PAGE 41~45

16 0 0
                                    

🎈🎀 *ZAMAN KISHI*🎈🎀

*WRITTEN BY*
*MOMYN MUSADDIQ/HYDAR*✍🏻

*PAGE 41~45*

Wani asibitin kud'i Maryam ta kai Asiyah Wanda yake ba nisa a tsakanin su sosai.

  Tana zuwa kuwa aka amsheta aka shiga da ita emergency.
Zuwan su baifi da minti biyar ba sulaiman ya shigo cikin asibitin.
  Da gudu ya fito ya k'arasa cikin asibitin inda ya samu Maryam a tsaye sai faman zarya take.

  Tana ganin sa ta k'arasa wajen sa da sauri tana cewa
"Yauwa ka k'araso sun shiga da ita tun d'azu basu fito ba tukun nan."

  Kallon ta sulaiman yayi yace
"Wai me ta gefar da ita Maryam?"
"Wllh Nima bansani ba Amman inada tabbacin abin a k'ofar d'akin ta ne dan Nima na kusan faduwa a wajen Allah ya taimake ni."

  Shiru Sulaiman yayi yana nazari kafin wani Dr ya fito yace
"Ina mijin matar nan?"
Da sauri Sulaiman da Maryam suka k'arasa wajen sa yana cewa
"Gani nan Doctor ya jikin nata."
"Ka sameni a Office."
Bin bayan Doctor yayi ya bishi office.

  Gaba d'ayan su zaune suke akan kujera Doctor yana rubutu akan wani takarda sai da ya gama yace
"Garin ya kuka bari matar ka ta fad'i haka har ta bugu bayan kunsan tana d'auke da juna biyu?"

  "Doctor ni kaina bansan me ya faru ba uwar gida na ce kawai ta kirani tana fad'a mun Asiyah ta fad'i,pls Doctor Ina fatan ba matsala!"

"Eh to zan iya cewa ba matsala Kuma zan iya ce maka da akwai matsala!
Gaskiya yariyar nan ta bugu Allah yayi cikin Nan da bazai fita ba amman gaskiya tana buk'atar kulawa Wanda idan kukayi sake wani abu ya sake faru da ita makamancin haka za'a iya rasa cikin nan domin ba wani kwari yayi ba."

  Ajiyar zuci Sulaiman ya sauke yace
"Insha Allah Doctor zanyi iya bakin k'ok'arina domin ganin ta rabu da cikin Nan lfy."
"Ok Allah ya taimaka."cewar likitan yana mik'a mishi wani takarda yace
"Muna buk'atar maganin Nan yanzu."

  Karb'a Sulaiman yayi ya fita koda suka had'u da Maryam bai boye mata komai ba ya fad'a Mata.

  Sosai ta jajanta abun sannan al'amarin ya bata tsoro.

  Pharmacy da ke cikin asibitin ya nufa ya siyo duk abinda ake buk'ata ya dawo ya bawa Doctor suka koma ciki.

  Wani d'aki daban aka maida ita yayin da aka nad'e mata kanta da farin kalle an saka mata ruwa a hannun ta da alama sunyi mata alluran barci dan har yanzu ko motsawa batayi ba,amman sun tabbatar Mana da ta farfad'o.

  Maryam sulaiman ya bari a wajen Asiyah sannan shi ya koma gida dan dauko musu kayan bukatu.

  Rukayya tana zaune a parlour tana charting hankalin ta kwance sai faman dariya take Sulaiman ya shigo.

  Mik'ewa tsaye tayi tana cewa
"Sannu da zuwa Dadyn Jannart."

  Kallon ta yayi Bai amsa ba yace
"Me yahaki tafiya asibiti ki duba Asiyah?"

  Zaro idanu tayi tace
"Subhallahi Asiyah batada lfy ne ba'a fad'a mun ba?"

  Tsareta yayi da idanu yace
"Ok kina nufin bakiji abinda ya faru da ita fa."

  "Wllh banji ba Dadyn Jannart wani abin ne ya sameta?"

"Faduwa tayi."ya fad'a a takaice.
Waro idanu tayi tace
"Allah yasa cikin jikin ta lfy yake."
"Alhamdullah Allah ya tsare shi."

  Wani bakin ciki ne ya rufe zuciyar Ruky dama idanun ta baki d'aya dakyar ta bud'e baki tace
"Barka Allah ya sake tsarewa."
"Ameen ki shiga kitchen ki had'a mata abinci yanzu zamu tafi dashi Ina jiranki."

ZAMAN KISHIWhere stories live. Discover now