YASMEEN.
*_Story & writing_*
*_by_*
*_Jannat mn(Real takowah)_**Wattpad_@Realtakowa*
*_Dedicated to my sister_*
________________________________
*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com_*BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM*_
_*14 January, 2020😍*_
_*Hudubar farko a duniya*_
_Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam yace a hudubar sa ta farko a birnin Madina; *"Ku yada sallama a tsakanin ku, Ku ciyar da abinci, Kuyi zumunci sannan Ku tashi cikin dare kuyi sallah lokacin mutane suna bacci. Idan kukayi haka hak'ik'a zaku shiga Aljannah."* Ya Allah ka bamu ikon aikata wad'annan ibadun amin. Ya ku 'yan uwa ku tuna cewa duniya nan ba itace asalin mazauninmu ba. Asalin mazauninmu itace aljanna inda babanmu Annabi Adam ya fara zama. Saidai mun sauko duniya ne na d'an wani gajeren lokaci. Saboda muyi wata yar jarabawa kafin mu koma. Dan haka kayi k'ok'ari iya yinka dan ka shiga ayarin salihan bayi, Wacce zata koma ainihin matsuguninmu maikyau yalwatacce. Kada ka b'ata lokacinka a wannan k'untatacciyar duniya. Mu dai ba zamu iya canja abinda ya faru ba. Haka zalika ba zamu iya tsara abinda zai faru ba. Toh..! don me zamu sawa kanmu damuwar abinda ba zamu iya canja shi ba?_
_*DAN HAKA KAYI RAYUWARKA CIKIN BAUTAR ALLAH SAI KA ZAMA MAFI FARIN CIKIN BAYINSA. ALLAH YASA MU DACE. AMEEN YA ALLAH👏*__*Page 6&7✍*_
________Tashi sukayi ta kama musu hannu suka tafi d'akinsu, cire musu kaya tayi ta canza musu wasu ta rakasu toilet sukayi alwala itama tayi suka fito, Ayman ya tafi masallaci....suma suka gabatar da tasu sallar.
Da sallamarsu suka shigo cikin falon Ayman na sab'e a saman kafad'ar Abdallah, fuskarsu d'auke da fara'a daka gansu kasan suna cikin farin cikin. Da gudunta nufesu tana fad'in,
"Oyoyo Abba sannu da dawowa"
K'ara yallwata fara'asa yayi d'aukarta yayi ya cillata sama ya cab'e shima yana fad'in,
"Yauwa Aymanata"
K'arasawa sukayi cikin falon cikin farin ciki da annashuwa, zama yayi a d'aya daga cikin kurerin falon tashi tayi zata bar falon,
"Sannun da zuwa Alhaji an dawo lafiya"
"Yauwa, lafiya qlau salma"
Lemon mai sanyi ta shiga zubawa a cikin kasaitaccen Cup mai d'auke da launika biyu fari da ja. Fuskarta d'auke da murmushi ta mika masa Cup d'in tana fad'in,
"Sannu da zuwa Alhaji an dawo lafiya ya hanya"
Karb'a yayi ya k'ara yalwata fara'arsa, wanda ta fito da tsantsar kamar da suke da Abdallah da Ayman, yana mai jindadin abinda tayi mass.
"Yauwa Hajiya, hanya saidai muce Alhamdulillah lafiya qlau Hajiya"
K'asaitaccen murmushi Abdallah yayi dan yana matuk'ar son yaga Abbana da Ummansa suna irin wannan barkwancin yace mata
"Hajiya"
ita kuma tace masa
"Alhaji."
A duk lokacin da suke irin wannan wasan indan ya kalli abbansa sai ya ringa jin dadi, domin bai tab'a ganinshi cikin farin ciki ba tun bayar mutuwar Amensa sai zuwan Ummansa cikin rayuwar su.
YOU ARE READING
YASMEEN.
FantasyLabari ne da ya k'unshi abubuwan ban mamaki kama daga kan:-Hak'uri, juriyar, tausayi, soyayya, yaudara, cin amana, son zuciya, uwa uba makirci gami da dana sani.