Page 26&27✍🏻

20 2 2
                                    

*°🔘°YASMEEN°🔘°* 
     *1442H/2020M.*
   
   





®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_

         '''🎐G•W•A🎐'''
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼




*NA MARUBUCIYA:-*
*JANNAT M. NASIR✍🏼*
*Wattpad_@JannatMN*


*SADAUKARWA GA:-*
*MY BLOOD SISTER*
*MARYAM M. NASIR (MANAB ƳAR BABA)*



Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.*
Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com
Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.*
Facebook page:- https://www.facebook.com/Dokinkarfe2019/
Bakandamiya:-
*GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.*



   
                
             *😭KUKAN KURCIYA.....🕊(7)* 

        _*Idan ka zamanto Mutumin kirki,mai ƙyaƙƙyawar manufa a rayuwa, sai Allah ya haɗaka da mutanen kirki masu ƙyawawan manufofi irin naka, domin samun cikar burinka. Allah yasa mu dace. Ameen Ya Allah 👏🏻*_




*SHAFI NA 26-27📑*

  
   
*__________📖* Safnat ce ta marairaice murya tace, "Yanzu dan Allah kin kyauta min da kika kira ni da Aunty doguwa? doguwa sunan wani garine a Kano fa."

          Fadwa ce tari caraf ta ce, Amma gaskiya Safnat baki da godiyar Allah, maimaikon kiyi mata godiya da ƙyaƙƙyawan sunnan da ta baki, sai ki nemin kushewa to gaskiya ki sake hali." Ta ƙarshe maganar tana dariya.

          Ta kalli Yasameen yace, "Ni dai godiya neke da sunan da aka ban, amma dan Allah kada a ƙara bani wani bacin ba zan iya ɗauka ba."

          Ciki dariya Safrat itama tace, "Ni ina godiya da wannan sunan da kika ban little princess, amma kada ki ƙaran wani bayan shi kiji ko gimbiya."
 

           Cikin fushi Safnat tace, "Ni gaskiya ba zan yarda ba sai an canza min sunan."

          Duk wannan abinda take ko kaɗan bata darawa, kuma tasan tsokanarsu take yi, amma taki yin ko murmushi balle dariya. Zama tayi a saman kuje ta nisa tace, "Duk wanda yake san na canza mishi sunansa ga dama ɗaya, zai yi min tambaya har uku indai na kasa amasawa to zan canza masa sunansa in ko na amsa su ba zan canza amma fa kaf tambayoyin a kan addini za ku yi min, kun yarda?"

            Da sauri Safnat ta amsa da eh ta amince, suma amincewa suka suna mata dariya na rashin wayon da tayi na kawai wannan abin.

            Safnat ce tace, "Tambaya ta farko wanene Annabi ne kifi ya haɗesa?"
   

   
         Murmushi Yasmeen tayi tace, "Annabi Yunus ne."

   
       "To..! Tambaya ta biyu a ina masallaci mai alfarma yake?"

  
                   "A Makkah mallacin yake."

            Mamaki ne ya kama Safnat a ranta tace, _Yarinya ba zaki iya amsa ta karshen nan ba._ tayi murmushin mugunta tace, "Tambaya ta uku wane sababine ake masa laƙabi mai tashi?"

                   "Ja'afar Bin Abi Ɗalib."

            Tsabar mamaki da ya kama Safnat kasa cewa komai tayi sai kawai ta koma ta jingina da kujera tana ta kallan Yasmeen.

       

              Kallan Safrat ta yi ta ce, To..! Aunty kumatu saura ke."

  

YASMEEN.Where stories live. Discover now