Page 1 ✍🏻

429 14 2
                                    

YASMEEN.



*_Story & writing_*
          *_by_*
*_Jannat mn(Real takowah)_*

*Wattpad_@Realtakowa*

*_Dedicated to my sister_*
     

________________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________

https://www.facebook.com/104534761033461/posts/119016616251942/?app=fbl

   _*Alhamdullilah Allah na gode maka daka bini ikon rubuta wannan littafin nawa, mai cike da dunbin darusa a cikisa, wanda inhar kuna tare dani xaku tsinci darusa da ke tattare da wannan littafin nawa . Kafin mu tsinduma a cikin wannan littafin ina son ku san mai wannan littafin KOMAI NISAN JIFA...! ya kunshi, toh dai wannan littafin KOMAI NISAN JIFA....! ya kunshi abubuwa kama daga kan:- HAKURI,  JURIYAH, TAUSAYI,  SOYAYYAH,  YAUDARA, CIN  AMANAH, SAN  XUCIYAH, GA UWA UBA MAKIRCI  DA DANA SANI, dadai sauransu inhar kuna biye dani xaku jisu yadda wannan ruguntsumin ya faru. Ina rokan  Allah ya bani ikon gama wannan littafin kamar yadda na fara lafiya👏🏻.*_

_*BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM*_

       *1st January, 2020😍*

           
_*Page 1 ✍🏻*_

____Cikin fushi ta d'aga hannunta ta wanke yarinyar da zafafan mari har guda biyu, wanda k'arfin marin saida yasa ta duka bakinta ya fashe jini yafara fita daga....,

Yarinya ce k'arama wanda bazata hauwara shekara goma ba, kyakyawa ta ajin k'arshe, farace sosai amma ba irin marar kyan nan ba, dan wani lokacin har wani ja zakaga tanayi soboda tsabar fari, fuskan nan tata daidai da ita tanada manyan idanuwa irin basu jan hankalin mai kallansu, daka ganta kaga jini fulanice.

"Ke wace iriyar jakace dan ubanki a garinku haka ake wanki ko haka uwarki ta koya miki kafin ta gudu ta shiga yawan duniyar.....?, maxa ki tashi kije ki cire wannan uniform din dake jikinki ki sake wanke min kayan nan, sannan saiki xo ki tafi yawon iskancin da kika saba."

"Dan ni wallahi banga amfanin zuwanki wannan makarantar ba, banda iskanci babu abinda kike koda yake bazanyi mamaki ba tunda gado kukayi keda dan uwanki wajen shegiyar uwarku, gashi yanxu daga uwar taku har d'an uwan naki ba'asan ida suka shiga ba,  sun shiga xuciya  ni wallahi har k'okwanto nake anya ku 'ya'yan malamne ma kuwa,"

"bazaki tashi ba saina sa k'afa na tattakaki, kika tsaya kina sauraron abinda nake fad'a wato ga mahaukaciya ko...., "  

D'agowa tayi tare da dafe bakinta da kuncinta, hawaye ke bin kuncinnata d'aya bayan d'aya bude baki tayi ta fara magana bakinta na rawa cikin murya kuka tace "d'an Allah Mama kiyi hakuri wallahi ba...."

bata karasa ba taji an buge mata baki sai da ta saki wata irin gigitaciyar kara, tsaye yake akanta ya dunk'ule hannunsa wada ya buge mata baki dashi,

"Zaki bar wajen nan ko sai nasa kafa nayi boll dake.....indan kika sake kika kara kallona da wadannan gwandara² idanun nan naki saina kwak'ule miki su mujiya kawai...."

Tashi tayi dana kuka fuskar nan tata duk tayi ja saboda tsabar kuka, shiga d'aki tayi ta nufi wata tabar ma wanda duk ta zazzare da ita da babu duk d'aya.

Tana kuka ta fara cire uniform din dake jikina,

bakomai ne yake sata kuka ba face rashin zuwa ta tahfiz din daxatayi yau gashi harda za'a karbar musu.

Dan zagin da duka da Mama take mata da cin mutunci harta saba dasu tun tanaji haushi da takaici harta daina.....,

Kuma gashi malaminsu Malam Rabi'u bashi da mutunci kokad'an, zane ta zaiyi babu ruwansa da tsayawa jin wani uzurinta.

YASMEEN.Where stories live. Discover now