YASMEEN.
*_Story & writing_*
*_by_*
*_Jannat mn(Real takowah)_**Wattpad_@Realtakowa*
*_Dedicated to my sister_*
________________________________
*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com_*BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM*_
_*15 January, 2020😍*_*DUKKAN RAI MAI DANDANAR MUTUWA NE*
_*Duniar da zaka abarta, mene kake ta k'ok'arin karito yaki halak yaki haram saboda ita?*__*Duniar da ba zaka tabbata a cikinta ba, mene naka kake nemanta kamar wanda zai dawwama a ciki?*_
_*Duniar da kake bako a cikinta akan hanya kake zaka tafi ka barta, mene zaka damu da ita?*_
_*Duniar da bata damu dakai ba meyasa kai zaka damu da ita?*_
_*Duniar da duk yanda kayi k'ok'arin ginata wata rana sai ta rushe, meyasa ba zaka barta ba ka gina lahirarka ba?*_
_*Duniar da Manzo (S.A.W) yace "Ka kasance a cikinta kamar bako ko matafiyi", mene kake neman share guri ka zauna?*_
_*Yakai d'an uwa ka rabu da ginin dunia ka gina lahirarka, dan itace matabbata can ne gidan dawwama.*_
_*Allah (S.W.A) yana cewa "DUKKAN RAI MAI DANDANAR MUTUWA NE"*_
_*Annabi (S.A.W) yace "KUJI TSORON MAI RUSHE JIN DADI{MUTUWA}"*_
_*Ya Allah muna neman tsarinka daga rad'ad'in mutuwa da duhun k'abari da wahalar hawan siradi da firgicin ranar tashin k'iyama.*_
_*Ya Allah muna rok'onk'a kada kasa dunia ta zama babban burinmu ko matukar kurewar iliminmu ka tsare mu daga azabar wuta.*_
_*Ya Allah muna rok'onk'a ka shigar damu aljanna ka sada mu da Annabi (S.A.W) dan rahamarka ya ma abocin rahama da jink'ai.*_
*Allah yasa mu dace. Ameen ya Allah*
_*Page 8&9✍*_
"Nagode sosai d'an uwa insha Allah zan yi kamar yadda kace.."
Cikin murmushi ya fad'i tare da dafa kafad'un 'yan uwan nasa guda biyu.....
Wayar Nabil ce ta fara ruri tana neman agaji alamun kira na shiga, d'aukarta wayar yayi ya duba da sauri ya daga gani wanda ke kirasa
"Assalamu Alaykum"
"Toh..! Dady gamunan zuwa"
"Guyz..! Ku tashi muje Dady na neman mu yanzu yanzun nan yace"
Tashi sukayi da saurinsu suka bar wajen, domin sun san halin Dadynsu baya san jira ko kad'an.
Da sallam suka shiga cikin falon Dady, cikin nutsuwa suke tafiyar har suka k'arasa ina Dadyn yake zama sukayi a k'asa, had'a baki sukayi a tare suka furta
"Barka da hutawa Dady"
"Yauwa 'yan samarina"
Cikin fara'a suke gaisawa da mutumin da ke zaune a d'aya daga cikin kujerin falon,
Kabeer ne yace
"Dady gamu"
Gyaran murya yayi yace
"Yauwa naji dad'i zuwanku yanzu baku tsaya b'ata min lokaci ba. Dama bakomai ne yasa nake nemanku ba face abu biyu da zan sanar daku. Abu na farkoh shine magana akan karatuku da kuka kammala yanzu, kuma nasan ko wane daga cikinku yana tsaye da k'afafunsa, kuna da abin yi wato kuna da jari da sana'a mai k'arfi. Kuma dukkan ninku business kuka karanta kuma shi kukeyi yanzo, kunada wayewar kai akan kasuwanci 100%, kunsan yadda zaku tada 50 ta koma 200 ba tare da kunsa algush a cikin kasuwancin ku ba. Hakane yasa na yanke hukuncin baiwa kowanenku d'aya daga cikin Companys d'in da nake dasu, kuma kada kuyi zaton d'auraku Manager zanyi, a Company da nace zan ba kowane ku a'a kyautar Allan zan bakusu, yanzu haka wannan takardun da kuke gani a gabana, ba kowane takaddu nane face na Company da zan ba kowane, yanzu nan kowa zai saka hannu nima zansa. Sannan ga lawyer na nan Barrister Aliyu nasan kunsanyi shi farin sani ma, shi zai zama shede duk da komai a rubuce yake. Kowa yazo ya d'auki takar da d'aya acikin takaddun nan...."
Matsawa sukayi kowa yasa hannu bakinsu d'auke da bisimillah, kowa ya d'auki takarda d'aya a cikin tarin takardun da suke baje a saman center table din dake gaban Dady.
"Masha Allah kowa ya d'auka kenan, abinda ya rage kusa hannu."
"Toh..! Dady"
D'aya bayan d'aya suka riga saka hannu akowace takardar da aka miko musu, duk wannan abin da ake babu wanda yasan wane irin Company ya samu ba da inda yake.
Saida suka gama gaba d'aya saka hannun da ake buk'ata a suyi sannan Dady yace
"Alhamdulillah! Yanzu kowane ku yanada Company kuma mallakinsa, zakuyi mamaki da har yanzu bakusu wane irin Company kowa ya samu da kuma a ina yake, kada ku damu nasan tashin hankalinku kada ace zakuyi nisa da junan kuba. Toh..! Ku kwantar da hankalinku kuna tare bazakuyi nisa da junanku ba, kowanenku Company nisa a wannan garin yake, amma bazan sanar muku da a ina yake ba kuma wane irine sai ranar da komai ya kammala sannan zaku sani....."
Bud'a baki sukayi da niyar zasuyi magana, amma ya dagatar dasu ya hade fuska yace
"Kada kuce zaku........"
_See me next page✍🏻_
_*Vote*_
_*Like*_
_*Comment*_
_*#Realtakowa*_️
YOU ARE READING
YASMEEN.
FantasyLabari ne da ya k'unshi abubuwan ban mamaki kama daga kan:-Hak'uri, juriyar, tausayi, soyayya, yaudara, cin amana, son zuciya, uwa uba makirci gami da dana sani.