*RUGAR SAJE*By Nusaiba Ayuba Suleiman
Wattpad@nusysa
IG@Nusaiba A.S.Sarkin zango.*FITTATU 18📚 2 0 2 1💥*
⚖
*HOME OF QUALITIE'S WRITER'S ASSO📚*
'''{{The Home Of Qualitative Writers That Are Educate Humanities}}'''
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=106249334371950&substory_index=0&id=106248871038663&sfnsn=mo
*⚜️{{H.Q.W.A📚}}✍️*بسم الله الرحمن الر حيم.
_Deducated to my sweet Mamah😍_.
_24_
Kiran sallar la'asar ne ya tadashi, ahankali ya sauke idonsa akanta, lumshesu yayi ya kuma budewa akanta yanajin sabon shauki da kaunarta na ratsashi.
Gashinta daya dan hauro saman goshinta ya gyara mata, shi sai lokacin ma yaji jikinta zafi dauu, da sauri ya mike yana kiran sunan Allah, bandaki ya shoga ya fara wanka yayi alwala, sannan yadan hada ruwa mai dan dalmi dalmi,dakin ya dawo yana tunanin ta yanda zai tashe ta, shahada yayi ya karasa bakin gadon yadan rusuna, cikin sigar lallami yake tashinta, kadan ta bude idonta, tana ganinsa tayi saurin mayarwa wasu nlhawaye masu dumi suna sauka akan kumatilunta.
"Miemie....tashi kinji jikinki da zafi taso na taimaka miki".Hannunsa ta buge cikin jin haushinsa tace" bar ni ban so, laifin maye nayi maka da zaka min wannan hukuncin, ko dan kaga ni marainiya ce, shi ne kake min duk muguntar daka ga dama, ni dai ka maidani wajen Mamah kawai".
Tuni ta sakin mai kukan sakalci, shi kuwan ya gama susucewa, dug ya daga hankalinsa, tallafo ta yayi ya hada da jikinsa, gashi itan sai rawan dari take zqzzabin sosai yake son kara haura mata, hannunsa ta kamo ta dora akanta tace "taba kaji shima fa ciwo yake min, ko gashin kaina ma yau ciwo yake min, ga bayana kamar an balle sa nakeji, ni wllh ka ciren wannan ciwon tunda muguntar daka min ya samon ciwon".
Kai ya dafe yana tunanin wai daman haka kowane namiji yasha fama da matarsa adaren da suka hada shinfida, ko kuwan shi ne tasa tazo da wannan salon, ya tuna Sakeena ko kuka bata mai ba, duk daya hada mata da mugunta don ya fahinci ba virging bace, amman bai ga wannan kalam shan wahalan ba awajenta.
Da dabara da lallami ta kaita bandakin, tawul ya ke tsomawa yana dan shafa mata ajikin dan zazzabin ya samu daman sauka, duk sai wani nonnokewa take tana kare kirjinta, gashi tana son matse kafafunta amman ta kasa, shi kuwa sai wajen yake kallo uana tuna dumi da gardin dadin daya gama kwasa yan awannin da suka wuce.
Kallonta yayi ya tabe baki sai can kuma ya sakin mata ajiyar numfashi yace " uhmmm...gulma ajali, da ina romancewa dake sai kara min speed kike, amman yanzu kinemi tadan hanklai da kukan banza, ko kinmin shiru anan, ko na kara abinda baki so din".Baki ta tura tana kananun gungumi, ga kwallan shogwaban da batasan da zamansa ba sai zubawa yake, bayan yadanji jikin nata dadan dama sai ya hada mata ruwan zafi amman ba can ba, girshi kadan yasa da dan detol kadan, hannunta ya kamo yace,
"Oya tashi ki shiga ruwan zafi kyaji dadin jikinki".Kafada ta makale tace " uhmmm....uhmmm...ni dqi ka barni haka babu abinda zanyi".
Shima baki ya tabe yace"kanki zakiyiwa yarinya, idan wajen yayi funfuna babu ruwana, kinga dai ina da wata matar, zanje qajentane tana bani abinda baki isan kin bani ba, tunda kinbar naki ya rube".Kuka ta sakin mai tana son buga kafarta ba daman, hakan dai ta shiga ruwan dayasata sakin wani wahalhalin kukan ba shiri, hannu take yarfewa tana son tashi acini ruwan, harar ya maka mata hakan ne yasa ta nutsu.
Sai daya hada mata ruwan har sau uku ya tabbata taji dadin jikintan sosai sannan ya barta ta idasa wankan tsarki.
Few minutes ta fito daure da towel, sai wani ahannunta tana goge kanta dashi, dangisa kafarta take dan bata iya takata sosai, kallonta yake yana daga kan sallaya, hannu ya mika mata kan tazo, sai ta make kafada tana tabe baki zata sakan mai kukan da baya so, tamke fuska yayi yana mata nuni dakan gado, hadiye kukan tayi ta koma bakin gadon ta zauna, tana saken ajiyar zuciya, sai daya gama shafa adduoinsa sannan ya dauko mata doguwar riga da kayan ciki, shima sai da kyar ta yarda yasa mata, sannan ta tada sallar la'asar, kafin ta idar sai gashi da tire mai dauke da madaidaicin kofi da shayi aciki yana turiri, sai sandwich akan gefe da spoon sai wani dan kananun kwayan magana awata yar gwalba.
Ajiyewa yayi harta kammala, sannan ya dawo kusan da ita ya soma bata, tana gama ci kuwan ta fara kelawa amai awajen, sai data gama ne sannan ya taimaka mata ta dauraye bakinta ta koma kan bed shi kuma ya gyara wajen.
Haka dai ya ke hidima da ita har magrib, sannan ya fita, kafin ya dawo kuwan ta koma dakinta tanayin sallar isha ta dane gado ta kudundune dan wani rikitaccen zazzabi ne yake hawan mata kai.
Shi kuwan bai shigo gidan ba sai wajen goma na dare, kai tsaye dakinta ya nufa dai dai ya shiga yaga wani ya fito daga bandaki da shortnikker ajikinsa sai towel da yake goge suman kansa, kan yayi magana har ya bangajesa ya fita da gudu, mai da dubansa yayi kan Maryam da take sauke nunfashi da kyar da alama zazzabin ne yake dawainiya da ita, sai dai daga ita sai wani karamin siket iya cinyarta sai rigar da bata gama sauka kan cibiyarta ba.
Numfashi mai zafi ya fesar sannan ya fita da sauri, dai dai bakin get ya hango wannan gayen ya fita da gudu, shima bayansa yabi, nan suka kafa yar tsere, abinka da dan ball ya saba guje guje, sai gudun bai masa wuya ba, ya kusan kamasa kenan wata mota data shawo kwana ta daukesa sama, sai daya gama wahala asaman sannan ya fado baya munfashi, da gudu ya karasa kan sa yana dan jijjigasa, taba kirjinsa yayi yaji zuciyarsa tana harbawa kadan kadan, da sauri ya kira motar asibiti anan suka zo suka daukesa, shoma Malik din binsu yai sai dayaga dakin da aka shigar da gayen sannan ya tafi gida zuciyarsa cike da rudani da tunaninnika.
Dakin Maryam din dai ya sake komawa nan ya kwanta agefenta yana sauke ajiyar zuciya, yanzu kam ya tabbatar da cewa ana hada musu gadar zare ne, kuma tabbas na kusa dashi ne ke hada mai, amman baya son ya zargi kowa tukun har sai ya gama bincikensa.
Washe gari da safe haka ya kuma komawa asibitin nan suka tabbatar mai jikin da sauki sannan zai iya farkawama akowane lokaci daman buguwace tasashi suma, sai yada kafatawa ma'aikatan wajen kashedin kula dashi sannan ya bar asibitin.
YOU ARE READING
*RUGAR SAJE*
Non-Fictionsarkakiyar soyayya da zumunta mai hade da cin amana, shiga ciki ka karanta tsantsar soyayya, da tarin sadaukarwa.