*°🔘°YASMEEN°🔘°*
*1442H/2020M.*
®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_'''🎐G•W•A🎐'''
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼*NA MARUBUCIYA:-*
*JANNAT M. NASIR✍🏼*
*Wattpad_@JannatMN**SADAUKARWA GA:-*
*MY BLOOD SISTER*
*MARYAM M. NASIR (MANAB ƳAR BABA)*Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.*
Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com
Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.*
Facebook page:- https://www.facebook.com/Dokinkarfe2019/
Bakandamiya:-
*GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.*
*😭KUKAN KURCIYA.....🕊 (2)*_*Ƴan uwa idan kana cikin jin daɗi ka godewa Allah, idan kana cikin wahala ka yi haƙuri. Daɗi da wahala kowannensu ba ya ɗorewa. Addu'a ita ce makamin mumini. Haƙuri kuma shi ne gishirin rayuwa. Allah yasa mu dace. Ameen Ya Allah👏🏻*_
*Wannan shafi tukwici ne a gareku fan's ɗin ƙwarai YASMEEN FAN'S. Haƙiƙa kun nunamin ku ɗin ƴan amana, ina godiya da kulawarku a gare Ni. Ku yi komai ba komai bane na wajena.*
*SHAFI NA 16-17📑*
*__________📖* Yana fita ya nemi waje ya zauna ya dafe kansa dake bazanar tarwatsewa, yana ambatan Allah a cikin zuciyarsa dan ya samu sassaucin yanayi da ya ke jin kansa a ciki.Rayuwarsa ce ta baya ke ta dawo masa a cikin ƙwaƙwalwarsa, kamar a tv haka idanuwansa ke hasko masa rayuwar da yayi da ƴar ƙanwansa abin sansa, sai kuma hoton wata mata da yake gani a cikin kansa ta na bashi abince a baki, amma matar fuskarta ta yi masa dishi-dishi baya iya ganin kamaninta.
Ya ɗauki tsawon lokacin a nan yana tunani rayuwarsa ta baya bai sani ba, har sai da Dr. Ya zo ina yake ya dafasa sannan ya dawo daga dogon tunanin da ya tafi.
"Dr. Ya jikin nata? Fatan dai kun yi mata duk abinda ya dace a yi mata?"
"Alhamdulillah! Komai lafiya ƙalau, muyi mata duk abinda take buƙata ayi mata."
"Dr. Zan iya ganinta?""Eh! Za ka iya, amma yanzu barci take yi sai zuwa anjima, sannan allurar da aka yi mata zata sake ta."
"To..! Dr. Ba komai zan jirata har ta tashi, ina san na ji tamin magana na ji daɗi, dan sosai nake jinta a raina kamar ƙanwata."
"Okay! Allah ya bata lafiya."
"Ameen Ya Allah Dr. Na gode sosai."
"Ba komai Yassar ai aikinmu ne wannan."
"Haka ne, yanzu ina ne ɗakin da take kwance ina san naje na ganta?"
"Okay! Bari nasa a raka ka." Wata nurse ya Kira yace, ta raka shi ɗakin da akai yarinyar da aka yiwa aiki yanzu."
Cikin girmamawa ta amsa da to, ta shige gaba Yassar ya bi bayanta, har ɗakin da Yasmeen ke kwance ta kai shi sannan ta jiyo. Duk abinda ke faruwa Safnat na kallansu ta kasa cewa uffan, ban da hawayen nadamar da miskilancinta ya sata babu abinda take yi, itama bin bayansu ta yi.
Tura ɗakin ta yi bakinta ɗauke da sallama ta shiga, zaune ta same shi a gefen gadon da Yasmeen ke kwance, ya ƙura mata idon yana kallanta yana murmushin da shi kansa bai san na menene ba, ƙarasawa ta yi har inda yake ta ɗan dafa kafaɗarsa, jiyowa yayi ya ga wanene ya dafashi ya ganta, da ɗan mamaki ya kalleta dan shi har ya manta na suna tare da ita, ido ya zuba mata yana kallanta cikin tausayawa ganin idanunta sunyi jajir.
YOU ARE READING
YASMEEN.
FantasyLabari ne da ya k'unshi abubuwan ban mamaki kama daga kan:-Hak'uri, juriyar, tausayi, soyayya, yaudara, cin amana, son zuciya, uwa uba makirci gami da dana sani.