Page 31-32✍🏼

54 2 1
                                    


*༺•⚘🌺YᎪᏚᎷᎬᎬN🌺⚘•༻*
             *1442H/2020M.*

   


®☄
*ɢᴀsᴋɪʏᴀ ᴡʀɪᴛᴇʀs ᴀssᴏᴄɪᴀᴛɪᴏɴ✍*
_{ɢαѕkíчα ɗαчα cє dαgα ƙíntα ѕαí ɓαtα, burínmu mu fαɗαkαr dα αl'ummα dσmín ríвαntαr duníчα dα  kumα lαhírα.}_

         '''🎐ɢ•ᴡ•ᴀ🎐'''
*_ɢᴀsᴋɪʏᴀ ᴅᴏᴋɪɴ ᴋᴀʀғᴇ•_*🏇🏼



*ɴᴀ ᴍᴀʀᴜʙᴜᴄɪʏᴀ:-*
*Ꮣαnnαt ᴍ. ɴαѕír✍🏼*
*ᴡαttpαd_@Ꮣannatмɴ*


*sᴀᴅᴀᴜᴋᴀʀᴡᴀ ɢᴀ:-*
*ᴍч вlσσd ѕíѕtєrѕ*
*ᴍαrчαm ᴍ. ɴαѕír(ᴍαnαв Ƴαr вαbα )*



ᴡᴀᴛᴛᴘᴀᴅ:- *ɢαѕkíчαᴡrítєrѕᴀѕѕσ.*
ɢᴍᴀɪʟ:-gαkíчαwrítєrѕαѕѕσcíαtíσn@gmail.cσm
ʏᴏᴜᴛᴜʙᴇ ᴄʜᴀɴɴᴇʟ:- *ɢᴀsᴋɪʏᴀ 24ᴛᴠ .*
ғᴀᴄᴇʙᴏᴏᴋ  ᴘᴀɢᴇ:- httpѕ://www.fαcєвσσk.cσm/ᴅσkínkαrfє2019/
ʙᴀᴋᴀɴᴅᴀᴍɪʏᴀ:-
*ɢᴀsᴋɪʏᴀ ᴡʀɪᴛᴇʀ's ᴀssᴏᴄɪᴀᴛɪᴏɴ.*

    

*sʜᴀғɪ ɴᴀ 30-31📑*

   
*__________📖* Sai yamma liƙis suka dawo daga office, kowa ya shige gidansa dan samun nutsuwa da sauke gajiyar da suka kwaso, ranar ba wata hira suka yi ba suna gama cin abincin dare kowa ya nufi gidansa, aka bar su Safrat a gidan su, dan dama a can suke cin abincin dare.

    A ɗakin Yasmeen Yassar da Safnat suka baje suna hira ita dai Yasmeen ba ta tanka musu, sai dai suka yi abin dariya kawa ta ɗan murmusa, dan dama can yawan dariyar nan ba ɗabi'arta ba ce, murmushi ta fiye yi shima ba kullum take yinsa ba, amma kuma fuskarta takasance kullum a sake take ba'a ɗaure ba.

   
   
    Nisawa yayi yace, "Lil princess ajinki nawa a Makarantar boko." Ɗakowa tayi ta kallesa haɗe da ƙara d yalwata murmushinta tace, "Ai Ni Yaya ban taɓa zuwa makarantar boko ba ballantana ma na shiga a ji." A matuƙar razane suka kalleta suka haɗa baki wajen cewa, "Baki taɓa shiga aji ba? to a ina kika koyi turancin da muka ji kina yi ranan nan?"
   
   
    "Hmm!" Ajiyar zuciya tayi tace, "Duk abin da kuka ga ina yi Yaya Ahmad ne ya koya min, Ni ban taɓa zuwa makarantar boko ba dan Baba baya bari, sai dai tahfiz kawai nake zuwa itama daga baya malam rabi'u ya koroni, shine Yaya Ahmad abin ya basa haushi sosai, yace zai haɗa ya cigaba da koyan karatun har da na tahfiz ɗin."
   
   
    Jijina kai suka yi kawai sun ma rasa bakin yin wata maganar sai can Yassar yace, "Lil Princess ko zaki ɗan iya ban labarin wannan Yaya Ahmad ɗin?"
   
   
    Gyara zama tayi tace, "Eh! Yaya me zai hana zan iya. Nan fa ta fara basu labarin rayuwar da suka yi da Ahmad, dama ko shi waye da abubuwan da yayi mata na alheri, tun farko har kawo ranar da suka rabu, tabbas labarin da Yasmeen da ta basu na Ahmad ya matuƙar girgizasu, kana ganin fuskokinsu zaka ga zallar tausayawa Ahmad.
   
   
     Ita kuwa tana gama basu labarin sai ta fashe da kukan ita tana kewa yaya Ahmad, Dan Allah su kaita wajensa, ko da gaisawa ne suyi su dawo. Nan fa suka fara rarrashita da bata baki har suka shawo kanta ta daina kuka, sai da ta daina kukan gaba ɗaya sannan yasa ya kama hannuwanta yace, "Lil Princess kina san makaranta?"
   
   
    Har saurin take wajen faɗi, "Sosai ma nake san makaranta Yayana." Murmushi yayi ya saki hannuta ya miƙe, kallo suka bisa da shi, bai wani jima ba sai gashi ya dawo dakin ɗauke da wata ƙatuwar leda a hannusa, har gabata yaje ya miƙa mata yace, "Wannan naki ne kayan makaranta ne, kuma insha Allah gobe zaki fara zuwa makaranta, komai da ake buƙatar dalibi ya kasance da shi yana cikin wannan ledar, karɓi ki duba in basu yi miki ba sai na sako miki wanda kike so."
   
   
    Karɓar tayi tana murna baki har wuya, Safnat ce ta taya fito da kayan itama cike da farin cikin abin da Yassar yayiwa ƙanwarsa, uniform suka fara fitowa da su saboda sune a sama, kalar uniform baki da fari ne ɗinki kuma na riga da siket ne, rigar me dogon hannu siket ɗin kuma ya wuce gwiwa amma bai sauka ƙasa ba, sai doguwar farar safa da wani haɗadɗen bakin takalmi sau ciki mai ratsin fari a gefe, tsabar murna bakinta ya ƙi rufuwa sai washeshi take yi, bata ƙara shiga cikin murna ba sai da ta zaro dalleliyar jaka da filas masu kalar da tafi so wato kalar purple da pink haka kalar filas da jakar ta suke.

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Jan 04, 2021 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

YASMEEN.Where stories live. Discover now