*°🔘°YASMEEN°🔘°*
*1442H/2020M.*
®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_'''🎐G•W•A🎐'''
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼*NA MARUBUCIYA:-*
*JANNAT M. NASIR✍🏼*
*Wattpad_@JannatMN**SADAUKARWA GA:-*
*MY BLOOD SISTER*
*MARYAM M. NASIR (MANAB ƳAR BABA)*Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.*
Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com
Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.*
Facebook page:- https://www.facebook.com/Dokinkarfe2019/
Bakandamiya:-
*GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.*
*😭KUKAN KURCIYA.....🕊 (6)*_*Ƴan uwa jomai ka rasa za ka iya samun wanda ya fi shi, amma ban da kwanakin rayuwarka, idan sun tafi sun tafi kenan, don haka kada ka bata rayuwar ka wajen abinda ba zai amfane ka ba, yi ƙoƙari wajan yin abinda zai amfaneka duniya da lahira...Allah yasa mu dace. Ameen Ya Allah 👏🏻*_
*SHAFI NA 24-25📑*
*__________📖* Juyi kawai yake ya kasa rintsawa, abinda ya faru ɗazu da rana ke tayi masa yawo a ƙwaƙwalwa, ita kuwa Safnat tuni barci yayi gaba da ita bama ta san meke faruwa ba, da dai ya ga juyin da yake tayi ba zai masa maganin abinda yake ji ba ya tashi daga kwancen da yake ya nufi bathroom ya ɗauro alwala ya fara gabatar da nafilfilu da addu'o'i tare da roƙon Allah ya bashi ikon kula da ƴar uwarsa har ƙarshen rayuwarsa.Bayan ya gama addu'o'insa ne ya miƙe ya fita a ɗakin, ɗakin Yasmeen ya nufa ya tura ya shiga ciki, turus ya tsaya yana kallan abinda yayi tozali da shi, kwance take saman tayal sai barcinta take cikin kwanciyar hankali, yadda kasan ta samu lallausar katifa ƙarasawa yayi inda take kwance ya tsuguna ya ɗauke ta cak, ya kwantar da ita akan gadonta ya ja bargon da yake saman gadon a gefe ya luluɓe mata ƙafafuwanta zuwa cikinta.
Addu'o'i yayi ya shafe mata jiki da su sumbatar goshinta yayi, ya miƙe da nufi barin ɗaƙin ya ji an riƙon hannusa, juyawa yayi ya ganta tana masa murmushi kuma ta riƙe hannusa gam, ɗagowa yayi ya zauna shima murmushin yayi mata yace, "Dama ba barci kike ba?"
"Barci nake, farkawa na yi tun lokacin da ka shigo ɗakin ai ina jinka, ai ni bani da nauyi barci duk barcin da nake ko ya aka ɗan yi motsi sai naji na farka."
Mamakine ya kamasa aransa yace, _Wannan wace irin yarinya ce, a hankali fa na buɗe kofar na shigo amma har ta farkar caɓ! To yanzu da banko ƙofar nayi na shigo sai na iya firgitar da ita fa._
Yaƙe yayi yace, "Lallai ƙanwata Allah ya baki kinji daɗinki, yanzu dai kwanta ki koma barcinki dare yayi sosai."
"To! Yayana amma sai nayi nafila sannan zan koma, Yaya Ahmad ya gaya min ana so mutum ya rinƙa yin nafila idan dare ya raba, yace ba ƙaramin lada da alheri mutum yake samu ba idan yana yin nafilar dare, kuma yace duk abinda ka roƙi Ubangiji a wannan lokacin yana amsa maka roƙonka, ya kuma biya maka dukkannin buƙatun da ka roƙesa, ka ga ni lokacin ina gida ina yawan farkawa cikin dare, kuma bana jin tsoro nake fita na yo alwala nazo nayi nafilata na roƙi Allah ya bayyana min ku, nayi addu'o'i da Yaya Ahmad ya koyan na rinƙa yi indai ina gabatar da nafilfilu na, Allah sarki Yaya Ahmad ko yana a cikin wane hali yanzu ina kewarsa Yayana ka kaini wajensa dan Allah ko gaisawa ne mu yi."
YOU ARE READING
YASMEEN.
FantasyLabari ne da ya k'unshi abubuwan ban mamaki kama daga kan:-Hak'uri, juriyar, tausayi, soyayya, yaudara, cin amana, son zuciya, uwa uba makirci gami da dana sani.