27

7 0 0
                                    


       *RUGAR SAJE*

BY NUSAIBA AYUBA SULEIMAN

   WATTPAD@NUSYSA
I.G@NUSAIBA A.S.SARKIN ZANGO

  ⚖
*HOME OF QUALITIE'S WRITER'S ASSO📚*
        _(The Home Of Qualitative Writers That Are Educate Humanities)._
https://www.facebook.com/100495222137315/posts/100496042137233/?substory_index=1&sfnsn=mo

                  *[📝I.W.A📝]*

بسم الله الرحمن الر حيم

   _Deducated to my sweet Mamah😍_.

  _27_

  Da gari ya waye ma, tare suka fita gaba dayansu, wani babban waje Uncle din ya kaisu yace suyi siyayyarsu duk abinda suke so su dauka, daganan suka wuce masallaci, dai gab da shan ruwa sannan suka nufi gidan wani abokinsa, balarabe ne, anan suka sha ruwa, tun aranar Maryam taso sanar da Malik halinda ake ciki amman Uncle ya hana yace su masa bazata sai yafi.
    Maryam din kuwa tuni ta kwaso kaayanta daga hotel din da suka sauka ta dawo dasu gidan Uncle dinta, da haka suke gabatar da ibadarsu cikin aminci da buwayar ubangiji.

    Ana sauran kwana biuu salla Malik ya sauka, shi da sauran yan tean dinsu musulmai wadanda zasu gabatar da aikin hajjinsu, bai samu Maryam ba ahotel din, sai yai tunanin ta fita ne, sai dai ya taki sa'a dan ya tarar da Sakeena adakinta, anan ta fara kawo mai karairayi wai ai Maryam din bata zama, tayi wasu abokai maza da mata su ne suke daukarta kullum suna fita, sai can dare take dawowa kamar abuge take, to dayake ma yanzu ya gama sanin wace ita sai kawai ya bita ayanda take so, yai ta fada  har yana cewa"wllh dani Maryam take, watau ba zata bar wannan halin nata ba dai?, zata dawo ai ta same ni mai rabani da ita sai Allah".

   Murmushi Sakeena tayi tace "Uhm, wani abunma ai dan karna fada ne kaga kamar na mata sharri, amman lamarin yarinyar nan ya fara bani tsoro ai."

   Afuzge yadan kalle ta yace "kwantar da hankalinki, ai nasan maganinta ne, ina nan zata dawo ma duk inda ta shiga."

Yana fita ya kira Maryam din awaya, nan yake sanar da ita ai yazo , ya kusan awa ma da sauka, sai tace mai ai itama tana wani waje ne, amman zata kwatanta mai yanzu yazo, baiyi musu ba ya amsa sannan suka kashe wayar.
    Cikin mintuna kalilan ya isa inda ta turo masa da kwatancen, awajen wani gida mai kyau ya ganta, da murmushi akan fuskarta ta kama hannunsa tace "dan Allah muna shiga ka rufe idonka kaji, wani abu zan nuna maka."

   Hararar wasa ya mata sannan suka shiga ciki da sallama, idon nasa ya dan lumshe yana shakar kamshin da gidan yake, sai da suka zo tsakiyar gidan sannan ta tsaya ta ce masa ya bude, ahankali yake ware su tas ya sauke su akan mutumin da yake ganin kamar basu da maraba sai na girma da manyanta, idonsa ya murza yana kara matsawa kusa da mutumin dayake ta sakar masa murmushi, sannan ahankali ya maida kallonsa ga Maryam da itama take sakin masa nata murmushin.

     Kallon hutuma da tambaya yake mata, sai kawai tamai dariya ta koma kusa da Uncle dinta ta ce"Uncle Abdulmalik Muhammad  Saje, kanin Abba yayan mamana kuma."

    Kallonsa Malik ya mayar kan Uncle din murya na rawa yace "da gaske kai ne? ashe zamu kuma ganinka, tsawon lokacin nan kana raye amman babu wanda ya sani, dan Allah kaine?kar ya zama gizo kake mana."

   Murmushi Uncle yayi yana bude masa hannu alamar ya taho, da sassarfa kuwan Malik ya shiga jiki sa yana sauke ajiyar zuciya, farin ciki ne ke dibansa, ji yake kamar ya taka rawa, sai da aka gama nutsuwa tukun na, sannan Malik ya tambayesa bayan rabuwa mai ya faru da shi, ya akayi kuma yazo nan.

     Shafa kansa yayi cike da kulawa da kauna yace"zan so na baku labarin abin daya faru yanzu, sai dai kuma da zakumin hakuri zuwa bayan shan ruwa, kunga yanzu karmu cinye lokacin mu anan gashi yamma ta farayi."

  Kai suka jinjina sannan suka ci gaba da firar yaushe gamo, sai da sukayi sallar la'asar sannan Malik ya kira Sakeena yace ta shirya zaizo ya dauke ta, akwai inda zasuje, to wajen magriba yaje ya dauko ta suka taho nan gidan, ita sai ranar ma taga Maryam tunda suka zo, sai kuma take kallon Uncle cike da mamakin kamanninsa da Malik dinta, sai dai tabar abun batayi mahana ba, har sai bayan da aka sha ruwa.

     Anan ne yake fara fada musu yanda akayi, yace "lokacin da kwale kwale ya nitse damu kasa nayi tunda daman ban iya ruwa ba, to bansan dai yanda aka yi ba na ganni ne awani waje sai bayan na dawo hankalina,  sannan na kula kamar a kurkuku nake, sai bayan kwanaki sannan wasu mutane larabawa da bakar fata su biyu suka zo suka fitar dani,anan naji wai tsintata akayi gaban wani ruwa da ke Nijar, shi ne wadanda suka tsinceni din suka iyo safarata zuwa nan, to kuma sai aka kamasu da hodar iblis, shi ne nima na shiga cikin, shi ne su kuma wadannan suka nemi fita dani akan zan amsa wani laifi ne su kuma zasu dau nauyin zamana anan har karshen rayuwata sai dai kuma ba damar na fita daga kasar don da zarar nayi kokarin fita, to abin da suka boye ne zai bayyana, daga nan kuma hukuncin kisa ne zai tabbata akaina.
Badan na so ba na amsa da hakan, aka fito dani, sannan suka hadani da wani malamin addinin musulunci dan na samu ilimi, to sai Allah ya hada jininmu dashi wannan malamin har ya nemin jin tarihina, nikuwa na fada masa komai , acikin yaransa akwai wadda muke mutunci da ita sosai, daga karshe dai soyayya mai karfi ta shiga tsakaninmu, har mahaifinnata, kuma malami na ya bani aurenta."
Ya juya yana kallon Bahiyya dake sunkui da kai, murmushi yayi yace"Shugabar yan kunya, wasannan ya'yanki ne ai, duka babu surukai anan, ki dena wani jin kunyarsu."

   Kai ta dauke tana son danne kunyar sake taso mata, anan kuma ta janye matan suka koma dakinta da yaran.

   Bayan kwana biyu aka yi karamar sallah, ana cikin hidiman sallah kuma Malik yana can yana kokarin zama da manyan kasar, akan lamarin Uncle dinsa, so ba'a dau wani lokaci ba aka wanke Uncle Malik insa aka gane baida wani laifi, daman ya amsa ne saboda ya kubutar da rayuwarsa, bayan sati guda kuma suka gara shirin dawowa gida gaba dayansu.

    _Alhamdulilla, anan zan dakata kuma sai Allah ya nuna mana bayan sallah, kuyi hakuri dani naso gama littafin ne kafin azumi sai dai halin dana ke ciki na yau lafiya gobe cuta yasa nake jinkirta rubutun, kumin addu'a dan Allah, idan Allah ya bani lfy da tsawon rai zuwa bayan sallah zaku ganni, idan kuma lokaci yayi sai na ce Allah ya sada mu da rahamarsa, wllh ina jin jiki dan Allah kusa ni a addu'oinku, Allah ya bamu lfy mai albarka da amfani, ya bawa sauran yan uwanmu musulmai lfy, wadanda suka rigamu gidan gaskiya kuma Allah ya jikansu, idan tamu tazo yasa mu cika da imani._

*RUGAR SAJE*Where stories live. Discover now