*°🔘°YASMEEN°🔘°*
*1442H/2020M.*
®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_'''🎐G•W•A🎐'''
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼*NA MARUBUCIYA:-*
*JANNAT M. NASIR✍🏼*
*Wattpad_@JannatMN**SADAUKARWA GA:-*
*MY BLOOD SISTER*
*MARYAM M. NASIR (MANAB ƳAR BABA)*Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.*
Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com
Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.*
Facebook page:- https://www.facebook.com/Dokinkarfe2019/
Bakandamiya:-
*GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.**RIBACI RAYUWARKA DA AYYUKAN ALKHAIRI.*
_*•Ka k'ara zage damtse wajen ganin ka ninninka ayyukan alkhairi a wannan rayuwa ta duniya, domin ita ce kad'ai mafita ga rayuwar tabbas ta gobe alk'iyama.*_
_*•Kasancewa cikin ayyukan alkhairi da wuraren da ake aikata alkhairi, tare kuma da aikata alkhairin gami da yi don Allah shi ne ke datar da bawa duniya da lahira.*_
_*•Don haka kada ka rai na aikin alkhairi komi k'ank'antarsa, ribace shi ka ga ka fa'idantu da shi, sai ka samu guzuri mai tsoka da zai taimake ka ranar da zinari da azurfa ba sa amfani, sai wannan ƙyawawan ayyukan ne kad'ai za su yi amfani.*_
_*•Allah ya ba mu ikon aikata alkhairi a dukkan tsawon rayuwar mu ta wannan duniya, ya ba mu ikon tuba daga zunubanmu, ya kuma sanya mu daga cikin bayin sa nagari.*__*ALLAH YA SA MU DACE. AMEEN YA ALLAH👏🏻*_
*SHAFI NA 12-13📑*
*__________📖* Zaune suke suna wasan da suka saba, ita kuma ta kura masa ido ta rasa me yasa a duk lokacin da ta kalli Abdallah take ji a ranta kamar itama tana da yaro namiji kamar sa, amma ita a iya saninta bata da wani yaro da ta haifa sama da Ayaman da Ayamana.
“Hmm!” Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta ce, “Na fuskanci Abdallah kana so yaran nan dai su rainaka, ace kullum kana tare da su in kana gida kuma wai kana wasa da su, ya kamata fa ace ka rage wasa da su dan kasan yaro bai san wasa ba, kuma hausawa na cewa da wasa da yaro gwara kwana da yinwa.”Dagowa yayi ya kalleta yana murmushi yace, ”Umma da wa zan wasa in ba da ƙannena ba? Ba ni da wani ɗan uwa ko yar uwa sama da Ayaman da Aymana suma haka, kuma kin ga idan ban jasu a jikina ba wa zan ja Umma?”
‘’Babu, a cigaba da wasa, wai Abdallah yaushe za ku je gidan hajiya? in zaku je dan Allah ka yi min magana zan baka saƙo ka kai mata, ka ji yaron kirki?’’
"To..! Insha Allah zan miki magana, ina jin ma muje yau tun da ba islamiya, kin ga gobe insha Allah juma’a sai na kai Aymana pack ɗin da suka ce suna son zuwa.’’
‘’Hmm! Ku dai bakwa taɓa gajiya da zuwaye-zuwaye wajen wasanni.’’
‘’Umma ai da Yaya zamu je ba….’’ Bai ƙarasa maganar da ya ke san yi ba Umma ta bige masa baki har sai da ya dan fashe ta kallesa tace, ‘’Daga yau in ana magana ba da kai ba ka ƙarasa baki, kuma na ƙara jin kana abin da ya shafi rashin kunya a bakinka.” Juyowa ta yi ta kalli Abdallah tace, “Ka da ka sake ka tafi yau da gobe da Ayman ka tafi da Aymana kawai, kuma bana buƙatar kace zaka ban haƙuri dan ba in da zai je tun da bashi da kunya.’’ Abin ka da yaro kuka sosai Ayman yake ganin jini a bakinsa, jin Umma tace ka da a tafi da shi ko ina yau da gobe yasa ya kara fashewa da kuka yana cewa, ‘’Umma dan Allah ki yi haƙuri na dai na ba zan ƙara yin rashin kunya ba wallahi.’’
‘’Rufe min baki! Ko na zubar da haƙoranka babu ida zaka yau kama ji na faɗa maka, maza ka tashi ka tafi ɗakinku kada ka sake na ƙara ganinka anan ƙasa, in kuma ka bari na ganka sai na faffasa maka jiki.’’ Tashi yayi yana kuka ya tafi ɗakinsu, itama tashi ta yi ta kalli Abdallah tace, "Ka biyo ni ka karbi saƙon da za ka kaiwa Hajiya.’’ Tana gama faɗin haka ta haye sama, jikinsa a sanyaye ya bi bayanta dan har cikin ransa bai ji daɗin hukuncin da Umma ta yake akan Ayman, saboda duk fitar shi yace masa yana zuwa pack da gidan Hajiya, amma ba yadda ya iya Umma ta yanke hukunci kuma tace kada ya yi magana akan haka. Karɓo saƙon ya yi ya sauko ya cewa, Aymana da ke zaune tayi shiru itama da alama bata ji daɗin hukuncin da Umma ta yanke akan ɗan uwanta, ‘’Tashi ki sako hijabinki da takalminki mu tafi ki yi sauri kin ji Aymana.’’
YOU ARE READING
YASMEEN.
FantasyLabari ne da ya k'unshi abubuwan ban mamaki kama daga kan:-Hak'uri, juriyar, tausayi, soyayya, yaudara, cin amana, son zuciya, uwa uba makirci gami da dana sani.