🎈🎀 *ZAMAN KISHI*🎈🎀
*WRITTEN BY*
*MOMYN MUSADDIQ/HYDAR*✍🏻*PAGE 46~50*
Sai k'arfe sha d'aya tukun Waleed ya shigo yazo ya sameni zaune nayi tagumi ina tunani.
Dafa kafad'ata yayi yace
"Kiyi hakuri matata wllh Hafsat ce ta ballemun da rikici Wai bazata iya kwana ita kad'ai ba tsoro takeji shine fa na tsaya rarrashin ta har na samu tayi barci,Kuma....."dakatar dashi da cewa
"Ban nemi sanin abinda ya hanaka dawowa dawuri ba! Amman ka sani kaji tsoron Allah Abban Sadiq karka shiga mun hakk'i kamar yanda Nima bazan bari ka shiga hakk'in ta ba."nayi maza na kwanta domin kukane naji yana zuwa mun.Gaba d'ayan jikin sa yayi sanyi domin yasan yayi laifi.
Gadon shima yahau ya tallafoni jikin sa.
Kamshin turaren Hafsat naji a jikin sa da sauri na mik'e zaune hawaye na zubomun nace
"Mijina k'amshi turaren Hafsat ne har ya rik'e rigarka haka bayan kace mun rarrashi kawai kayi?"Rarraba idanu ya tsaya yimun ganin haka yasa na sake sulalewa k'asa na kwanta Ina kuka.
Sauka yayi da sauri yaje gareni yana cewa
"Dan Allah kiyi hakuri matata ki yafe mun Amman ba abinda kike tsammani bane ya shiga tsakanin mu wllh babu komai."Ko kallon sa banyi ba naci gaba da zubar da hawaye na wanda tun d'azu yake son zuwa bai samu dama ba sai yanzu.
Hannun sa yakai zai kamani nayi saurin cewa
"Ka barni Abban Sadiq kaje wajen amaryar kawai."Daukana yayi chak ya nufi gado dani ya zaunar dani a jikin sa sannan ya fara cewa
"Kiyi hakuri matata nasan nayi laifi amman ba nayi bane dan na kuntata miki but dan Allah ki yafe mun."Goge idanuna nayi nace
"Ba komai na yafe maka Amman dan Allah karka sake aikata haka domin hakan zai iyasa ka aika wani abin wata rana.""To Gimbiya ta." Daga Nan kuma sabo ya chanza ya d'auke su ya kaisu duniyar ma'aurata ta.
Sosai Waleed yaji na chanza masa sai faman samun albarka yake yana mun sambatu wanda ni har abin ya fara bani tsoro.
Ko washe gari tare dashi muka shiga kitchen yana manne a jikina duk inda nayi sai ya bini kamar wani jela.
Bayan mun gama tare mukayi wanka muka shirya cikin kananun kaya Wanda suka mana matuk'ar kyau.
Parlourn sa muka dawo muka zauna shi ya mik'e yace yana zuwa ya shiga d'akin Hafsat.
Itama tayi wanka ta saka wasu shegun kaya riga da wando Wanda ana ganin komai na jikin ta.
Yana ganin ta ya tsaya yana kare mata kallo.
Zuwa tayi ta rungume shi tace
"Oyoyo Angona nayi missing d'in ka."Shima sake runguman ta yayi yayin da wani abu yazo ya tsaye mishi yace
"Nima haka Amarya na nayi missing d'in ki sosai."Sai da suka dad'e a haka kafin yace
"Muje muyi breakfast."B'ata fuska tayi tace
"Nifa gaskiya bazanyi tare da wannan matar taka ba ka kawo mana namu nan kawai muyi."
Murmushi yayi yace
"Ai hakan bazaiyu ba Hafsat kinsan yau girkin ta ne sannan kuma ai tare muke cin abinci saboda haka fito kizo muje bana son haka."Sake shagwa6e fuska tayi tace
"To mijina muje ba damuwa."Haka suka fita rungume da juna har parlour.
Ina ganin su gabana ya fad'i musamman da naga Hafsat da wannan shigar da duk ya fidda tsarai cin ta.
Duk da Hafsat bata kaini dirin jiki ba hakan bai hanani jin kishi ba a take ha hade fuska na tsare Waleed da idanu.
YOU ARE READING
ZAMAN KISHI
General Fictionlabarine akan gidaje uku wanda ko wanne cikin su nashi salon kishin, labarine me dauke darusa da dama ki nutsu ki karanta domin limintuwa da wannan k'ayatattacen labarin.