*RUGAR SAJE*By Nusaiba Ayuba Suleiman
Wattpad@nusysa
IG@Nusaiba A.S.Sarkin zango.*FITTATU 18📚 2 0 2 1💥*
⚖
*HOME OF QUALITIE'S WRITER'S ASSO📚*
'''{{The Home Of Qualitative Writers That Are Educate Humanities}}'''
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=106249334371950&substory_index=0&id=106248871038663&sfnsn=mo
*⚜️{{H.Q.W.A📚}}✍️*بسم الله الرحمن الر حيم.
_Deducated to my sweet Mamah😍_.
'''sakon ta'aziyya ga Mai-dambu, Allah ya jikan Baba yasa ya huta, tare da al'ummar musulmai'''
_20_
Ba ta shigo bangarensu ba sai dare, shi ma dan Mamah ta korata ne, tana tura baki haka ta tafi badan taso ba, tana shiga gabanta ya fadi, ko a ina taji wannan kamshi tasan tabbas ma'abocin sa yana kusa, wara idon tayi, sai dai bata ga komai, ba, cikin sanda ta lallaba ta shige dakonta gashi Mamah yau ta hana yan tayata kwana zuwa.Har ta dora hannunta kan makunnin hasken dakin sai kuma ta fasa, tunda akwai hasken vantilation ko iya shi kadai yana dan haskowa ta window dinta, kayanta ta rage sannan ta shiga bandaki, mintuna kusan talatin sannan ta fito dan tun safe cikinta yadan baci, dole sai da tayi juye sannan tayi sauran uzurinta.
Bata shafa mai ba doguwar riga kawai ta saka sai innar wear, sannan tayi shafa'i da wuturi ta dane gado, kara ta saka jin ta fada kan mutum, mikewa tayi tana shirin sakin wata karar akayi saurin rufe mata baki, sannan ahankali aka sakar mata rikitacciyar sumba agefen wuyan ta, jikinta ne ya dau rawa tuni hawaye ya fara gudun tsere akan fuskarta, sannan ahankali taji an fara mata magana,
"Matsoraciya kawai, tun shigowarki nake kallonki , amman dake mahauniya ce sai yanzu da kike neman illatani sannan zaki kula, kinsan me kika dannne min kuwa da kika fado?".Duk da tadau murya amman amatukar tsorace take, yaushe ya zo gidan, me ya kawo shi ma dakinta, jin ya ture ta daga jikinsa ne ya dawo da ita hanakalinta, kallonsa tayi atsorace, daga shi sai dan sweet pant da wata vest data kama shi sosai, kawar dakai tayi tana kudundunewa da bargo, duk da zafin da akeyi dan ita bata son sanyin ac, shiyasa bata kunnashi.
Ko gama dai daita numfashita batayi ba taji ya kuma haurowa gadon, tashi tayi da sauri tana tura baki, bai kula ta ba sai ma kwanciyarsa dayai ya na sauke numfashi alamar kwanciyar tamai dadi, ta dau kusan awa tana zaune duk kuwan da barcin da ke damunta, tuni ta kula da yai barci amman ta kasa kwanciya dan atsorace take, tashi tayi ta koma kan sofa ta kwanta ko minti goma batai ba barci mai nauyi yai gaba da ita.
Ahankali ya tashi bayan ya tabbatar tayi barci, kura mata ido yayi yana jin wani sukuni da farin ciki na ratsa shi, tun azahar da Ahmad ya fada masa ai Mairoji shi aka daurawa ba wani ba, yake jin kansa kamar yana shawagi ne asama, bai taba jin farin ciki irin nayau ba, shi yasa koda suka shigo bangarensu sai ya duba dakin dayasan nata ne ya sauka anan, kuma atake ya yankewa kansa yau kwanan tane dan ya raba kwana.
Sai dai wani bangarwn na zuciyarsa na kwabarsa da tunatar dashi wace yake aure, yarinyar data gama watsewarta atiti, wadda bata san kima da darajar kanta ba, tunip ransa ya baci, da sauri ya tashi daga gabanta yana kara daure fuska kamar tana ganinsa ne, gadon ya koma ya kwanta yana fatar bacci ya dauke sa, domin siffarta ce take mai gizo kamar ba yanzu ya gama ganin taba.Dai dai ana tada kabbara amasallaci na asuba ta tashi, kallon gadon tayi taga ba ya nan, maybe ko ya tafi masallaci ne, ta raya hakan aranta, tashi tayi ta dauro alwala, tayi nafilarta kafin tayi sallar asuba din, tana kan sallaya tana lazimi ya shigo, bai ko kalli inda take ba ya zare farar jallabiyar dake jikinsa ya haura saman gadon, tana ganin bakinsa yana motsawa da alama shima lazimin yake ko zikirin safiya, nade daddumar tayi ta koma kan sofa, ahankali tace "ina kwana,anzo lfy?".
Adunkule ya amsa mata, yace " lau"sai amsar ta bata haushi, wai 'lau' kamar wani me ciwon baki, baki ta tabe tana maida kanta kan dan karamin filon dake kan sofa din, wani barcin ta kuma komawa, don ranan batada shiga aji sai biaèyu na rana.
Barci tasha sosai, sai wajen goma ta tashi, wanka tayi ta shiry cikin wani lace doguwar riga, sai hijabi data sa dan karami daya tsaya iya cikinta, cikin gida ta shiga kai tsaye don ta saba acan take cin abincin ta, bata taba yin girki ba anan bangarenta, Mamah ta tarar tana bawa Marka mai aikinsu bayanin 6anda za'ayi kunun kanwa na ranar, da kuma gidajen da ba'a bayar ba za'a mika musu.
Bayan ta gaida ta ne ta nufi dakin Mamahn da ta daukarwa kanta gyara shi kullum da safe, tana ygarawa ne, ya shigo da sallama kallonta yayi yai saurin dauke kai, don shigar ta fito da ita yanda yake son ganin matarsa,
"Ki hada min abinci mai dan nauyi, kuma karki batamin lokaci".
Kallon takaici ta masa sannan taci gaba da aikin ta, ta dauko wasu kaya zata sakasu acikin sif, sai da tazo kusa dashi yasa mata kafa, gaba daya ta fado kansa, ai tuni yayi mata kyakkyawan masauki ajikinsa yana shakar dadda'dan kamshin dake tashi ajikinta, lumshe ido yayi yana mata kallon kasa kasa, ita kuwan banda kokarin tashi babu abinda take, so take ta mike, don Mamah na iya shigowa koda yaushe.
'dalar mata duwainis yayi yana dan matsasu, wani laushi yaji kamar ta saka burodi, ahankali ya kuma matsawa dai dai lokacin Mamah ta shigo dan ta tabbara zuwa yanzu Maryam din ta gama gyaran daki.
" dallah can dagani, kin wani danne mutum kamar bakya gani, kina tafe kai asama kamar wata bazawar rakuma, dagani ni ana ganinki finge finge nan sai dan karen nauyi".Tashi tayi tana tura baki tace " dadin abin kai ka samin kafa na fadi, kuma ai da saninka ka rike ni na kasa tashi, yanzu da Mamah ta shigo ta ganni kuma fa, wanne kallo kake son tayi min, nidai kam Allah ya tsare ni kuma hada hanya dakai ma wllh....".
Gyaran murya Mamah tayi sannan ta karasa shigowa tace "ah ah....uwata har yanzu baki gama gyaran bane, baki karya ba fa, wannan lalacin naki yana son yaja miki matsala fa da cikinki, ko kadan bakyason bashi hakkinsa na abinci ko".
" mamah, faduwa fa nayi, kuma ni dai gaskiya kiyi magana idan ina gyaran daki adena shigomin, kuma ban yarda bayan na gama ba ashigo dan kar abata min".
Murmushi kawai mamah tayi tace "kiyi sauri ki sauko, kinsan dai yau akwai ayyuka agidannan, gobe suna, dan ma wasu abubuwan aikinsa muka bayar da abun ya hade mana ai".Shigowar Sakeena yasa Mamah dakatawa da maganarta, gaisuwa tayi wa mamah irinta yaran turawa da taga sunayi, sannan ta kalli sashen da Ya Malik yake daya maida kansa kan waya, tace" My....ya zaka taho nan ka barni ni kadai kasan kuma fa kamin laifi don jiya baka kwana adaki na ba, ina kaje daga zuwanmu zaka tsiri wasu halayen daban, gaskiya nidai bazan dau haka ba".
Kallon Maryam tayi tadan mata murmushi tace"ah ah, kaga amare, mijinnaki har yanzu bai ]tariyar taki bane, naganki agida ko kuma dai kin gintse auren, tunda naga zaman wajoko yafi karbarki, uhmm....to Allah ya kyauta, My.... pls taso mu koma part din mu".
Takaici da haushinta ne ya cika sa, ji yake kamar ya tashi ya shake mata wuya, kai ko kalle ta ba, ya kuma gyara kwanciyarsa akan gadon Mamah, ita kam Mamah tun data ji Sakeena ta fara sakin zance, tayi waje domin zataji abinda bai mata ba, idan kuma tayi magana za'a ga kamar ta shigarwa yar wanta ne.
Itama Maryam din bata ko bi takan Sakeenar ba tayi ficewarta, don sha day saura tasan kuma yan ball basa wasa da cikinsu, dole ta shiga kichen don ta sama masa abinda zai ci.
YOU ARE READING
*RUGAR SAJE*
Non-Fictionsarkakiyar soyayya da zumunta mai hade da cin amana, shiga ciki ka karanta tsantsar soyayya, da tarin sadaukarwa.