*RUGAR SAJE*
By Nusaiba Ayuba Suleiman
Wattpad@nusysa
IG@Nusaiba A.S.Sarkin zango.*FITTATU 18📚 2 0 2 1💥*
⚖
*HOME OF QUALITIE'S WRITER'S ASSO📚*
'''{{The Home Of Qualitative Writers That Are Educate Humanities}}'''
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=106249334371950&substory_index=0&id=106248871038663&sfnsn=mo
*⚜️{{H.Q.W.A📚}}✍️*بسم الله الرحمن الر حيم.
_Deducated to my sweet Mamah😍_.
_16_
Wannan abu da Ahmad yayai ya batawa Mairoji rai, domin gani take ai shima yana sonta, to dan me zai auri wata bayan gata, hakan yasa taki dawowa garin Dutse, domin karfi da yaji take jin kishin Khausar, gefe guda kuma tanajin tausayin Malik, dan ita kadai tasan waya aura, adan zaman da tayi dasu, ta fuskanci inda ita kanta babar Sakeenan ta dosa, mace ce ba mai tsoron Allah ba, indai bukatarta zata biya , burinta zai cika ba tada damuwa da duk abin da zai faru, kyma tana iya karar da komai nata don samun farin cikin yaranta.Abangaren Laura kam, sosai Hajiya take tsumata da abubuwa, domin a irin hudubar data mata tace ko kanta ne ta bawa Ahmad din, indai hakan zai janyo ra'ayinsa kanta, Mamah na kula da duk take takensu, sai dai bata daga hankaliba, dom8n Allah ta rike, kuma tasan zai dubi yaranta ya kare mata su aduk inda suke.
______
Malik&Sakeena
______Ranar da suka sauka aSpain tayi zaton Malik zai kaita iri wajen shakatawan nan da wuraren ban sha'awa, amman sai taga ba inda suka je, sai shi ne ma ya dan fita bai dade ba kuma ya dawo, shi ma kuma tun daga ranar bata kuma sanyashi a idonta ba sai da akayi kusan kwana biyar, sannan ne ta gansa ya shigo da kayan kanana, yana tsane jikinsa da wani dan shawel, da alama ya dan motsa jiki ne.
Da dare yayi taci uban kwalliya da wata rigar barci, ta nufi dakinsa yana fitowa daga wanka kenan ita kuma tana shiga, kallonta ya tsaya yi yana jin wata sabuwar tsanarta na shigar mai, ita ko kadan fa bata burgesa, yayi yayi ya sata aransa ko yaya ne amman ya kasa.
Takowa tayi har gabansa, cike da kirsa ta dora hannunta akan kirjinsa tana kashe masa ido, murmushi yai mata bawai dan ta burge sa ba, ah ah , sai don yana son yau ya kurewa iskancinta, cikin nasa salon mai tafiya da ita ya rungumo ta jikinsa, sannan sunka dangana da gadon dake tsakiyar dakin.
Tun tana jinta duniyar sama, sai ga ta ta fara neman dauki, hakuri take basa tana kuka da iya karfinta amman ko gizau baiyi ba, haushin ta da tsanarta sune suke kuma samun mazauni azuciyarsa, bai taba zina ba bai san yanda mace take ba, amman ayau ya tabbatar ya hadu da macen da ta watsar da kanta atiti, tunawa dayai da Maryam dinsa tuni wata kuzari ta kuma kwasarsa, yanajin bai kai ya sauka akanta ba haka, ya kamata ya nuna mata a maza ma akwai namiji.
So yake ya kawar mata da duk wata banzar tunani dantake yi akan maza, mazan ma ai suna suka tara, to shi kam yana cikin mazan da ba a isa a raina iyawar su ba, sai daya tabbatar ya sauke mata duk wani motsi dake kanta sannan ya sarara ya barta yana kuma jin tsanarta.
Bayan ya fito daga bandaki ne, ya kalle ta sai sauke ajiyar zuciya take, kallon banza ya mata ya dauke kai yana karasawa jikin wadrop dinsa,
"Ki tashi ki wuce kichin, abun ci nake so mai dan nauyi, yunwa nake ji, nazo nayi aikin da babu abun daya karamin sai yasar min dan abin dan ci akai, maza ki tashi karki batan lokaci".Kallonsa take da mamaki sannan ta kalli agogo sha daya da arba'in na dare, tana shirin mai magana ya juwo yana watsa mata kallon da yasa ta yunkurawa ba shiri tana ciza baki.
Fita tayi tana dafa bango dan j8n kafafunta take kamar ba'a jikinta suke ba, da harara ya bita yana banka mata tsaki, sarai ta ji sa, sai dai ba tada yanda zatayi burinta kawai ya gama shigowa hannunta, alokacin ko kallon Mairoji ba zata yarda ya sakeyi ba balle yai tunanin dawo da ita cikin rayuwarsa.Tuwon semo tayi, dan taga akwai garin, sai miyar alayyahu da tamai, a ido kam miyar gwanin ban sha'awa, dan tasha mai ga kuma daukar kamshi da take, cikin mintuna talatin da wani abun ta gama komai, ta kawo mai har dakinsa, yana kallon miyar yawunsa ya tsinke domin kuwa da gaske yunwar yake ji, abinc8n ya janyo yana taba tuwon ya biyo hannunsa, alamun bai dahu ba, sai bai ji komai ba dan ko iya miyar ma ta isa ya c8 ya sha ruwa.
Yana kai miyar bakinsa yai dan jim, sannan ahankali ya maida ta bakinsa cikin dan bowl din data ajiye mai dan wanke hannu, tashi yai ya je har dakinta ya samu ta fito wanka kenan, hannunta ya kama, har zuwa nasa dakin ya zaunar da ita yace " cinye shi tas, ko digo bana son gani".Kai ta girgiza tace"wllh Yaya dear akoshe nake, kaci kawai".
"Wasa nake dake kenan?maza cinye sa kafin na tattakaki anan".
Jikin ta na rawa ta dibi abincin takai bakinta, ita kanta sai ta kasa hadiye wa, domin kamar tayi barin maggi ne aciki, dan yayi yawa sosai, haka tarugun da tasa kamar sai tsaga mata baki, tashi tayi tana kallonsa, tace " dan ....".
Bai saurare taba ya nuna mata kayan yace"yi waje dasu, wawiya kawai, ashe ba iya kanki ne baki killace ba, hatta abinci ma baki san yanda zaki sarrafashi ba".Simisimi kuwan ta debi kayan ta fita tana gunguni, da kansa ya shiga kicin din ya samarwa kansa abunda zai sawa cikinsa, sai yanzu yqke jin takaicin sallamar kukunsa, aganinsa ai mace zai kawo gidan ba shida matsala da abinci.
Irin wannan rayuwar ita take wakana agidan Malik, domin yanzu da kansa zai shiga madafa ya dafa abinda yake so iya cikinsa, ita kuma idan taga dama ta hada kwamacalarta taci, bai dame sa ba, kuma tun daga qannan lokacin bai kuma neman ta ba, domin ko kadan baya marmarinta, zabin Mqlam ce aransa, akanta kuma yake son ya fara jin yanda dandanon mace yake, kusan watansu biyu amman babu wata ko yar shakuwa data fara shiga tsakaninsu, ko yaushe daga tsawa sai hantara, idan ya mata hakan ita kuma mai makon yar kirsa da shagwaba sai dai ta wuce tana gunguni, ko kuma idan rashin kunyar na kusa haka zasu haukata gidan da cacar baki yana fada tana maidawa, sai idan ya gaji yai kanta dan makewa, ita kuma ta gudu dan ta san lafiyar jikinta.
+++++
"Oga ka fita harkata dan Allah ka barni na auri wanda nake so, indai dan ta 'yar ka ne ka dauki kayanka, amman dan Allah ka barni na shaki iskar yanci".
Bai kalle taba , bai kuma kula ta ba, sai ma surutunsu da suke yi da Simrah don yarinyar tayi wani mahaukacin sabo da shi, tashi tayi zata fice daga falon yace ,
" kina sa kafarki awaje, za ki ji sanarwar daurin auren mu kuwa dake, ki dawo ki zauna har sanda zan sallame ki".Zaman tayi kuwa tana sakin kuka, domin da irin wannan damar yake juyata son ransa, gashi kuma babu wanda ya isa yace mai bai yi dai dai ba, wanda ma yake dan jin maganarsa Malam Saje, to shi kuma tuni ya koma Dutse, dan haka yake mulkar kowa agidan yanda yaso, barin ma Mairoji taji labari.
+++
"Laura, kar ki sauka kasa na fada miki Ya Ahmad da matarsa.ne fa afalon, karki je kiyi abinda za'a ji kunya dan Allah, kuma fa wannan shigar taki bai kamata ki fita da ita ba".
Ko sauraren Ummie ba tayi ba ta fito ta nufi downstair.
Kallon bakinta da take cuna mai yayi yana murmushi, akan wai ya hana ta robar yaji data dauko akicin bayan tasa an mata wainar fulawa, ganin yana kallonta yasa ta kuma cuna bakin tana son fara mai shagwabar da ko yaushe take narkar dashi, bata ankara ba sai jin saukar bakinsa tayi cikin nata, ido ta zaro tana son tunasar dashi abangaren Mamah fa suke ba bangaransu ba, shi kuma yaki bata damar hakan, domin da gayya yai, yaga sakkowar Laura kuma yasan zuwa zatayi ta zauna musu kamar yadda ta saba ta sasu agaba, shi yasa yai hakan.
Sai daya gaji dan kansa sannan ya kyale ta, ita sai lokacin ta kuka da Laura din datayi suman tsaye, kunya taji ta kama ta amman sai ta share kawai ta dauki farantin wainar ta fice tana jifan Ahmad din da wani kallo daya sashi tashi ya bita yana sakin murmuahin zan kama ki ne.
Tabata da Ummie tayi shiya dawo da ita hankalinta, murmushi Ummie tayi tace " na fada miki ai karki sakko, duk kawaicin masoyannan yau kin kai su makura sun nuna miki abinda idonki keson gani, sai kije ki sauya shiga ai, wanda kikayi domin sa bai san kina yi ba, dan iska ne ke wahal da mai kayan kara".
Tsaki Lauran ta saki ta wuce dakinsa kamar ta tashi sama, iata gani take kamar da hadin bakin Ummie a wannan wulakancin da ake mata, daki ta shiga ta fashe da kuka mai cin rai, tare da alwashin sai ta kori Khausar daga gidan ita ta maye gurbinta.
YOU ARE READING
*RUGAR SAJE*
Non-Fictionsarkakiyar soyayya da zumunta mai hade da cin amana, shiga ciki ka karanta tsantsar soyayya, da tarin sadaukarwa.