YASMEEN.
*_Story & writing_*
*_by_*
*_Jannat mn(Real takowah)_**Wattpad_@Realtakowa*
*_Dedicated to my sister_*
________________________________
*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________https://www.facebook.com/104534761033461/posts/119016616251942/?app=fbl
_*BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM*_
*3st January, 2020😍*
_*Page 2 ✍🏻 *_
____A fusace yayi kanta ya dauke ta da kakkauran mari ta tafi zata fadi ya damk'ota, ya had'ata kanta da bango sannan ya damk'i yalwataccen gashin kanata....
Ya kama yaja da iyakar k'arfinsa, wata irin kara ta saki da kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro. Lokaci d'aya kuma tayi shiru saboda azamar tayi yawa, banda hawaye babu abinda take idanunta sunyi jajir dasu, goshinta ya kunbura.
"Ke wace irin dabbace baki da hankali yanzu gashi kin b'ata tamin kaya na, toh! wallahi sai kin wankesu, kumu su fita tas dasu, in kuma ba haka ba saina sa wuk'a na yankaki kowa ya huta mujiya kawai."
Hukuri ta ringa bashi, amma ko tausaya mata baiyi ba sai ma kara jan gashin nata yakeyi,
Hayaniya sukaji suka fito suga meke faruwa, "Yauwa Adam cisge mata wannan shegen gashin" itadai kuka kawai takeyi tama kasa buda baki.....
"Aa! Jafar ba haka za'ayi ba, kai Adam saketa ka jeka cire kayanka, ka kawo matasu ta wakesu tas kaji koh?"
"Toh..! Wallahi kinci sa'a sauri nake shiyasa zan rabu dake, amma bada ban haka ba dasaina tattakaki acikin gidan bazan kawai."
Sakin gashin nata yayi ya nufi d'akinsu muntina kad'an ya d'auka ya fito rik'e da kayan da yacire, watsa matasu yayi ajikita sannan "yace saura kuma naga basu fita ba" yana gama fadin haka yayi waje abinsa.
"Amma wallahi Mama bakiyi ba, nidai banji dad'i ba dakin bari ya wanata, amma wai kika dakatar dashi, wallahi da nine bazan saketa ba sai naga k'arshen rashin kunyar tata."
"Hhhhh! Sai kuma bakai bane koh? Ka ganka Jafar na fuskaci kafini rashin imani....."
"Ke kuma saiki wanke masa kayan tas, idan kikayi masa jika² toh! Kema zakiga jika², kuma ni babu ruwana wallahi koda kasheki zaiyi bai dameni ba." tana gama fad'in haka tabar waje shima Jafar ya bar gidan.
Tashi tayi taje tad'ebo ruwa ta fara wankewa tanayi tana kuka, dakyar take iya cud'asu saboda sunfi k'arfinta, a haka ta gama ta shanya ta gyara wajen.
D'akinta ta tafi zama tayi a tabarma tayi tagumi tana tunanin rayuwarta tare da tausayawa kanta.
"Lokacin ya k'ure min babu damar zuwa wajen Yaya Ahmad, Mama bazata barni ba karshen zata iya dukana....."
Abinka da yarinta tuni barci ya sace ta, banda ajiyar zuciyar babu abinda takeyi.
••••••••••
Zaune take a d'aya daga cikin kujerun kasaitaccen falon nata wanda ya gaji da haduwa, BBC Hausa take kalla, dan Allah yayi da sanjin labarai dan taji me duniyar take ciki. Farace kyakyawa ce duk da ta dan manyanta, amma kyawunta yananan batazata wuce shekara 40 ba daka ganta kaga cikar bafullatana.
Da gudu suka shigo suna fad'in Umma fad'awa jikinta sukayi suna dariya, yarane guda biyu bazasu wuce shekara5 ba mace da namiji kyawawa dasu masha Allah, kuma suna matukar kama da kagansu kasan twice ne koda baka tambaya ba, itama dariya tayi musu sannan tace "Harkun dawo ne"
YOU ARE READING
YASMEEN.
FantasyLabari ne da ya k'unshi abubuwan ban mamaki kama daga kan:-Hak'uri, juriyar, tausayi, soyayya, yaudara, cin amana, son zuciya, uwa uba makirci gami da dana sani.