Page 4&5✍🏻

90 7 2
                                    

YASMEEN.



*_Story & writing_*
*_by_*
*_Jannat mn(Real takowah)_*

*Wattpad_@Realtakowa*

*_Dedicated to my sister_*

________________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

_*BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM*_

_*9 January, 2020😍*_

_*BABBAN TASHIN HANKALI*_
_Babu babban tashin hankali sama da kad'auki lokaci mai tsayi kana ibada, ranar gobe Allah yace kaje wajen wadanda kayi domin su subiya ka._

_Allah ya raba mu da riya ya k'ara azurta mu da ikhlasi a cikin ayyukan mu da rayuwar mu baki daya._

_*SHIRI DA TANADI DOMIN RANAR LAHIRA.*_
_Sau da yawa masoyinka ke cutar ka, mak'iyinka ya taimake ka. Ka ga mai kudi yana sata, talaka yana sadaka, makadi ya fadi gaskiya, malami yayi k'arya._

_Wannan shi ya sa aka kira ta duniya._

_Dan'uwa Idan kana cikin jin dadi ka gode ma Allah, idan kana cikin wahala ka yi hak'uri._

_Dadi da wahala kowannensu ba ya d'orewa. Addu'a ita ce makamin mumini. Hak'uri kuma shi ne gishirin rayuwa._

_Ka tuna cewa, rayuwa ba ta yi sai da kwana, komai tsawon dare gari zai waye._

_Ba kuma a kullum ne ake kwana a kan gado ba. Kuma Kada ka cuci wanda ya cuce ka._

_Sharri kare ne ko ya yi nisa zai dawo ma mai shi. Saboda haka, Idan kana son ka cimma abinda kake so to dole ne sai ka yi hak'uri da wani abinda ba ka so, amma fa shi Mai gajiyar hak'uri ba ya cin dafaffen wake._

_Kuma Rinjayar mai k'arfi ba shi ne gwaninta ba, Gwani shi ne wanda ya iya bakinsa, ya rinjayi zuciyarsa, ya iya had'iye fushinsa._

_*""Komai ka rasa za ka iya samun wanda yafi shi amma ban da kwanakin rayuwarka, idan sun tafi sun tafi kenan, don haka kada ka b'ata rayuwar ka wajen abinda ba zai amfane ka ba, yi k'ok'ari wajan yin abinda zai amfaneka duniya da lahira.....""*_

_Da fatan mun wuni lafiya. Allah ya bamu lafiya da k'arfin Arziki, Allah ya sadamu da alkhairan wannan rana. Ameen ya Allah👏🏻_

_*Page 4&5✍*_

________Ajiyar zuciya kawai take saukewa, cikin kuka ta kwashe duk abunda akayi mata ta fad'a masa, rashi ya b'aci idanowansa sukayi jajir dasu kamar gauta har kwallah suka fara kawowa saboda tsabar tausayima da kuma tuna alk'awarin daya d'aukarwa.......yama rasa mai zai ce mata, kawai sai ya rungumeta yana bubuga bayanta yace

"Yasmeen d'ita kiyi hakuri, insha Allah nan bada jimawa ba zan d'aukeki daga gidan nan gaba d'aya kinji...."

"Yaya Ahmad yaushe kenan, mai zai hana yanzu ka d'auke ni ka tafi dani wajen Yayana, wallahi ni na gaji da zaman gidan.......kuma Yayana yace min yana nan zuwa ya tafi dani, wajansa zaka kaini koh?"

"Eh..! Zan kaiki insha Allah, amma kuma sai kin cinye jarabawar aji shidda, na matakin fita daga primary da zaku fara nan bada jimawa ba, sannan zan kaiki wajen Yayan naki"

"Toh..! Yaya Ahmad nayi maka alk'awarin insha Allah zan cin jarabawar, amma wai Yaya Ahmad taya malam zasu barni na zana jarabawar bacin ban tab'a zuwa makarantar boko ba?, kuma koh uniform bani dasu"

"Hhh! Kada ki badani mana 'yar k'anwata ai nasan duk cikin daliban karkaran nan, babu wanda zai iya karawa da 'yar kanwata, saboda ni nasan na koyar da ita yadda ya kawata. kuma kinga akwai sauran lokacin harna k'ara koya miki wasu abubuwa da yawa, tunda yanzu da saura wata d'aya zuwa biyu ku fara. Zancen uniform kuma jibi insha Allah za'a gama d'inka miki su......nayi magana da shugaban makaranta na bada sunanki hotonki dama dukkan abinda ake bukata na bada tun kwanaki yanzu lokaci kawai muke jira......."

YASMEEN.Where stories live. Discover now