*RUGAR SAJE*By Nusaiba Ayuba Suleiman
Wattpad@nusysa
IG@Nusaiba A.S.Sarkin zango.*FITTATU 18📚 2 0 2 1💥*
⚖
*HOME OF QUALITIE'S WRITER'S ASSO📚*
'''{{The Home Of Qualitative Writers That Are Educate Humanities}}'''
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=106249334371950&substory_index=0&id=106248871038663&sfnsn=mo
*⚜️{{H.Q.W.A📚}}✍️*بسم الله الرحمن الر حيم.
_Deducated to my sweet Mamah😍_.
_12_
Bayan an dawo daga daurin aurenne, aka kuma taruwa ababban falo, sai da Malik ya kuma ganin Mairoji da idonsa sannan ya yarda ba mafarki ne ko gizo ba, Baba Lawan ne ya bude taro da addu'a, sannan ya tambayi Malik dangantakarsa da Mairoji, babu wani dogon bayani ya fada musu yanda suke da ita, take wajen ya kaure da hayaniyar murna, sai da Baba Bulama ya yi magana sannan akayi shiru, Ahj Bara'u ne yai gyaran murya yace"to Abdulmalik kamar yanda ka fada mana dangantakarku, muma nan zamu fada maka dankantakarmu daku biyun duk da ita Maryam din ta sani, kaine dai baka sani ba".
Nan ya sanar da Malik yanda suke, da kuma yanda su Mairoji suka zo hannunsu, kamar yadda Kawu ya musu bayani. Idon Malik taf da tsantsar tausayinsu yake kallonta kamar ya maidata ciki, haka yake ji.Bikin sai ya zamana anyi shi cike da jin dadi, domin kowa ka gani da farin cikin faruwar abubuwa da dama atare dashi.
+++
Bayan sati komai ya gama kintsuwa na hidimar da akayi, sannan ne aka fara haramar zuwa can Dutse tunda Malam Ahaji ya koma can da zama, babu yanda Mairoji batayi ba da Malik ya kira mata Goggoji awaya yaki, ta nemi ya bata lambar da zata samu wani na gidan ma amman yaki, yace bazata yake son yi musu ne.
Sauran kwana biyu su tafi haka ya dauketa da sauran yan matan family da zuwansa gidan duk suka tare agidan, domin ba kyarya, ya tafi da imanin da dama daga cikinsu, ko da suka fito za'a tafi ma sai da wata Sakeena ta bata mai rai, abin daya faru kuwan.Sun fito sai Mairoji ta bude gidan gaba zata shiga, zaraf sai sakeenan ta rike murfin motar tace wa Mairoji ta koma baya, to ta girme mata, sai batayi musu ba juya zata shiga bayan, shi kuma yana ganinsu tunda yana mazaunin direba ne, bai kula su ba sai data shogo ta zauna ne sannan shi kuma yace ta koma baya itama, kallonsa tayi taga kamar bashi yai magana ba, ita ma sai ta dauke kanta, dan ta nuna mai tanada aji , ransa ne ya baci dan bai fiya son yana maimaita magana daya ba kamar karamin mutum, kin tada motar yayi , a karshe ma sai ya fita ya koma kusa da maigadi ya zauna yana laluben waya.
Takaici ne yasa Sakeena fitowa tana watsawa Mairoji kallon tace "saiki koma gaban ai, sai kuci uwar da zaku ci".Ita dai Mairoji ba tace uffan ba ta koma gaba ta zauna, sauran yan matan suna kallonsu, daga masu hararar Sakeena sai masu hararar Mairoji, kamar mintuna biyar sannan ya shigo ya tayar suka tafi.
Wani babban Supermarket ya kaisu, yana cikin motar bai fita ba dan yaga wajen da mutane, kuma yana fita zai janyowa kansa hayaniya, cemusu yai kowacce taje ta dibi abinda take so, har sun fita ya kira Mairoji ya bata card dinsa bayan ya fada mata code din da zata sa, sannan suka shiga cikin wajen.
Suna shiga kuwa Sakeena ta karbe card din tana harararta, murmushi tayi aranta tace 'zaki dawo dashi ne' . Kaya suka zage suna diba kamar ance musu kyautane, abin harda hauka da fariya, masu hankalin cikinsu sune suke daukar abun da zai amfane su.
Mairoji kam, bangare turare ta nufa wani mai dan karen dadi ta dauka, irin na maza, sai agogo na maza, mai kyau da tsada, sai necktie, ko wanne hurhudu ta dauka, sai bangaren abin hannu dana kafa, ta zabi masu kyau kusan set uku, iya abin data dauka kenan,sai man zafi data dibarwa Goggoji, dan tace shi kadai zata kai mata tsaraba, sai bangaren kwalam data nufa, anan suka ci karo dashi, dan da fari bata gane sa ba, sai daya dago kansa sannan ta gansa, riga mai hula ce ya dora akan kayansa, ya rufe kusan rabin fuskarsa, kallo daya ya mata ya dauke kai yana kallon tarkace cakulatin data kusan cika kwandon hannunta dashi, rabawa yai ya wuce wajen jallabiyun mata da jakkunkuna.
YOU ARE READING
*RUGAR SAJE*
Non-Fictionsarkakiyar soyayya da zumunta mai hade da cin amana, shiga ciki ka karanta tsantsar soyayya, da tarin sadaukarwa.