*°🔘°YASMEEN°🔘°*
*1442H/2020M.*
®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_'''🎐G•W•A🎐'''
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼*NA MARUBUCIYA:-*
*JANNAT M. NASIR✍🏼*
*Wattpad_@JannatMN**SADAUKARWA GA:-*
*MY BLOOD SISTER*
*MARYAM M. NASIR (MANAB ƳAR BABA)*Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.*
Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com
Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.*
Facebook page:- https://www.facebook.com/Dokinkarfe2019/
Bakandamiya:-
*GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.*
*😭KUKAN KURCIYA.....🕊 (5)*_*Ƴan uwa, idan kuna son sanin muhimmancin lafiya ka ziyarci asibiti. Haka kuma idan kuna son ganin muhimmancin ƴanci ku ziyarci gidan yari. Wadda kuma bai gane muhimmancin rayuwa ba ya ziyarci makabarta. Allah yasa mu dace. Ameen Ya Allah 👏🏻*_
*SHAFI NA 22-23📑*
*__________📖* Cikin tsawa da faɗa ta buɗe baki tace, "Rabu da su Yayana daina kuka babu wanda ya isa ya ƙara rabamu..."Cikin kaɗuwa gaba ɗaya su suke kallan mai wannan maganar, ɗagowa yayi ya kalle ta cikin mamaki a ransa yake tambayar kansa, _Dama tana magana?_ takawa tayi take har gabansa ta duƙa tana share masa hawayen da ke fitowa har a lokacin daga idanuwansa.
"Ka daina kuka Yayana, babu mai rabu mu, a da lokacin da kuka tafi kai da Umma kuka bar ni bani da wayo, yanzu duk inda zaka je tare zamu je, dan Allah Yaya karka ƙara barni nasha wuya a wajen Mama, Yaya Jafar da Yaya Adam, ko Baba baya kulani kullum sai Mama tasa ya dake ni, Yaya Ahmad ne kawai ke kula da ni baya barina na yi kuka, shima rannan suka rufesa da duka har sai da ya daina motsi, suka fitar da shi suka jefar da shi a wajen gida. Yayana dan Allah kada ka barni, Yaya Ahmad yace min indai muka haɗu ba zaka ƙara barin nayi maka nisa ba, dan Allah karka sauraren su ni ƴar uwarki ce a wajenka zan...." Kukan da ya ci karfinta ne ya hanata ƙarasa abinda take san faɗa.
Rugumeta yayi yana cewa, "Da gaske kece Yasmeen ɗinta?"
"Eh! Yaya Ni ce Yasmeen ɗinka."
Murna ya shiga yi da hamdalah ga Allah da ya bayyanar masa da masoyiyar ƙanwarsa, su Daddy kama tsabar mamaki sun kasa cewa komai kallansu kawai suke.
Kabir kuwa da tun lokacin da ta fara magana idansa ya kawo ƙwalla, tasowa yayi ya ƙaraso wajensu shima ya duƙa yace, "Dan gaske kece asalin Yasmeen ƙanwarmu?""Eh! Yaya Kabir nice."
"To! Me yasa baki gaya mana ba? Kuma tun yaushe kika gane hakan?"
"Tsoro nake ji shiyasa ban gaya muku ba, na gane hakan kuma tun daren da aka kwantar dani a asibiti na gane, ban ƙara tabbatarwa ba sai da kuka zo washe gari na ji an an ambaci sunanka, a nan na ƙara tabbatar da ku ƴan uwana ne."
"Ta ya kika gane nine Yayanki?."
Kamo hannusa ta yi, dama sanye yake da riga t shirt da wando rigar marar dogon hannuce, ta nuna masa baƙin abinda ke damtsen hannusa tace, "Da wannan na gane, Yaya Ahmad ya gayamin wannan baƙin abun dake damtsen mu a wajen Umman mu kuka gado sa, kuma ya gaya min sunan Yayana Yassar ya ce muna kama da Yayana sosai banbancin mu na fishi hasken fata da idanuwa, kuma in dai na ji wani mai suna Yassar a tare da shi akwai mai suna Kabir ba shakka sune ƴan uwana."
YOU ARE READING
YASMEEN.
FantasyLabari ne da ya k'unshi abubuwan ban mamaki kama daga kan:-Hak'uri, juriyar, tausayi, soyayya, yaudara, cin amana, son zuciya, uwa uba makirci gami da dana sani.