*RUGAR SAJE*By Nusaiba Ayuba Suleiman
Wattpad@nusysa
IG@Nusaiba .A.S.Sarkin zango*FITTATU 18📚 2 0 2 1💥*
⚖
*HOME OF QUALITIE'S WRITER'S ASSO📚*
'''{{The Home Of Qualitative Writers That Are Educate Humanities}}'''
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=106249334371950&substory_index=0&id=106248871038663&sfnsn=mo
*⚜️{{H.Q.W.A📚}}✍️*
بسم الله الر حمن الر حيم._Deducated to my sweet Mamah😍_
_9_
Sai bayan sun kuma samun nutsuwa ne sannan Bulama yacewa Kawu da Mairoji zai koma, nan shima Kawu ya nuna bai yarda ba, da kyar dai suka bar maganar kan cewa zata zauna ne, kafin Simrah tayi kwari sai Uncle Mahmud yazo ya kaita taga yan uwa.
Da wannan shawarar aka tsaida magana, bayan adduar bakwai suka koma bayan sun bawa Mairoji makudan kudade, sun kuma bude mata acc, Salme kam tuni ta gama shan jinin jikinta, sai yanzu ta gane dawa take zaune, ada tana ganin kamar iya Mairoji kadai akawa alfarmar zama agidan Kawu, amman yanzu ta gane ita akawa alfarmar, kuma ita ke cin arziki azaman gidan, hakan yasa ta rusunar da kai tare da yada duk wani makamin ganin tafi Mairoji, sai dai abun daya ke kara bata haushi yanda kowa na gidan yake nan nan da Mairoji, soyayya ta musanman suke bata, ko kadan basason ganin tayi shiru ko tana tunani, yanzun zasu fara shiga damuwa kowa na nuna kulawarsa akanta.Da fari ta dauke kanta, sai dai ganin abunda aka aiko mata daga Maid sai ya hautsina tunanin Salmen, sabuwar mota yar yayi ta zamani dai dai hawan mace, ita Kawu Bulama ya aiko mata dan fita, Salme taji takaicin wannan abu, ita aganinta wannan ai wariyar launin fata ce, da nuna Mairojin tafi ta, ko yaushe da wannan bakin cikin take kwana take tashi.
+++
"Ke Laure...na fada miki ki dena shafan hoda, Allah zan hadaki da Mama, ga naki kayan kyalin can amman saikina taban nawa".Harara Laure ta makawa Ummie cikin fada tace " amman wllh ke dai anyi yar bakin ciki, yanzu idan banyi kwalliya yanda zanyi kyau na fito amace ba, taya wancen mai kyan usulin ya tanka, Allah Ummie ina matukar son Ya Ahmad, nifa idan bashi na auraba...to bani babu aire, kuma shima haka, dan bazan bari wata ta aure sa ba ina gani".
Baki Ummie ta rike, tana mata kallon baki da kai, daman ba tun yanzu ba tasan Laure tana son Ya Ahmad, sai dai bata zata abun yakai har tayi ikirarin idan bata same sa ba , ba bu mai samunsa. Zama ta gyara tace "Laure shawarar dazan baki, wllh ki kama kanki, kinga Ya Malik yafi Ya Ahmad fada da masifa, amman hakan ba yana nufin Ya Ahmad bai da fada ba, kinsan halinsa idan ya ganoki tsab zai iya maidake Ruga kije ki karasa rayuwarki acan, kuma banda abinki ai kwarya tabi kwarya, ina ke ina nagartaccen namiji irin ya Ahmad, Allah ki raba kanki da wannan shirmen naki dan babu inda zai kaiki".
Juyowa Laure tayi tana kallon Ummie, murmushi ta saki sannan tace " ban taba zaton kina cikin masu mini hassada ba Ummie, amman yau kin fallasa kanki, wllh kamar abakin Hajiya, sai na fada mata, karfa ki manta dalilin zuwan mu gidannan, ke kisan yanda zaki janyo hankalin Malik ya soki, ni kuma Ya Ahmad ya so ni, kinga damu da uwarmu duk mun huta, mun auri matasan dake jin da gayu da naira, matsan da ake ji dasu akaf fadin garin Dutse, kiyi tunani da kyau, idan kuma bakin ciki da kyashi zaki tsaya, sai nace Allah bada sa'a".
Baki Ummie ta saki tana binta da kallon mamaki, ta san dalilin da Hajiya Tako ta turosu Dutse, dan su aure yaran Baba Badamasi, amman ita kam bata jin zata iya bada kanta ta nuna tana son namiji, karatunta tasa agaba idan Malik ya nuna yana ra'ayinta, tabbas zatayi farin ciki, idan kuma bai nuna ba, amatsayinta na kanwarsa zata mai addu 'ar Allah ya kawo masa mace ta gari, ita ma haka, amman ba zata iya aikata abinda Hajiya ta turo su yi ba.
Tashi tayi ta nufi bandaki ba ta kuma bi takan Laure da take feshe jikinta da turararruka ba.Kasa ta sauko jin muryansu suna ta faman hayaniya, duk da ba masoya hayaniyar bane amman idan suka hadu da juna, kamar sa cinye namansu danye, cikin tafiya mai daukar hankali take takowa, har ta karaso inda suke, sallama ta musu bayan ta zauna akujerar dake fuskantar ta Ya Ahmad, wayarta ta dauka tana danne danne, dudka hankalinta daya tafi ga jarumin nata, sai dai abin takaicin ko kallo bata ishesaba, karshe ma tashi yayi yacewa Malik yazi ya rakashi wani waje.
Kamar ta fasa ihu haka taji, amman dake tana dauke ne da shawarar Hajiya akanta sai tayi saurin cewa"laa...Yaya nazo na rakaku mana, daman ina son yin siyayy...."wani banzan kallo Malik ya aika mata dashi, kafin ya saki tsaki ya fice daga falon, Ya Ahmad kam tuni daman ya fice ko sauraron shirmenta ma baiyi ba.
Yana fita ya fara mita"wllh wannan yarinyar ta kusan barin gidannan, wannan inskanc8n nata bazan dauka ba, ayi yarinya babu wani kamun kai, sai rashin tarbiyya da rashin kunya!".
Ahmad bai magana ba sai da suka shiga mota ya tayar, sannan ya dan kallin gefen da Malik yake yace "ba zata bar gidannan ba, amman zatayi danasanin zaman ta agidan, ba nason ka kuma nuna mata komai".
Da haka suka fita taga gidan, Ahmad na taisar Malik dan ya dau zafi da abun.
.++++
Bayan shekara biyu, Mairoji Simrah tayi wayau sosai, wanda alokacin ne Mairoji ta gama sakandari, inda Kawu Bulama ya nemi data koma can Maid da zama, badan sunso ba haka aka fara shirin komawarta can, ga bikin Anti Shahuda da za'ayi da Ya Salman, kuma can Maid din zasu ayi komai acan.
Lokaci na karatowa har tafiyarsu ta zama saura kwana uku, dan idan sunje da sati za'a fata biki.
Kuyi hakuri, wllh banda lfy ne, kuma kunsan sanyi ake, ina da mara lfy, shiyasa kuka jini shiru, kuma typing din kadan, afuwa🙏
YOU ARE READING
*RUGAR SAJE*
Non-Fictionsarkakiyar soyayya da zumunta mai hade da cin amana, shiga ciki ka karanta tsantsar soyayya, da tarin sadaukarwa.