Page 14&15✍🏻

30 1 2
                                    

*°🔘°YASMEEN°🔘°* 
   *1442H/2020M.*



®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_

         '''🎐G•W•A🎐'''
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼


*NA MARUBUCIYA:-*
*JANNAT M. NASIR✍🏼*
*Wattpad_@JannatMN*

*SADAUKARWA GA:-*
*MY BLOOD SISTER*
*MARYAM M. NASIR (MANAB ƳAR BABA)*

Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.*
Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com
Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.*
Facebook page:- https://www.facebook.com/Dokinkarfe2019/
Bakandamiya:-
*GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.*

   
         *😭KUKAN KURCIYA.....🕊 (1)*

      _*Ƴan uwa sau da yawa masoyinka ke cutar ka, maƙiyinka ya taimake ka. Ka ga mai kuɗi yana sata, talaka yana sadaka, makaɗi ya faɗi gaskiya, malami yayi ƙarya. Wannan shi ya sa aka kira ta duniya. Allah yasa mu dace. Ameen Ya Allah 👏🏻*_


*SHAFI NA 14-15📑*

*__________📖* "Assalamu Alaykum, ƴar tsohuwancy kina nan kuwa?"

      "Ka ci gidanku Audu, nice tsohuwar? To yaro ko ubanka na fi shi ƙwari da lafiya ballantana ma a gangaro gareka kai yaro."

    "Hhhh! Lallai ma wannan tsohuwar da tsaurin ido da yawa kike, yanzu dan Allah baki ji nauyin maganar da kika faɗa ba? ki dube ki fa ki ga duk kin gama cin zamanin ki kinyi laushi, amma kike haɗa kanki da irin mu masu jini a jika, to yasin ki sake...." Bai ƙarasa maganar da yake yi ba ta ƙatse shi da cewa,
   
    "Ka ji ni da ja'irin yaro to duk waye yasa ni na yi laushi ban da gyatuminka, ai da ban kawo shi duniya ba da babu abinda zai sa nayi laushi, domin shi ya fara sauya min halittuna daga zuƙeƙiyar mace, duk da har yanzu a zuƙekiyar nake duk da laushin da gyatuminka yasa nayi, kuma a hakan ma ko yanzu nace zan yi aure, sai ka ga ana bin layi domin cike form ɗin fitowa takarar aurena."
   
    "Caɓ! Wai akan wa za'a cike fom ɗin ne? ni ban gane zancenki ba, dan ni a iya sanina baki da wata buɗurwar ƴa da za'ayi layi akanta, dan ke nasan ko a sadaka zamu bayar da ke babu wanda zai ɗauke ki, ƙarshe ma guduwa za'a rinƙa yi idan akayi tozali dake tsohuwancy."
   
    "Audu wallahi zan ci mutuncinka, ka dube ni da kyau daga sama har ƙasa, ka ga ni na wuce duk irin lomamun ƴan matan nan naka, wanda duk ƙwailaye ne irinka ko irgan ɗangi ba su fara ba ballantana ma....."
   
    Saurin dakatar da ita yayi bata ƙarasa amayar da abinda ke bakinta ba, dan yasan halinta yanzu zata kwaɓomasa zancen da zai sashi jin kunya bai shirya ba yace, "Haba ƴar tsohuwancy tamu ke daɗi na da ke baki san wasa ba, ai ni tuni na san cewa kaf ƴan matan da nake gani babu wacce takai ki haɗuwa, gaskiya kakan mu ba ƙaramin dace yayi ba da ya samu zuƙeƙiyar mace irinki hanci har baka tsohuwancy tamu, amma dai nasan ba'a ƙaramin artabu ya sha ba, wajen ganin ya zama tauraronki mafi haske a  cikin buyagin da suke zuwa neman soyayyarki, ƴar ƙyaƙyawar tsohuwar mu?"
   
    "Artabu ma babba aka sha Audu, domin kaf ƴan matan ƙauyen mu a lokacin babu wacce ta kai ni kyau da iya ɗaukar wanka, ina gaya maka Audu ai mun sha gayu ada."
   
    "Hhhh! A hakan? Caɓ! Gaskiya an yiwa ƙyau yankan baya, kice kawai tsohuwancy kun sha kwalabo da yawa? To amma mai yasa yanzu bana gani kina gayu ko dan ƙara'in nan da ƙyawawa ƴan matan masu jini a jika suke yi?"
   
     "Eh! Mana a hakan, baka ga yadda gyatuminka yake da kyau ba? Ai ni ya kwaso gaba ɗaya, shiyasa yake da kyau kamar yadda nima nake da shi ba, ƙara'i kuma ai gyatuminka ne yake hanani yi, shi ya je yana yi shiyasa ka ganin haka."
   
      "Allah sarki tsohuwancy, kice shiyasa na gani gaki nan kin koma kamar wata juji, har ki ɗan ban tausayi fa sosai."
   
       "Ai kuwa dai shiyasa ka ganin kamar juji, shi kuma gyatumin ya zama kamar kwatamai, saboda tsabar ƙara'in da yake yi, ai dole na baka tausayi."
   
    Ganin yadda take wankesa a fakaice kamar yadda shima yake mata ne,  "Hmm!"  murmushi yayi ya dakatar da ita da cewa, "Ni ba ma wannan ba ga saƙon ki inji Ummana tace a kawo miki."
   
    Karɓa tayi tace, "Allah sarki Khadijatu bata gajiya, na gode sosai Allah yayi mata albarka ya raya mata zuri'atar baki daya, fatan dai tana nan lafiya ƙalau? Dan na ɗan jima rabon da na ganta."
   
    "Ameen Ya Allah tsohuwancy, Lafiya ƙalau take, tace ma tana gaishe da ke, kuma tace kiyi haƙuri da jinta da kika yi shiru kwana biyu, ta nan zuwa insha Allah."
   
    "Bakomai wallahi ai ba sai ma ta takura kanta da yawa ba, ni a hakan ma na gode sosai. Wai ina mutumina ne Aymanu? Bai biyo ku bane?"
   
    Aymana ce tace, "Yana gida laifi yayi wa Umma, shine tace ba za'a zo dashi ba."
   
    "Ai ta kyauta dan ice tun yana ɗanye ake tankwarasa, in ya bushe ba zai tankwafi ba, ka ga ai gobe ba zai ƙara aikata abinda yayi ba."
   
    "Haka ne tsohuwancy ashe dai har yanzu kan yana ja da yawa."
   
    "To..! Da ce maka aka yi irin kan gyatuminka ne da ni da zai dai ja tun yanzu."
   
    "Ke daɗi na da ke a fakaice sai kita ciwa mutum cin mutunci ba ruwanki."
   
    "Hhhh! Au! Wai dama kai kana jin haushi."
   
    "A'a! Bana ji, saboda zuciyar dutse gare ni kamar yadda taki take."
   
    "Hhhh! Ai kyan ɗan ya ga ji ubansa, kaga baka gada a banza ba hhh." Ta ƙarashe maganar tana masa dariya, don tasan iya ƙularwa ta ƙular da shi sosai, dama haka take so domin in ba haka take masa ba wata rana zai iya ɗaura mata hawan ruwa.
   
    "Aymana tashi mu tafi, ni dama in dai dan ta wannan tsohuwancy zan zo gidan nan, to yasin sai ta yi shekara da shekaru bata ganin ba."
   
     "Umma ta gaida ashsha Audu, ni dama ban gayyace ka ba, inka ga dama kada ka ƙara zuwa ida nake ni bai dame ni ba."
   
    "Haka kika ce ko? Ai na kusa na tafi na bar miki ƙasar gaba ɗaya, kin ga ina tafi sai ki zuba ruwa a kasa kisha."
   
    "Eh! Haka nace, a sauka lafiya duk inda zaka ka je, ruwa kuma zan zuba a ƙasa na sha har da suɗi."
   
    Bai ce mata komai ba ya kama hannun Aymana suka fice a gidan, ita kuma dariya kawai take masa tace, "Bishiyar giginya, na nesa, yaro sha inuwarka kawai." Tana gama faɗin haka ta cigaba da abinda take yi kafin su zo.
   
   
                    _*(•)(•)(•)(•)(•)*_
   
   
    Da sallama a bakinta ta tura ƙofar ɗakin, hannuta ɗauke da farantin ta shiga cikin ɗakin. Kwance yake ya kalli bango yana wasa da shi, bai ji shigowarta ba har ta zauna gefensa ta shafa kansa, jiyowa yayi ya ga wane ne yake shafa masa kai, Umma ya gani ya tashi zaune ya buɗe baki zai yi magana ta ɗaura yatsanta a kan bakinsa alamun yayi shiru, shiru yayi bai ƙara yin yunƙurin cewa kala ba. Farantin da ke hannuta ta aje a gefen gadon ta ɗauki ƙaramin plate dake rufe ta buɗe ta, lafiyayen abinci ne a ciki ta ɗauki cokali ta fara basa abincin a baki yana ci, sai da ta tabbatar ya ƙoshi, sannan ta aje plate ɗin ta ɗauko lemo ta zuba masa a kofi ta ba sa ya sha ya koshi, tashi tayi ta haɗa kayan ta ɗauka zata fita yace, "Umma ki yi haƙuri wallahi na daina ba zan ƙara ba." Jiyuwa ta yi tana murmushi tace, " Na haƙura Ayaman, kada ka ƙara rashin kunya ba kyau, ka ji ko?" Taso wa ya yi da gudu ya ƙarasa gareta ya rugumeta yace, "Eh! Ummana na ji bazan ƙara ba insha Allah." Itama rugumesa ta yi ta ce, "Yauwa yaron kirki Allah ya yi muku albarka."
    
     "Ameen Ya Allah, Umma yanzu zan iya fita?"
   
    "Eh! Zaka iya fita amma kada kayi rashin ji."
   
    "Ba zaki ji ba Umma."
   
    Yana gama faɗin haka ya fice a ɗakin da gudu yana murna. Murmushi kawai tayi a cikin ranta tace,  _Allah ya shirya mana ku._
   
        Yana sauka yaci karo da su zasu shigo falon, da mamaki suka tsaya suna kallansa, murmushi yayi musu yace, "Oyoyo! Yaya an dawo lafiya?"

YASMEEN.Where stories live. Discover now