*RUGAR SAJE*
BY Nusaiba Ayuba Suleiman
Wattpad@nusysa
IG@Nusaiba A.S.Sarkin zango*FITTATU 18📚 2 0 2 1💥*
⚖
*HOME OF QUALITIE'S WRITER'S ASSO📚*
'''{{The Home Of Qualitative Writers That Are Educate Humanities}}'''
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=106249334371950&substory_index=0&id=106248871038663&sfnsn=mo
*⚜️{{H.Q.W.A📚}}✍️*بسم الله الرحمن الرحيم.
_Deducated to my sweet Mamah😍_
_02_
Kuka goggoji take yi kamar ranta zai futa, fadi take"shikenan mairota, shikenan kema kin yi nesa dani, na rasa Safiyya kema gashi na rasa ki, ya Allah duk inda Mairoji take ka zama gatanta, Ya Allah ga baiwarka nan ka tallafi rayuwarta aduk inda ta shiga, kasa ta fada hannu na gari".Kowa dake wajen amsawa yake da ameen, masu kuka nayi da kuma masu matsar kwalla.
Da haka suka karasa daya Rugar dake gaba dasu sosai, duk da ba tada yalwar mutane, kuma bukkokin ciki ba sufi goma ba, *Rugar Na ma'u* sunan rugar kenan, gidan Haj Tako suka nufa dan ita ce gidanta yake da dakunan kasa har uku da kuma shafaffen siminti atsakar gidan, sai bukkoki hudu da rumbu biyu agefe guda.
Sallama sukai suka shiga iya matan da suka tsira, mazan kuma suka tsaya daga waje, da magagin barci a idonta ta fito tana tambayar waye da yar rocilan ta ahannu, gani Goggoji yasa ta wattsake cike da fargaba tace"Goggoji lfy kuwan awannan dare, ince dai ba farmaki aka kawo muku ba?".Ta fada tana kallon matan dake tare da ita, wanda yawanci duk danginsu ne, da matan yan uwansu maza.
Kuka Goggoji ta fashe da shi daman kadan take jira, cikin tashin hankali Tako ta matso wajenta tana tambayarta me ya faru, wata acikin matan Baffa Jauro, mai suna Laraba ita tayi mata bayani da kuma rasa Mairoji da akayi.
Zaman dabaro Tako tayi tana salatin daya d'au hankalin yaranta dake bacci da kuma mijinta, fitowa sukayi suna tambayar meya faru, nan aka fada musu, kuka Ummilo ta saka dan kawar Mairoji ce sosai, Laure kam tabe baki tayi aranta tace 'watakil ma ita ta bisu, wannan mai idon atsakar ka din ', da kyar aka rarrashe su, sannan akayiwa mazan magana suka shigo, dakunan nan na kasa guda biyu aka basu suka duru aciki matan kuma, suka shiga bukkokin, da haka atakure aka kai asubahi, dukda cewa ba wanda ya samu barci acikinsu sai yara kanana.Washe gari da safe kusan kafafen yada labarai sunyi kasuwa da sammakon sanarwar yan bindiga dad'i sun tashi wata Ruga da ke jigawa, bayan sun kad'a garken shanaye dana sauran kiwo, sannan sunyi gaba da yan mata uku daga ciki.
Hankali tashe Alhaji Badan ya shigo gidansa yana sab'a malun malun, idan ka gansa zakayi zatan cewa akai ga gawar babarsa nan, tsabar yanda fuskarsa tayi kutukut da tashin hankali, da Ahmad suka fara cin karo, yai saurin kama hannunsa ya jashi xuwa falonsa, da kyar ya iya daurewa yaima sa bayani, shi ma hankalinsa kamar yaso yafi na uban tashi, yace "amman Abbah karmu bari Malik ya sani, wllh zai iya tashin garinnan baki daya, daman tun jiya yake cemin gabansa na faduwa kamar akwai abinda zai faru a Rugar Saje , yanzu kam idan yaji wannan bakin labarin ba makawa sai hankalin kowa dake garinnan ya tas....." kasa karasawa yai ganin kallon cikin idon da Malik din ke masa, da alama ya dade awajen kuma yaji duk abinda suka fada, bai musu magana ba sai barin falon dayai ya fita waje, kallon Ahmad Abbah yayi bakinsa na rawa yace"yaji mai muka ce....Ahmad yaji fa, shikenan ni kuma tawa kaddarar kenan".Da sauri suka bi bayansa, sai dai basu same sa ba, amman sun samu tsarabar karan motarsa ya fita daga gidan da shegen gudu, hankalin Abbah ya gama tashi, shima mota ya nufa Ahmad ya bi bayansa, suka rufawa Malik baya, sai dai basu ga ma alamarsa ba ko kadan, kai tsaye Jahun suka nufa dan anan yankin da rugga ge suke.
YOU ARE READING
*RUGAR SAJE*
Non-Fictionsarkakiyar soyayya da zumunta mai hade da cin amana, shiga ciki ka karanta tsantsar soyayya, da tarin sadaukarwa.