*°🔘°YASMEEN°🔘°*
*1442H/2020M.*
®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_'''🎐G•W•A🎐'''
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼*NA MARUBUCIYA:-*
*JANNAT M. NASIR✍🏼*
*Wattpad_@JannatMN**SADAUKARWA GA:-*
*MY BLOOD SISTER*
*MARYAM M. NASIR (MANAB ƳAR BABA)*Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.*
Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com
Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.*
Facebook page:- https://www.facebook.com/Dokinkarfe2019/
Bakandamiya:-
*GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.*
*😭KUKAN KURCIYA.....🕊 (4)*_*Ƴan uwa Rinjayar mai ƙarfi ba shi ne gwaninta ba, gwani shi ne wanda ya iya bakinsa, ya rinjayi zuciyarsa, ya iya haɗiye fushinsa.*_
_*Komai ka rasa za ka iya samun wanda ya fi shi, amma ban da kwanakin rayuwarka, idan sun tafi sun tafi kenan, don haka ka da ka ɓata rayuwar ka wajen abinda ba zai amfaneka ba, yi ƙoƙari wajen yin abinda zai amfaneka duniya da lahira...Allah yasa mu dace*_
_*Barkan mu da Juma'a. Da fatan mun wuni lafiya? Allah ya bamu lafiya da ƙarfin arziki, Allah ya sada mu da alkhairan wannan rana. Ameen ya Allah👏🏻*_*SHAFI NA 20-21📑*
*__________📖* "Umma dan Allah yaushe Yaya zai dawo? Gaba ɗaya gidan ya yi mana wani irin.""Ayman nima ina kewar Abdallah, amma ba yadda zamu yi dole mu yi haƙuri har ranar da Allah zai sa muje masa ziya, dan ba zan iya jira har sai ya gama karatunsa ba sannan zamu ga juna."
"To..! Umma yaushe zamu je masa ziyara?"
"Ka bari Daddy ku ya dawo sai ka tambayesa, amma na san ba yanzu zamu je masa ba sai an ɗan jima."
"Saboda me yasa ba zamu je masa ba yanzu Umma?"
"Saboda in dai muka ce zamu ta ƙura masa, ba zai maida hankali a karatunsa ba, kana san mu zama silar rashin cikar burin Yayanku?"
"A'a! Umma bana so, mu barshi ya yi karatunsa a nutse karda mu takura masa, ni na haƙura da zuwa masa ziyar zamu rinƙa video call da shi har ya gama karatunsa gaba ɗaya ya dawo."
Hamdala ta yi a cikin ranta da samun damar shawo kan yaran cikin sauƙi, ba tare da sun sha wuya ba. Murmushi ta yi tace, "Aiko da Yayanku ya yi matuƙar alfahari da ku."
Sai a lokacin Aymana ta buɗe baki tace, "Indai Yaya zai yi alfahari da mu, na yarda da abinda Ayman yace ba zamu ta ƙura masa ba."
"Wow! Yarana masu tunanin manya, Allah ya albarkanci rayuwarku, ya kuma raya mana ku twin's ɗin Abdallah."
Juyawa suka yi in da sautin maganar ke fitowa, da gudu suka yi kansa suna faɗi, "Oyoyo Daddy!" Rungume juna suka yi muna murna.
"Sannu da zuwa Daddy, an dawo lafiya?"
"Lafiya kawai twin's ɗina, fatan na same ku lafiya."
"Eh! Daddy lafiya ƙalau muke."
"Kun ci abinci kuwa."
"A'a! Kai muke jira ka dawo muci."
"Ayyah! Abin alfaharina, ku zo muje na baku a baki ku ci ku ƙoshi."
YOU ARE READING
YASMEEN.
FantasiLabari ne da ya k'unshi abubuwan ban mamaki kama daga kan:-Hak'uri, juriyar, tausayi, soyayya, yaudara, cin amana, son zuciya, uwa uba makirci gami da dana sani.