31

10 3 1
                                    

 

    *RUGAR SAJE*

BY NUSAIBA AYUBA SULEIMAN

   WATTPAD@NUSYSA
I.G@NUSAIBA A.S.SARKIN ZANGO

  ⚖
*HOME OF QUALITIE'S WRITER'S ASSO📚*
        _(The Home Of Qualitative Writers That Are Educate Humanities)._
https://www.facebook.com/100495222137315/posts/100496042137233/?substory_index=1&sfnsn=mo

                  *[📝I.W.A📝]*

بسم الله الرحمن الر حيم

   _Deducated to my sweet Mamah😍_.

  _31_
Cikin sauri ta karasa wajen, sai dai abun tashin hankalin, kamar ba wajen bane dan ta kasa gane inane tayi bunnin, domin kamar inyi wani dan gini ne awajen, hannu ta dora akan tana son sakin ihu, da sauri kuma ta maida hannun kan bakinta ta rife wani irin kuka na kufce mata.
  Ba mamaki ashe Malik ya fara dawowa hankalinsa, har yayi tunanin dawowa gida, yanzu fargabarta daya kar ya tuna da Maryam, da abun cikinta daya bari, zaman dirshan tayi agun tana sakin kuka, sai can dabarar kiran Mamanta ta fado mata.

   Tashi tayi ta goge hawayenta ta lalubo wayarta daga cikin jaka, kiran Mamannata tayi, tana dagawa bata jira abunma da zata ce ba, ta sakar mata kuka, tana fada mata abun dake faruwa.
   Ashar Maman tata ta saki cikin fada tace,
  "Saddiqu ne, wllh Saddiqu ne kuma sainaci abun uban yaron nan, shi ya rusa min shiri na, shege dan daba ki barni dashi, yanzu ki lallaba ki zauna, idan na gama da Saddiqu zan dawo kan mijinnaki, karki wani daga hankalinki."

   Rarrashinta tayi sosai sannan sukayi sallama, bangarensu ta nufa, tana kiyasta yanda zata kuma juyar da hankalin Malik daga kan kowa na gidan.

Watansu biyu da zuwa su Maryam suka sauka suma, sai dai tunda tazo Khausar ta sata agaba da kayan mata, sai da tayi sati biyu sannan ta sarara mata, nan suka shiryawa zuwa Maiduguri, gaba daya har yaran dan zuwa lokacin sun samu hutu suma.

   Sai ranar da zasu tafi sannan suka hadu da Malik, gabanta na wata irin faduwa ta ke kallonsa, shi ma ido ya tsura mata yana tunanin 8nda ya santa, dan tabbas kamar yasan fuskar amman bazai iya tunawa ba, kau da kansa yayi ya nufi mota dan hardashi za'ayi tafiyar da Sakeena.

Hawayene ya saukowa Maryam, gogewa tayi ta kalli yaranta dake ta surutu da Sultana, yafitosu tayi da hannu, da gudu suka zo, nuna musu motar daya shiga tayi tace" kunga wani can yana kiranku, kuje ku gaidasa".

   Amsawa sukayi sannan suka nufi motar, sai dai kafin su karasa har anja motar anyi gaba, bin motar tayi da kallo wani tukukin bakin ciki na dukanta, kafadarta aka dan bangaza, ta juya da sauri, ido hudu sukayi da Sakeena da take sakin murmushin mugunta,
  "An fada miki wai zaku samu kanshi ne cikin sauki har haka?, kinyi kuskure, dan Malik nawa ne ni kadai, duk macen data rabe sa, zata mutu kuwa agwauruwa."
Murushi Maryam tayi ta na dauke kanta, sannan tace "idan kin isa, ki tsince jinina dake yawo ajikinsa, sannan ki haramtawa wadannan yaran jin dumin mahaifinsu, ni da Allah na dogara kuma shi zai taimaka min ako da yaushe, ki abunki babu abun da zai faru sai abun da Allah ya tsara."

   Wuceta tayi ta nufi motar dasu Khausar suka shiga, zama tayi tana sauke ajiyar zuciya, sannan ta kalli Laura tace"wallahi kin taimaki kanki da kika raba hanya da waccan mahaukaciyar, da ace zata nutsu ta dawo kamar ke ai da kowa ya jata ajiki, amman ayi mutum babu komai aransa sai son zuciya , da neman duniya, Allah ya kyauta."

   Sunkuyar da kai Laura tayi cikin sanyin murya tace "kiyi hakuri daduk abun dake faruwa, komai mai wucewa ne."

Kai tadan jinjina sannan suka fara wata hirar, dai dai nan Mamah ta shigo motar sannan Sakeena ta shiga suka dau hanya.

   Misalin daya na rana suka isa, sun samu tarba mai kyau, sai da suka nutsu sannan aka fara gaggaisawa, anan suka hadu da Saddiqu daya dauki Ikram ya rike hannun Iklas, yana jin soyayyar yaran har jininsa, suna tsaye suna gaisawa yana tambayarta yaushe tazo, fuskarta dauke da murmushi tace,
  "Kwanan mu kusan sha shida ai da zuwa, ya aiki ya iyali?."

  Dariya ya danyi yace"iyali..?, tab sai dai acikin kawayenki ki samon wata, wadda zata iya da tuzurantaka na, har yau dai babu wani batu akan iyali."

   Dariya itama tayi tace"shikenan to, na baka Ummie in tayi maka sai kawa Abbah magana musha biki."

  Kai ya girgiza yace "sake wata wannan Gidado ne yake so, ki zabon wata dai."

  Dariya kawai ta kuma yi tace "zamuyi maganar daga baya, amman nidai Ummie nasan ita ce zata dace da kai, kyawawan halayenta kamar na marigayiya ne, tana da nagartattun halayen da ni kaina da ina da wa, wanda muke ciki daya da sai na mai kamu, amman tunda gaka tabbas zata zama mallakinka, rabu da batun Gidado, Ummie ba tada hayaniya ba zata iya daukar fadan Salme ba, kawai kayi shiri dan wllh sai na hada maka bomb awajen Abbah."
  Ta karasa fada tana mai dariyar mugunta, kai kawai ya kada yana murmushi, shi kansa bai isa yaki ummie ba, domin yasan idan ya aureta yayi babban dace, sai dai yana tsoro, yana tsoron ranar da yaransa zasu tashi amusu gorin cewa babansu tsohon dan ta'adda ne, ajiyar zuciya ya sauke sannan yaja hannun yaran suka fita.

   Duk abun da suke akan idon Malik, tunani yake tabbas ya san wadannan fuskokin, amman a ina, ganin zai batawa kansa lokaci yai wucewarsa shi ma, sai dai yaran dake hannun wannan mutumin daya gani sun tsaye masa arai, suna kama sosai Mamah, kau da zancen yake son yi amman ya kasa, da haka shima yabar wajen.

   Kwanansu hudu da zuwa aka zauna zaman mitin, anan aka gabatarwa da Saddiqu auren Ummie, sai Fannah da dan Alhaji Yahya kanin baban Saddiqu, auren dai mutane da dama aka tsayar da za'ayi nan da sati biyu masu zuwa, kallon kallo ake tsakanin kowa da kowa, sai dai babu mai magana, dolene kowa ya karbi zabin da aka masa.

  Bayan an tashi taron ne, Malki ya samu Mamah abangaren Maman Saddiqu suna zaune afalo gaba dayansu harsu Maryam, zama yai yana gyaran murya, kallonshi Mamah tayi ya dauke kai, kamar bashi ba kuma yace,
"Waccan wace ne mai yara biyu mata?, na ganta agidanmu kafin mu taho nan."
  Kallon ba kada kai Mamah tayi masa, sai Khausar ce cikin mamaki tace"badai kace harka manta da Maryam din taka ba?, wacce ka tafi ka bari da cikin wata uku, ka tuan?".

   Tabe baki yayi yace"banda sakeena ina da wata matar ne, ban santa ba, sai dai in so kuke dai na kara aure, zaku fake da wannan, wannan mitsitsiyar yarinyar za'a ce wai Maryam dina, kamar dai na san mai sunan, amman ba zan iya tunawa ba."

  Kallon mamaki Maman Saddiqu tamai kafin ta maida kanta ga Mamah data kafe sa da ido, kafadarta ta dafa, suka kalli juna ta mata alamar ta biyo ta.

  Bayan sun shiga daki ne ta kalli Mamah tace"ya akayi kika bari sihiri ya taba miki lafiyar danki haka, gashi nan abu mai mahimmanci ya manta dashi, zan hadaki da kanin babana, babban malami ne inshaAllah za'a shawo kan lamarin."

   Shiru Mamah tayi tana nazarin maganar Maman Saddiqu, kafin suka shiga tattauna abun daya faru tun shekaru hudu baya da suka wuce.

*RUGAR SAJE*Where stories live. Discover now