Page 3✍️

114 6 0
                                    

YASMEEN.



*_Story & writing_*
          *_by_*
*_Jannat mn(Real takowah)_*

*Wattpad_@Realtakowa*

*_Dedicated to my sister_*
     

________________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

_*BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM*_
     
         _*6 January, 2020😍*_

  _*Kyautatawa Allah zato!*_

_*Wata Rana wani mutum ya tambayi Abdullahi D'an Abbas r.a "Waye zaiwa mutane hisabi ranar kiyama?" Sai yace "Allah ne" sai mutumin yace "Na rantse da ubangijin Kaaba mun Tara."*_

_*Haka an taba cewa wani mutumin kyauye "Lallai zaka mutu" sai yace "daga nan sai wajen WA?" Akace "Wajen Allah" sai yace "Bamu taba ganin alkhairi ba sai daga wajen Allah ta yaya zamuji tsoron tafiya gareshi?"*_

_*Dan haka yan uwa mu ringa kyautat zato ga Allah shine zai isar mana komai. Ina rokon Allah ya yi min rahama ni daku da iyayenmu da malamanmu ya samu cikin inuwarsa ranar alkiyama ranar da babu wata inuwa sai tasa. Ameen Summa Ameen👏*_

_*Page3✍️*_

"Ke wace irin dak'ik'iyace da kika dawo nan kika kwanta kina barci,  wa kika ajiye ne da zai hura miki wuta. Zaki tashi koh sai nayi boll dake.....? shashsha kawai, mutum kullum yana abu amma saboda tsabar kwakwalwar ta kifice baya iya rikewa"

Tashi tayi ta fita had'o yayi da ledoji tayi ta dawo, madafar ta nufi ta fara had'a wuta muntin kad'an ta d'auka ta gama had'awa, saboda inda sabo ta saba tun batakai haka ba Mama ke sata hada wuta, tun tana k'onewa har ta saba bata k'onewa. 

Wata tukunya ta d'auko wanda tafi k'arfinta tana rinjayarta, amma ahaka ta d'agata da kyar ta daura a saman murhu takawo murfinta ta rufe sannan ta fita tabar madafar.

"Mama na had'a wutar"

"Toh..! Wa kika ajiye ne zaizo ya d'aura miki a saman murhun ne? Koh Ubanki ne zaizo ya d'aura miki ne? Koh shegiyar uwarki kikeso ta dawo ta d'aurane? Nama gane ni marainiyar wayanki kike so na tashi na d'aura.....?"

"Assalamu Alaikum"

"Wa'alaikassalam"

"Baba sannu da zuwa"

Banza yayi da ita bai tanka mata ba koh kallonta ma baiyi ba,

"Andawo lafiya baba?"

"Inda ban dawo lafiya ba ai bazaki gani anan ba, bafa nasan munafunci banza dana hofifa, ki fita a idona rufe Yasmeen, Uwarki ma tayi nata ta gama kuma ta gushe babu riba."

"Yauwa malam,  dama kai nake jira tun d'anzu"

"Allah yasa lafiya dai"

"Inafa lafiya, wai malam yanzu kamar ni nasa Yasmeen aiki wai tace mun bazatayi ba wai ni ba uwarta bace, kajifa dan Allah? Yarinya k'arama da ita, koh ina ta koyo wannan rashin kunya haka? Abin na ban mamaki wallahi dan ranan har zagina ta kusanyi...."

Sai kuma ta fashe da kukan munafinci harda hawayen k'arya, itadai Yasmeen tunda ta fara magana take kallonta da tausayin kanta, dan tasan babu abinda zai hana babanta dukanata yau.

"Inalilahi wa'ina ilaihi raji'un yau naga ta kaina ni habu, yi hak'uri Maimunah yi shiru daina kukan akan wannan hatsabibiyar yarinya."

"Ai dole nayi kuka Malam, yanzu indan yarinya nan ta lalace, me mutane zasuce akaina? Cewa zasuyi dagayya na bari ta lalace dan naga ba 'yata bace. Allah ne shedata akan wannan yarinya inayi iya bakin k'ok'arina akanta, amma abu yak'ici yak'ciyewa kaga kuwa dole nayi kuka tun yanzu kafin kuma nan gaba jinina ya hauu, saboda zagin jama'ar garin nan da ma......"

YASMEEN.Where stories live. Discover now