🎈🎀 *ZAMAN KISHI*🎀🎈
*WRITTEN BY*
*MOMYN MUSADDIQ/HYDAR*✍🏻*PAGE 81~85*
Sun d'auki tsawon mintuna uku a haka kafin asiyah ta zame jikin ta daga na Maryam tana goge idanun ta, dakyar ta bud'e baki tace
"Anty tare muku da mutane suna k'ofar gida."
Maryam ma goge idanun ta tayi tace
"Tun d'azu suna waje da Kun shigo tare ai."tayi maganar tana fita waje.Har waje ta fita ta shigo dasu Malam parlour, sai da katawo musu ruwa da lemo sannan suna gaisa, sosai Malam yayiwa Maryam bayanin yanda ya tsinci asiyah har izuwa jiya da Allah ya bata lfy, tunda malam ya fara Magaba Maryam da asiyah suke kuka har ya gama, sosai Maryam ta shiga yiwa Malam godiya ba kakkautawa, tabbass idan ba'a fad'a maka ba zaka tab'a cewa Maryam da asiyah kishiyoyi bane sai kayi tsammanin kanwar tace.
Waya Maryam ta d'auka ta kira Sulaiman, Koda ya daga cewa tayi kome yakeyi yazo gida yanzu anason ganin sa, sam Sulaiman baiyi tsammanin cewa asiyah aka samu ba, a tunanin sama ya d'auka ankawo wani malamin ne dan yayi mishi addu'a.
Koda Sulaiman sukazo tare da wasu abokan sa biyu, sai Antyn Asiyah wacce itama tazo ne ko ansamu wani lbr suka had'u a gate suka shigo tare, sam idanun sa basu kula da asiyah da take makale a lungun kujera ba sai ya Hajja da Malam da yagani a zaune.
Gaisawa sukayi cikin mutunci da girmamawa, bayan sun gama gaisawa ne Malam ya farayiwa su Sulaiman bayani game da asiyah.
Tunda Malam ya fara magana Sulaiman ya mik'e tsaye danshi sam hankalin sa baije inda Asiyah take ba har sai da Malam ya gama bayani sannan Sulaiman yace
"Dan Allah Malam ka taimakeni kamar yanda ya taimakeka ka nuna mun inda matata take dan Allah, wllh Ina cikin wani hali, yariyar nan marainiya ce Ina tsoron Allah ya kamani da hakkin ta na rashin kula da ita da banyi ba, dan Allah Malam ka taimaka."ya k'arasa magana yana fashewa da wani kuka me ban tausayi.Sosai Sulaiman yabawa su Malam tausayi, yayinda Maryam da Asiyah ma suke nasu kukan.
Murmushi Malam yayiwa Sulaiman yace
"Ga matar ka nan na kawo maka ita, Kuma alhamdullah yanzu lafiya lau take babu wani matsala sai da akwai wasu abubuwa da Zan bata tana amfani dasu.Tunda Malam ya nunawa Sulaiman inda Asiyah take ya nufi wajen ta da gudu ya rungumeta kam a jikinsa yana hawayen farin ciki tare da yiwa Allah godiya.
Asiyah ma kuka ta fashe dashi yayin da su Malam suka sunkuyar da kansu k'asa domin su kunya suka basu, Maryam ma sunkuyar da kanta tayi tana murmushi.
Sun dad'e sosai a haka kafin su raba jikinsu kowa ya zauna.Zaman su ba wuya yaran makaranta suka dawo, gaba d'ayan su tsayawa sukayi suna kallon Asiyah, sai da suka tabbatar itace sannan sukaje da gudu suka rungumeta suna Anty oyoyo.
B'angaren Ruky kuwa tana kwance a d'aki taji sallama amman sam Bata kawo Wai asiyah bace domin malamin ta ya tabbatar mata cewa Asiyah bazata tab'a dawowa ba, gyara kwanciyar ta tayi taci gaba da chart d'in ta a haka har yara suka dawo daga makaranta, jin hayaniyar tayi yawa ne yasata mik'ewa ta fito parlour don ta tsawatar musu saboda sun dameta da hayaniya.
Tana fitowa d'aya d'aki idanun ta suka sauk'a akan Asiyah da sai faman murmushi takewa yaran nasu.
Cak Ruky ta tsaya tana kallon Asiyah, da sauri kuna ta rike kanta da yake wani irin juya mata,
Wani irin mugun ihu ta saka, sai kuma ta fashe da wani mugun dariya ta ya tsorata duk Wanda suke parlour.
Kallon Asiyah tayi tace
"Kee! Kin dawo ko wllh sai na kashe sai na kasheki nace hhhhhh har cikin naki sai na kasheshi, Kuma sai na sake haukataki kin shiga duniya hhhhhhh."ta fad'a tana sake fashewa da wani mugun dariya.
YOU ARE READING
ZAMAN KISHI
General Fictionlabarine akan gidaje uku wanda ko wanne cikin su nashi salon kishin, labarine me dauke darusa da dama ki nutsu ki karanta domin limintuwa da wannan k'ayatattacen labarin.