page 3

17 2 0
                                    

*RUGAR SAJE*

    By Nusaiba Ayuba Suleiman

Wattpad@nusysa
IG@Nusaiba A.S. Sarkin zango

*FITTATU 18📚 2 0 2 1💥*


*HOME OF QUALITIE'S WRITER'S ASSO📚*
'''{{The Home Of Qualitative Writers That Are Educate Humanities}}'''
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=106249334371950&substory_index=0&id=106248871038663&sfnsn=mo
         
            *⚜️{{H.Q.W.A📚}}✍️* 

بسم الله الرحمن الر حيم.

_Deducated to my sweet Mamah😍_
      _3_
Kwanan su Mairoji shida mutanen nan suka kuma daukesu sukayi gaba dasu,can yankin maiduguri suka yada zango, amman cikin unguwar umalare, sai dai wannan karon gidane babba mai dakuna kusai bakwai, iya su kadaine aciki sai ko yaransa da suka rarrabu.

     Kullum banda kuka babu abin da suke yi, sun rokesu akan su maida su ga ahalinsu, amman sai ogan yayi dariya kawai, yace "ai mun gamu kenan, ku da danginku sai dai alahira, nan da shekara uku zaki zama matata, bayan wata tara kuma ki haifa mi yaro, dan an miji nake so ahaihuwar farko, wanda zai gaje ni, dan haka ku fitar da ran komawa wannan kazamar Rugar taku".

    Gaba daya dariya yaransa suka sa, suna nuna su Mairoji , wani kallo ogan ya musu nan danan sukayi shiru kowa ya koma bakin aikinsa, ahaka suke rayuwa kamar wasu marasa gata, kusan wata guda kenan Bad'ejo na fama da kanta, tun lokacin da abun ya faru take halin cuta,  sunyi tunanin rashin lafiya ne dako wace mace takeyi yayinda aka karbi budurcinta, sai dai ganin abun bana kare bane Mairoji da take ganin kanta wayayya acikinsu, tunda tayi karamar sakandire tuni tsohon karatun da aka dan taba ya motsa.

    Matsowa tayi kusa da Bad'ejon tace " ha...mu gani".
   Ba musu kuwan ta bude bakinta, nan Mairojin ta gama dube duben ta sannan tace ta rufe, idan ta ta dan bude ta duba gefe da gefe sannan ta tashi tana kallon oga daya fito daga bandaki, tabe baki tayi tace "malam sai ka fara tanadin kayan yaro da kuma ragon suna, da abin da za'a ci, da wallahi inta sauka lfy sai munyi taron suna".

    Kallon rashin fahimta yayi mata ya dauke kai, har zai shiga daki kuma sai ya juyo yace" wai dani kike...?"

Cike da turawa mutum haushi tace "ah...ah, da inuwarka nake".

   Murmushi yayi kawai ya shige daki, dan yanzu shi kam, wata irin soyayyarta ke dawainiya dashi.

    Kallonta bad'ejo tayi ta sa kuka tace " dan Allah Mairoji ke taimakan na zubda cikinnan, wallahi idan na koma da dan shege ruga kema kinsan kashe ni za'ai, ki taimaka karna haifi abinda zai zo ya zaman kalu bale ga rayiwata".

    Tsugunnawa Mairoji tayi tadan rungumo kanta, tana shafa bayanta alamar rarrashi, cikin kwantar da murya tace"kar ki damu bad'ejo muna tare dake, ba za'a zubar da cikinba dole.ne ki haifesa, sai dan da za'a haifa ya zame musu babban kalubale ga rayuwarsu, insha Allah ba bu wanda zai miki koda banxan kallo, bare yai tunanin cutar dake idan muka koma Ruga".

   Da kyar dai ta rarrasheta ita da salme dayar abokiyar tasu.

++++
   

     Da d'an sassarfa ya karaso wajen kujerun da aka ajiye dan hutawa, robar ruwa ya dauka ya kafa wa bakinsa, bai sauke ba sai da ya shanye shi tas, sannan yadau wani dan towel yana tsane dan gumin daya dan tsattsafo mai.
   Kallonsa k2 yayi cikin shakiyanci yace, "ya dai man.....ka fara tunanin wasan ne, naga sai zabgewa kake, ko dai aljanar take ce ta kawo maka ziyara take tsotseka ne bamu sani ba".

   Tsaki Malik yayi ya tashi ma yabar wajen yaci gaba da zagayen da yake, dariya k2 da sauran abokan wasansu suka sa masa, Kamal yace " kai guys ku dena dariya fa, gaskiya ku kula da MBM yana cikin damuwa, duk da bai damu da magana ba amman yanayinsa kadai ya nuna yana da damuwa, kune abokansa na jiki ku zaku fuskancesa ku gane mai yake damunsa".

      Shiru K2 yayi yana nazarin abinda Kamal ya fada, tashi yai ya bi bayan Malik din suna gewaye cikin sassarfa amman K2 yana kule dashi, tabbas yaga yana cikin damuwa amman yasan halinsa bazai taba fada masa ba, har yamma suna atisayen kafin kowa ya kama gabansa, kwanan biyar ya rage musu zasu fara karamin wasa, da kungiyar Bounmuth.

+++

    Ayanzu kam su Mairoji har sun fara sabawa da zaman Maiduguri, duk da basu taba futaba tunda suka zo, kusan wata biyu kenan, ga laulayi da ya sako Bad'ejo agaba, kamar ba zata kai ba, da haka suke rayuwarsu cike da takura, duk dama ba bu wani abu da ake musu na rashin kyautatawa.

    Yau garin sun tashi da fargabar wai wasu yan bindiga sun shigo, tun daren jiya oga suka fita shi da yaransa, sai suka kulle gidan ta waje, to basu kwanan agida ba har gari ya waye, wajen goma na safe aka fara harbe harbe, ga karar tashin boma bomai daya karade unguwanni, kuka Bad'ejo tasaka ta kamo hannun Mairoji tace mata"dan Allah karki bari wani abu ya same mu, kiyi wani abun kina jin mutane unguwa sai gudu suke, amman mu an kulle mu acikin gida, ina da buri akan wannan cikin na jikina,  so nake ya zame min makamin da zan yaki wannan azzalumin dashi, ki taimaka mana mu bar nan dan Allah".

   Ita kanta Mairojin duk dauriyar sai gashi tasa kuka, ta tabbata yau kam tasu ta kare, dan babu makawa mutuwa zasuyi awannan gidan.
 
   Tashi tayi tana bin  gidan da kallo cike da nazari, ta cen wajen bandaki katangar ba tada tsayi sosai, sai bata san ta cen baya ba kuma ya take, tsanin dake jingine agefe ta fara kokarin dauka sai dai yafi karfinta, hakan yasa ta kira Salme ta taimaka mata suka daga shi, suka jingina shi, sai data fara lekawa ta ga yanda tsahon katangar take ta baya sannan ta sauko, Salme tace ta fara hawa ta dira, sannan Bad'ejo sai ita ta karshe, ganin mata da yara na gudu kawai suma sai suka shiga cikinsu.

     Tun hantsi suke gudun ceton rai, basu yada zango ba sai kusan  la'asar, lokacin sun bar cikin gari sun shiga jeji, ga k'ayoyi da suka taka, dan Mairoji ma jin babban dan yatsanta take kamar ba'a jikinta yake ba, sai da suka tabbatar da sun tsira sannan suka zazzauna ajikin wani dutse, ban da kishi da yunwa ga gajiya da bakar azabar da kafafun su ke musu.

    Bad'ejo kam tun tana  amai da kuzarinta har ta koma kakari, dan babu komai acikinta, wata matashiya haka acikin wadanda suka tsira ta kalli yanda Bad'ejon ta lafe ajikin Mairoji tana sauke ajiyar numfashi da kyar, cike da tausayinsu tace"sannunku....ina kuka nufa daga nan?".

    Cikin haki Samle tace"Rugar Saje muke son komawa, amman bamu san hanya ba daga nan".

Cikin kulawa, matashiyar tace"awane gari kenan, dan nan fa muna cikin Maiduguri ne, kuma ni haifaffiyar nan ce, ban taba jin sunan wannan garin ba".

Mairoji da tadan fisu sanin sunan garuruwa tace"amakartar mu dai nasan wani malami dayake zuwa daga Kano, yace mana babu nisa sosai tsakaninmu da da garin, kuma garin da yayan babata yake akwai duwatsu, sosai dan wani ma kamar ya fado miki idan kina tafiya".

   Jinjina kai tayi , aranta tace"maybe irin yan mazauna kan karshen kanon nan ne, kuma garin da take nufi, ko can Dala ne, tunda ai akwai sauran duwatsu har yanzu acan.

    Dafa Mairoji tayi ta mata murmushi, tace"shikenan ni ma wan babana yana kano ne, kuma nima can zan koma, inshaAllah sai mu tafi tare, kafin agano inda kuke sai akaiku".

    Cike da murna suke ta mata godiya, sannan suka kuma daukar hanya suka nausa, dan so suke, su isa bakin titi kowa sai ya kama inda ya nufa.
    Kuyi hakuri mutuwa aka mana sai yau na samu damar muku update, sory 4keep you waiting guys.🙏
    

*RUGAR SAJE*Where stories live. Discover now