🎈🎀 *ZAMAN KISHI*🎈🎀
*WRITTEN BY*
*MOMYN MUSADDIQ/HYDAR*✍🏻*PAGE 51~55*
Kabir yana fita a gidan sa gidan su direct ya wuce.
Zaune ya sameta a tsakiyar parlour ta baje a carpet tana breakfast hankalin ta kwance.
Kallon ta yayi yayi tsaki yace
"Babu wani aiki da aka iya da ya wuce cii."Harara ta watsa mishi taci gaba da taunar k'ashin ta.
Hajiya ce ta fito a d'akin ta,da sauri Kabir ya durkusa k'asa yace
"Ina kwana Momy."
Waje ta samu ta zauna sannan ta amsa mishi da
"Lafiya k'alau."
Kallon Jiddah tayi wacce sai faman ci take kamar bata tab'a cin abinci ba tace
"Ki tashi ki tattare wajen ki dawo inason zanyi magana da ku."
Da to Jiddah ta amsa sannan ta tattare plate da cup din takai kitchen ta wanke hannun ta sannan ta dawo ta zauna.Kallon ta Hajiya Salma tayi tace
"Sake maimaita mun abinda ya faru kika taho."Gyara zama Jiddah tayi tace
"Momy yau da asuba da na tashi nayi sallah banji alamun Kabir ya tashi ba domin nayi tsammanin zaizo ya tayar dani Amman shiru baizo ba,sai nayi tsammanin ko ya makara ne to shine na shiga parlourn amaryar tashi da niyar nayi musu sallama su tayi suyi sallah tsautsayi yasa nazo na bige wani kwalba bangani ba ya fad'i ya fashe,shine fa ya fito yana dukana a gaban matar sa sannan yace na tafi gida sai ya nemeni."ta k'arasa maganar tana sake rushewa da kuka.Kabir kam mamakin Jiddah yasa ya kasa furta komai sai zuba mata idanu da yayi Yana kallon ta.
Kallon Kabir Hajiya Salma tayi tace
"To kaji abinda tace menene dalilin dukan ta a gaban matar ka da jiya jiya aka kawo maka ita?"Gyara zama Kabir yayi yace
"Wllh Momy duk abinda ta fad'a karya ne ba haka bane!
Ke yaushe na dakeki a gaban Ummu sannan ba mari na Miki ba kikace duka....."Hajiya ce ta katseshi da cewa
"Menene dalilin Marin ta Kabir?
Bakasan masifar da take cikin marin mace ba! Macen ma matar auren ka ba!
Kabir kaji tsoron Allah kazama mai adalci tsakanin matan ka banason ka shiga hakk'in ko daya daga cikin su,ka zama nami adanin namiji ubana,karka nuna banbanci tsakanin Matan ka domin hakan shi zai hana zaman lfy a gidan ka Allah ya muku albarka,
Ke kuma ki nutsu ki gyara halin ki kisan me kike sannan karki sake wannan karambani da kikayi, maza d'auki matar ka ku tafi."Haka ya d'auki Jiddah ya dawo da ita gidan shi ba yanda ya iya.
Parlourn Jiddah suka fara wucewa gidan Nan har yanzu ba'a gyraa na duk datti tsaki Kabir yaja yace
"Ke karkiga Momy tasa na maidaki ba hakan yana nufin bazan sake korarki bane matuk'ar baki daina kazantar nan ba ni Kuma bazan basa koraki gidan ku ba, saboda haka yanzu maza ki d'auki tsintsiya ki share parlourn nan ki goge kafin na dawo."Turo mishi baki tayi tace
"Nifa kawai ka d'auka mun me aiki gaskiya aikin gidan Nan sun fara mun yawa.""Wanne aiki kike da suka Miki yawa?
Shara ko wanke-wanke ko wanki ko gyara gida da gyaran yarki daman jikin ki baki d'aya!
Jiddah ki kalleki dan Allah ki kalli jikin ki bakyajin kunyar kanki!
Matuk'ar baki gyara wannan kazantar taki ba tu nidake fa sai dai hanje daga nesa domin na samu matata me tsafta da kunya me kula da miji na kawo ta."yana gama fad'an haka ya fita yabar Jiddah wacce tayi mutuwar tsaye tsabar bakin ciki.Kasancewar akwai wata k'ofa da zata sadashi da shashen ummu ta parlour sa tanan yabi ta billah ya tafi.
Tun daga bakin k'ofar kamshin turaren wuta ya daki hancin sa, lumshe idanu yayi yanajin wani farin ciki da nutsuwa na zuwa mishi.
YOU ARE READING
ZAMAN KISHI
Ficción Generallabarine akan gidaje uku wanda ko wanne cikin su nashi salon kishin, labarine me dauke darusa da dama ki nutsu ki karanta domin limintuwa da wannan k'ayatattacen labarin.