🎈🎀 *ZAMAN KISHI*🎈🎀
*WRITTEN BY*
*MOMYN MUSADDIQ/HYDAR*✍🏻*PAGE 56~60*
A Daren yau gabaki d'aya barci ya gagareni abinda Waleed ya aikata Mana kawai nake tunawa ganin zan sawa kaina ciwo hakan yasa na mik'e na nufi toilet nayi alwala nayi sallah raka'a biyu sannan na zauna Ina addu'a.
_Allahumma garratin majaumu wa hada'ati uyuuwa anta hayyun k'ayyumunlaa ta'akhuzuka sinatun walaa naumu, ya hayyuu yaa k'ayyumu ahdi alaihi wa'anmi ainii._
*Wannan itace addu'ar da ake idan barci ya gagara.*Ina cikin addu'a cikin ikon Allah barci ya d'auke ni Wanda bantashi ba sai da asuba.
Koda na tashi nayi sallah ban koma ba dan yanzu babu zazzabi a jikina hakan yasa na mike na nufi kitchen na had'awa yarana breakfast sannan na tafasa musu ruwan tea.
D'aki na koma na tattare na share sannan na shiga nayi wanka na fito.
Alhamdullah naji saukin jikina sosai yau kam, d'akin su Sadiq na shiga na tada su nayi musu wanka na musu Shirin zuwa school kafin sukayi breakfast.Zama nayi na fara tunanin yanda zanyiwa Waleed magana yakai yara makaranta, ganin Ina bata lokaci gashi Kuma zasuyi latti hakan yasa na yanke shawaran zuwa na musu knocking ko Allah zaisa ya fito ya kaisu.
Bakin k'ofar parlourn Hafsat na nufa naje na fara musu knocking.
Sai da na kusan minti goma sannan Hafsat ta fito tana cewa
"Wanne mayen ne wannan da zai takura Mana mun cin kin dad'in mu."ta k'arasa maganar tana bud'e k'ofar.Kallon ta nayi nace
"Dan Allah kiyiwa ya Waleed magana kice lokacin Kai yara makaranta yayi."Kallona tayi sama da k'asa kafin tace
"Hmm da alama dai baki da hankali! Mijin nawa driver ku ne da zai Kai Miki yara makaranta?
Maza ki tafi ki bamu waje bazaije ba."Tsaki nayi nace
"Ke malama kimun magana da mijina ba da ke nake ba, sannan ba shirmen ki nakeson ji ba."Wani karan ihu Hafsat ta saka ta fara kuka ai tuni hawaye suka wanke mata fuska ta rik'e kuncin ta sai faman kuka take.
Da gudu Waleed ya fito a d'akin yana tambayar
" lafiya me ya faru?."Cikin kuka Hafsat tace
"Zuwa tayi tace Wai na tasheka kakai yara makaranta sai nace mata kana barci shine fa tahau zagina da karshe ta mareni."ta k'arasa zance tana sake fashewa da kuka.Nikam tunda ta fara maganar na fara amfata innalillahi domin kana ganin yanda Waleed ya chanza kamar ba shiba cikin kankanin lokaci.
Juyowa yayi wajena a fusace ya wanke ni da wasu tagwayen mari sannan yace
"Ke Daman baki da hankali!
Hafsat zaki Mara tsabar bakida tarbiya?
To Bari kiji sai ta rama Marin da kika mata, sannan daga yau yaran naki bazasu sake zuwa makarantar ba na cire su!"Tunda ya mareni na furkushe a wajen Ina kuka har ya gama abinda zai fad'a duk Ina jinsa.
Jan hannuna yayi na mik'e tsaye yace da Hafsat
"Ki rama abinda taimiki."
Nan Hafsat ta shiga marin fuska na wanda ta maren yakai mari biyar Waleed kuma yana rik'e a hannuna dan karnayi yunkurin hanata.Sai da ta gama ya turani gefe yaja hannun matar sa suka shiga ciki.
Jini hanci na ya fara hakan yasa na mik'e na bar parlour zuwa d'aki na.
Gaba d'aya hawayen idanuna sun bushe nayi nayi kuka yazo mun yaki sai zuciya ta da take mun wani irin zafi dakyar nake numfashi tsabar b'acin rai da yamun yawa.
Haka na wanke fuskana na dawo wajen yara nace yau bazasu tafi school ba anyi musu hutu.
Ina fad'a musu haka na koma d'aki a wahale domin Allah ne kad'ai yasan halin da nake ciki a halin yanzu.
YOU ARE READING
ZAMAN KISHI
Ficção Gerallabarine akan gidaje uku wanda ko wanne cikin su nashi salon kishin, labarine me dauke darusa da dama ki nutsu ki karanta domin limintuwa da wannan k'ayatattacen labarin.