domin Nima ba lafiya gareni ba, ita uwar tata taje ta bayar mana tunda ita ta aikata mata wannan abin."Baki kawai Abba ya sake yana kallon Waleed wanda shi da yayi maganar ko a jikin sa, baima damu da kallon da Abban yake masa ba.
Baba da yake tsaye a gefen su ne ya kalli Waleed yace
"Waleed lafiyan ka kuwa kasan abinda kake fad'a?"
"Na sani gaskiya na fad'a bazan iya bada jini ba."
"To shikenan bari ni naje a gwada nawa idan yayi dai-dai da nata alhamdullah sai a diba idan kuma baiyi sai a siya ko."
"Da dai yafi."cewar Waleed.Wani wawan mari mahaifin sa ya wake sa dashi yace
"Waleed yaushe ka koma haka?
Fitsarre ka zama Waleed kasan da Wanda kake magana kuwa?"Dafe kumatunsa yayi yace
"Kayi hakuri Abba wllh bazan iya bada jinina a sakawa Humaira ba, idan har aka saka mata jini zan iya mutuwa Abba a hanlin yanzu banason ko ganin su daga su har mahaifiyar su."yana gama fad'an haka ya fita yabar asibitin gaba d'aya.
YOU ARE READING
ZAMAN KISHI
General Fictionlabarine akan gidaje uku wanda ko wanne cikin su nashi salon kishin, labarine me dauke darusa da dama ki nutsu ki karanta domin limintuwa da wannan k'ayatattacen labarin.