*°🔘°YASMEEN°🔘°*
*1442H/2020M.*
®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_'''🎐G•W•A🎐'''
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼*NA MARUBUCIYA:-*
*JANNAT M. NASIR✍🏼*
*Wattpad_@JannatMN**SADAUKARWA GA:-*
*MY BLOOD SISTER*
*MARYAM M. NASIR (MANAB ƳAR BABA)*Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.*
Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com
Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.*
Facebook page:- https://www.facebook.com/Dokinkarfe2019/
Bakandamiya:-
*GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.*
*😭KUKAN KURCIYA.....🕊 (3)*_*Ƴan uwa ku tuna cewa, rayuwa ba ta yuwa sai da kwana, komai tsawon dare gari zai waye. Kuma ba kullum ne ake kwana a kan gado ba. Kada ka cuci wanda ya cuce ka.*_
_*Sharri kare ne ko ya yi nisa zai dawo ma mai shi. Saboda haka, Idan kana son ka cimma abinda kake so to dole ne sai ka yi haƙuri da wani abinda ba ka so, amma fa shi mai gajan haƙuuri baya cin dafaffen wake.*_*SHAFI NA 18-19📑*
*__________📖* Bashi ya farka ba sai wajen 8:00am, a gaggauce ya ɗauki abubuwan da zai yi amfani da su ya shiga bathroom, bai wani ɗauki lokaci ba ya fito cikin shirinsa tsaf dashi.
Kallan gadon da take kwance ya yi ya ga sai kallansa take yi a cikin ransa ya ce, _Dama ba barci take yi?_ amma a fili sai ya sakar mata sanyayan murmushi ya ce mata, "Barka da safiya ƙanwata, ya jikin naki? Fatan kina lafiya?" Bata tanka masa ba sai dai ido kawai da take bin shi da shi."Hmm!" A jiyar zuciya ya sauke ya tako zuwa inda take kwance, zama ya yi a gefen gadon ya kamo hannuta ya ce, "Ƙanwata ba dai inda yake miki ciwo ko?" Kai ta gyaɗa masa alama babu inda ke mata ciwo, shiru yayi na ɗan yi na wasu lokuta sannan ya ƙara cewa, "Me yasa baƙya san yi min magana? Ko tsorona kike ji ne shiyasa baƙya san yi min magana?" Kai ta kaɗan alamu a'a ba ta jin tsoronsa.
Ido ya ƙura mata can kuma ya ce, "Ko bakya magana ne?" Kai da ɗaga a alamun eh ba ta magana, tausayinta ne ya ƙara shiga cikin ransa har sai da ƴar ƙwalla ta fito a gefen idonsa ya ce, "Daga yanzu ki ɗauke ni a matsayin Yayanki, kin ji ko? Zan tsaya miki sannan na kula take kamar ƴar uwata ta jini, ba zan taɓa barin wani abu ya ƙara taɓa ba ballantana ma ya cutar dake, kin yarda da ni na zama Yayanki Ƙanwata?" Kai ta ɗaga alamun eh ta yarda.
Har cikin ransa ya ji daɗi yarda da shi da ta yi ya ce, "Gashi kuma ban san sunanki ba ƙantawa, ko kina so na saka miki wani suna da ban?" Kai ta ɗaga alamun eh murmushi ya yi ya ce, "Zan ringa kiran ki da Yasmeen ya miki ko?" Sai a lokacin ta yi masa murmushi ta kaɗan masa kai alamun ya yi mata, daɗi ya ji sosai har ya kasa ɓoye farin cikin da yake ciki.
Miƙewa ya yi ya tasayarr da ita zaune, ya koma bathroom ya ɗauko wani kwano mai kamar kofi, sannan ya buɗe ledar da yayi mata siyata jiya ya ciro burush da makilin ya ɗauki robar ruwa, burush yayi mata ya ce ta kuskure bakinta ta zuba ruwan a cikin wannan kwanan da ya ɗauko a bathroom, ya wake mata fuka ya gyara ta itama ta fito tsaf da ita sannan ya haɗa mata tea mai kauri ya ringa bata a biki, sai da ta koshi sannan ta kauda kai.
"Kin ƙoshi ne?" Kai ta kaɗan alamun eh ta ƙoshi, murmushi ya yi yace, "Yauwa! Alhamdulillah! Haka nake so, yanzu bari naje gida na karɓo miki abin da zaki ci, dan na san kina jin yinwa saboda tun jiya baki ci abu mai nauyi ba sai ruwan tea kawai kike sha, yanzu zan dawo ki zauna anan kada ki yi motsi mai karfi, kin ji ko Ƙanwata?" Kai ta kaɗa alamu to.
Murmushi ya yi ya ce, "Yauwa! Ƙanwata zan turo wanda zata kula min dake kafin na dawo."
Murmushi ta yi ta kaɗa kai shima murmushi ya yi mata ya nufi ƙofar fita, yana buɗewa yaci karo da ita, kallanta ya tsaya yana yi cikin mamaki murmushi kawai take ta zuba masa, shiko baki ya saki yanata kallanta ba ƙyaftawa, da dai ta ga bashi da damar dai na kallanta ya bata hanya ta wuce, sai ta kawo hannuta wajen idonsa kamar zata tsone masa ya yi saurin ƙyafta su.
"Hhhh!" Dariya ta yi tace, "Ashe dai ba saƙago ka zama ba?" Murmusawa ya yi mata ya ce, "Mamaki ne kawai yasa nake ta kallanki ba ƙyaftawa." Itama murmushiwa ta yi tace, "Mamakin me kake?"
Matsawa yayi gaf da ita har suna jiyo numfashi juna ya raɗa mata a kune, "Kyau na ga kin daɗa daga jiya da daddare zuwa yanzu, sai wani kyali da sheƙi kike, sirrin ne? Ko dai ko dai..?"
Hararar wasa ta yi masa itama ta raɗa masa a kunne tace, "Sirrin ya wuce na nisanta da ka yi, ai duk wannan kyau, sheƙi da kuma kyalli da kace na yi, ka kalli kanka a mudubi za kaga yadda kaima ka yi su."
Sosai ya murmusa yace, "Kice Allah? To da alama dai nisantar junan mu ya karɓe mu kin ga sai mu ƙara, yau da gobe dama jibi..?" ɗagowa ta yi ta ƙara dalla masa hararar wasa har da murguɗa baki tace, "Ni bani hanya na shiga cikin mun bar ƴar Ƙanwar mu da yinwa."Shima hararata yayi cikin wasa yace, "Naƙi in kina da karfi tureni ki shiga."
Kallansa ta yi na ɗan wasu lokacin tace, "Kasan dai zan iya." Gyara tsayuwarsa ya yi ya ce, "To..! Bisimillah!"
Wani shu'umin murmushi ta yi masa wanda ya kasa fassara na menene tace, "Bani zan yi ba yanzu."
"Hmm! Waye zai yi miki yanzu?"
Ɗan juyawa bayanta ta yi tace, "Kalli bayana ka gani." Ɗagowa ya yi ya kalli bayanta, mamaki ne ya lulluɓesa a ransa ya ce, _Dama da waɗannan yaran take tafe? Bata gaya min ba ta bar ni sai saki layi nake yi._ Haɗe rai ya yi kamar bashi ba ya matsa musu hanya su shige ciki, dariya sosai suke yi masa harda ita kanta Safnat ɗin....
_*See me next page✍🏻*_
_*Vote*_
_*Like*_
_*Share*_
_*Comment*_
_*#JannatMN*_
*©JANNAT M. NASIR•*
YOU ARE READING
YASMEEN.
FantasyLabari ne da ya k'unshi abubuwan ban mamaki kama daga kan:-Hak'uri, juriyar, tausayi, soyayya, yaudara, cin amana, son zuciya, uwa uba makirci gami da dana sani.