🎈🎀 *ZAMAN KISHI*🎈🎀
*WRITTEN BY*
*MOMYN MUSADDIQ/HYDAR*✍🏻*PAGE 6~10*
Bayan na raka mijina dawowa nayi cikin gida na sake gyara ko Ina na sake sabon shara na goge duk inda muka b'ata sannan naje nayi wanka na shirya cikin doguwar riga na kwanta dan na dan huta kafin time da girki kuma ya sake yi.
*SU WANENE KUBRA DA WALEED*
Nidai sunana khadeejat Amman iyayena suna kirana da Kubra, na kasance ta uku a cikin yaran iyayen mu da suka Haifa duk da yayuna biyu mata duk basa Raye.
Inada k'anne hudu biyu daga cikin su maza sai biyun Kuma 'yan mata ne twins Hasana da Usaina.
Mahaifin mu malam Adamu malamin makarantar allo ne, Wanda yake koyarwa ne a k'ofar gidan mu tare da almajiran sa.
Sai mahaifiyar mu Safa'atu wacce muke Kira da Umma wacce sukayi auren so da kauna da mahaifin mu.
Duk da mahaifin mu bashi da wani karfi Amman alhamdullah ya kula da mu ya bamu tarbiya dai dai gwargwado.
Sannan munyi karantun boka duk da ba nisa nayi ba iyaka secondary School na tsaya.
Sai Hassana da Usaina Wanda yanzu haka suna ss2 a secondary.
Wannan dan takaitaccen abinda zan iya fad'a muku.
*WALEED*
WALEED dai dan gidan malam Abdullahi ne, shima malami ne kamar nawa mahaifin yana koyarwa da almajiran sa,
Waleed ne kad'ai dan da Allah ya bashi sannan sai yaran da yake ruk'o.Malam Abdullahi Yana da matar sa Zainabu mace ta gari wacce bata d'auki abin duniya a bakin komai ba.
Malam Abdullah bashi da wata sana'a sai koyar da almajirai sai Kuma noma da yake yi, a haka ya samu ya saka dansa d'aya Waleed a makaranta Wanda a yanzu haka yayi degree Amman bai samu aikin gwamnati ba sannan babu wani sana'ar kirki da yakeyi.
Lokacin da malam Adamu da malam Abdullah suka had'a yaran nasu aure gaba d'ayan su babu Wanda ya musa saboda sunbawa yaran su tarbiya.
Koda akayi auren babu wani sana'ar da Waleed yake gashi yanzu yanada iyali hakan yasa shi ya yanke shawaran fara sai da ruwa.
Da farko gaskiya su malam sunki dan a ganin su Bai kamata matashi kamar sa ga yayi karatu ga kyau da yajeda shi ace yana saida ruwa, dakyau Waleed yasha kansu suka amince suka saka mishi albarka a kasuwancin sa.
K'arfe shida na safe Waleed yake fita aikin sa na saida ruwa dan kuwa alhamdullah Kuma Yana samu ba laifi.
A haka kuwa har Allah ya had'a shi da wani Alhaji muktar Yana Kai mishi ruwa kullum gidan sa,ganin Waleed mutum me mutunci da Amana yasa shi d'aukan shi ya maidashi yaron shagon sa a Nan kasuwar sabon gari.Sosai Waleed yake kula mishi da shago gashi yana da kashin arziki tuni shago ya sake habak'a sosai.
Haka kuwa Alhaji muktar ya bawa Waleed jari ya nema Masa shago a kasuwa yace shima ya fara nashi na kansa.
Sosai iyayen sa da matar sa sukayi murnar wannan karamci da Alhaji muktar ya musu Wanda a yanzu Allah ya sawa shagon albarka ya hab'aka sosai har ya samu ya siye gida da abin Hawa.
Wannan shine kad'an daga tarihin wandan Nan family's.
_____________________Ko da Kabir ya fita direct gidan su ya nufa, a parlour ya samu mahaifiyar sa zaune da carbi a hannun ta tana ja.
Sallama yayi ta amsa mishi a nitse.
Macece me ki manin shekaru sittin (60yrs) a duniya kana ganin fuskan ta kasan babbar macece abinda yasa tsufa Bai gama bayyanuwa a jikin ta ba rik'e ibada da tayi.
YOU ARE READING
ZAMAN KISHI
General Fictionlabarine akan gidaje uku wanda ko wanne cikin su nashi salon kishin, labarine me dauke darusa da dama ki nutsu ki karanta domin limintuwa da wannan k'ayatattacen labarin.