*༺•⚘🌺YᎪᏚᎷᎬᎬN🌺⚘•༻*
*1442H/2020M.*
®☄
*ɢᴀsᴋɪʏᴀ ᴡʀɪᴛᴇʀs ᴀssᴏᴄɪᴀᴛɪᴏɴ✍*
_{ɢαѕkíчα ɗαчα cє dαgα ƙíntα ѕαí ɓαtα, burínmu mu fαɗαkαr dα αl'ummα dσmín ríbαntαr duníчα dα kumα lαhírα.}_'''🎐ɢ•ᴡ•ᴀ🎐'''
*_ɢᴀsᴋɪʏᴀ ᴅᴏᴋɪɴ ᴋᴀʀғᴇ•_*🏇🏼*ɴᴀ ᴍᴀʀᴜʙᴜᴄɪʏᴀ:-*
*Ꮣαnnαt ᴍ. ɴαѕír✍🏼*
*ᴡαttpαd_@Ꮣannatмɴ**sᴀᴅᴀᴜᴋᴀʀᴡᴀ ɢᴀ :-*
*ᴍч вlσσd ѕíѕtєrѕ*
*ᴍαrчαm ᴍ. ᴍαѕír(ᴍαnαв Ƴαr вαbα )*ᴡᴀᴛᴛᴘᴀᴅ:- *ɢαѕkíчαᴡrítєrѕᴀѕѕσ.*
ɢᴍᴀɪʟ:-gαkíчαwrítєrѕαѕѕσcíαtíσn@gmail.cσm
ʏᴏᴜᴛᴜʙᴇ ᴄʜᴀɴɴᴇʟ:- *ɢᴀsᴋɪʏᴀ 24ᴛᴠ .*
ғᴀᴄᴇʙᴏᴏᴋ ᴘᴀɢᴇ:- httpѕ://www.fαcєвσσk.cσm/ᴅσkínkαrfє2019/
ʙᴀᴋᴀɴᴅᴀᴍɪʏᴀ:-
*ɢᴀsᴋɪʏᴀ ᴡʀɪᴛᴇʀ's ᴀssᴏᴄɪᴀᴛɪᴏɴ.*
*😭ᴋᴜᴋᴀɴ ᴋᴜʀᴄɪʏᴀ.....🕊(9)*_Ƴan uwa haƙuri iri biyu ne. Na farko haƙuri abin da kake so idan baka same shi ba. Na biyu haƙurin abin da baka so idan ya sa meka. Samu da rashi duk na Allah ne ƴan uwa, kuma ita duniya ba matabbata ba ce, yau gareka gobe ga waninka, sai ana kai zuciya nesa sannan ake samun cigaba a rayuwa. Ƴan uwa mu kasance masu haƙuri a kowane hali muka tsinci kanmu. Allah yasa mu dace, Ameen Ya Allah 👏🏻_
*sʜᴀғɪ ɴᴀ 29-30📑*
*__________📖* Idanuwansa sun kaɗa sunyi jajir tsabar tashin hankalin da ya shiga har ƙwalla suka fara kawowa.
Ayman da Aymana ma kanta sukayi suna kiran, "Umma! Umma! Ki tashi dan allah, meke damunki? Daddy me ya samu Ummanmu?" Banza yayi musu dan be san me zai ce musu ba, tashi yayi a matuƙar tashin hankali ya nemo ruwa me sanyi ya yayyafa mata shiru bata ko motsa ba, ganin haka yasa hankalinsa ya ƙara tashi, bai yi wata-wata ba ya sureta yayi waje ya sata a mota ya fice a guje sai asibiti.
Bai wani ja dogon lokacin yana gudu akan titi ba ya ƙarasa asibitin dake kusa da su, cikin gaggawa aka shiga bawa Umma taimakon gaggawa likitoci ne burjit akanta sunfi awa biyar akanta, amma basu yi nasara samun sun farfaɗo da ita daga doguwar sumar da tayi, kuma a iya binciken da suka yi basu gano meye musabbabin kawo mata wannan cutar, haka suka kaita ICU ba tare da ta farka ba.
Fitowa suka yi suka samu Daddy a bakin ƙofa ya haɗa kai da gwiwa ya rasa inda zai sa kansa, tsoronsa ɗaya kada ya rasa Umma kamar yadda ya rasa tsohuwar matarsa Amina, a lokacin da yake matsanancin buƙatarta, duk da yaso Amina sosai a baya, amma son da yakewa Umma yanzu yafi son da yakewa Amina, dan yanawa Umma so mafi soyuwa a rayuwarsa.
Duk maganar da Dr. Mahmud ke yiwa Dadday bai jisu ba, domin ya daɗe da lulawa a cikin duniyar tunani, dafasa Dr. Mahmud yayi yace, "Alhaji!" A firgice Daddy ya farka daga duniyar tunanin da ya shiga, a ruɗe ya shiga jero masa tambayoyi, "Dr ya matata take? Tana ina? Ta farka kuwa? Wane ɗakinta aka kaita?"
Shiru Dr.Mahmud yayi ya rasa ta ina zai fara yiwa Daddy bayanin abinda ke faruwa, dan ya lura a matuƙar ruɗe yake, muddun ya faɗa masa abinda yake faruwa kai tsaye, to komai zai iya faruwa.
Wani tunanin ya faɗo masa ya ɗan sashi murmusa tare da yin hamdala a cikin ransa, sannan ya ƙara duban Daddy a nutse yace, "Alhaji ka biyoni office zan yi maka bayani."
YOU ARE READING
YASMEEN.
FantasyLabari ne da ya k'unshi abubuwan ban mamaki kama daga kan:-Hak'uri, juriyar, tausayi, soyayya, yaudara, cin amana, son zuciya, uwa uba makirci gami da dana sani.