*RUGAR SAJE*
By Nusaiba Ayuba Suleiman
Wattpad@nusysa
IG@Nusaiba A.S.Sarkin zango.*FITTATU 18📚 2 0 2 1💥*
⚖
*HOME OF QUALITIE'S WRITER'S ASSO📚*
'''{{The Home Of Qualitative Writers That Are Educate Humanities}}'''
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=106249334371950&substory_index=0&id=106248871038663&sfnsn=mo
*⚜️{{H.Q.W.A📚}}✍️*بسم الله الرحمن الر حيم.
_Deducated to my sweet Mamah😍_.
_18_
Bayan tafiyar K2 shiru tayi tana kuma yin tunani akan abinda yace mata, tabbas da gaskiyarsa kuma babu alamar wasa amaganarsa, ajiyar numfashi ta sauke tana kiyasta yanda zata faso gari itama nan da dan wani lokaci, murmushi ta saki tana jin kanta na wani juyawa.Bayan kamar kwanan uku ta gama yanke hukuncin daya mata, number din da K2 ya bata ita ta kira, bugu biyu kuwan ya dauka, bayan sun gaisa take fada mishi ita ce matar Malik daya bawa number rannan,
"Yah...ai na dau murya, yanda muryarki take da dadin nan ai ba za5ayi wuyar dauka aka ba, to ya kin yanke hukuncin ko kuma kinfi son kiyi ta zaman kunci kamar ajail?"." na gama yanke abinda zai fisshe ni, sai dai ni bansan dawan garin ba, kuma ba nida wasu kudi ahannuna da zan dan wataya dasu".
Murmushi yayi aransa yace "anzo wajen".A fili kuwa sai yace" haba dai, kina nufin duk kudin da ake bawa iyalan 'yan ball duk sati, ke baya baki naki, gaskiya Malik bai kyauta ba, amman kiyi hakuri zan masa magana, shigasa nace miki wannan zaman takura kawai kukeyi".
Ranta ya baci sosai, har hakan yaso bayyana ta muryarta,
"Ba sai ka masa magana ba, kyqle sa zan yi magana zuwa gida za'a turo min ko nawa nake bukata".Da saukri ya dakatar da ita yace" inaa....hakan bazai yiyu ba, duk amintar dake tsakanina da Malik ace iyalinsa na bukatar kudi sai ta nema agida, haba mutuncin ai baice haka ba, indai kudi ne zan kawo miki shi da kaina, duk yanda kike bukata".
Godiya ta shiga yi masa, yace "haba babu komai, ai duk yiwa kaine, abinda nake so dake kawai shi ne karki fada masa idan na baki, kinsan zuciya ba tada kashi, sqi kiga yana tunanin wani abun, kuma ni ba zanso hakan ba".
" kar ka damu ba zai sani ba, kawai dai ni ina son ka taimakamin na zama celebrity, so nake na zama abar kwatance aduk cikin family dinmu".Murmushi kawai yake dokawa yace"baki da matsala, gobe zaki ganni, ko zuwa yamma ne".
Da haka sukayi sallama, ya kashe wayar, tsalle ta daka tana ihun murna, daya daga cikin burikanta yana gab da cika, wai yan Maid zasu ga tsiya da wasali, tuni ta fara kiyasta yanda zataci uban kowa.
++++
Cikin abinda baifi sati biyu ba Sakeena ta fara zama irin yanda take so, kudi kuwan ba matsalarta bane dan K2 yana bata fiye ma da abindata nema, sannan kuma ya hadata da yaran turawa marasa kai, yarane da babu kwaba, dukkan su ta girme musu domin basu fi shekara sha tara ba, ita kuma tana da ashirin da hudu, haduwar su ya kuma sawa idonta ya bude sosai.Rananr da suka shirya zuwa wani show da za'ayi , sun biyo mata ne don duk cikinsu ita ce ba mota ahannunta, sau ran kowa nada ita, to idan suka shirya fita sai su biyo mata, lokacin Malik na zaune afalon yana waya da coach dinsu kan maganar siyansa da kungiyar Real Madrid zatayi, fitowa tayi ya kalle ta alama yai mata data koma, amman sai ta tsaya taki tafiya har ya gama wayarsa.
Kallonta yayi daga sama har kasa, wani wando ne da bai karasa idon sahun ta ba, sai wata farar riga mai spagetti hand, da itama bata karasa rufe cibiyarta ba, sai gashin da aka kara mata wanda ya saje da gashin ta kamar dama can nata ne, sosai kirarta da take fizgar yaya maza ta fito sosai, kai ya girgiza kawai ya dauke kai sannan yace mata,
"Ki koma ki canza wannan shigar, kar ki manta mu yaran musulmai ne bana kafirai ba".Baki ta tabe tayi gaba tana mita,
" ni na zata ma akan wani abu mai mahimmanci ka tsaidani, ashema akan wani shirme ne na daban, sai na dawo".
Da kallo ya bita, dan yanzu abindata tsira kenan, kuma babu damar ya mata magana zata fara masa fitsara, shi kuma abin daya tsana kenan, rashin kunya.Wajen ya kayatar da ita fiye da yanda take hasashen ganinsa, wani dan wajene suka shiga kamar falo haka, anan taga K2 da sauran abokansu kowa da babe din daya kama yana matsewa, da sauri K2 ya kamo hannunta ya zaunar da ita kusa dashi bayan ya sallami yarinyar dake tare dashi yace zai neme ta.
Kallon wajen take gabanta nadan faduwa, dan tunda take tantairancinta bata taba ganin anyi tarayya agabanta ba, amman yanzu kuma, mata ne ma suke neman junansu agabanta, banda mazan da suma wasu na aikata irin haka, da kuma masu tarayya tsakanin mazan da matan _(innalillahi waennailairrajioun, subhanallahi, yanzu fa abinda yake dawainiya da jama'a kenan, mace ta nemi mace, namiji ya nemi dan uwansa namiji, sai ka rasa wacce uwar sukeji idan suna wannan kazantar, ya Allah, ya Rahmanu, ya Gaffaru, ya Zuljalalu wal ikram, ya Rabbhissamawati wal ard, ya Allah ka tsaremu da tsarewarka, ya Allah ya karemu dan girman iyawarka, ya Allah karka barmu da halinmu, ya Allah ka tallafa amana, wannan zamanin Alllah ka bamu ikon danne zuciyoyin mu, kasa mufi karfin duk wani shaidanci da zai shiga idaniuarmu, da kunnuwanmu, ya Allah ka tsare mana bakunan mu da fadar shaidanci da sharri, Allah gamu gareka, wallahi iyaye ku tashi tsaye akan yaranku mata da.maza, kar kawa tazo wajen yarki kice mata wai shiga ciki ina jin barci take, ke kina tsakar gida kina aiki ita tanacan tana miki babban aikin da baki san dashi ba, ana can ana raruke miki yarinya, kusan awanni suna daka su biyu, sai ta tafi kina washe baki kina cewa wance dai Allah ya hada jin8nsu da wance, ai wance tana son yarnan, kai soyayyar da wance kewa yarinyar nan yawa gareta, uhmmm Umma! Mamah! Innah! Momy! Mamy! Ammy! Anni!!!, wllh kina zaine mace zata lalata miki yarinya, ba zaki tashi sani ba sai ta isa aure , ta fara korar samari, saboda duk cikinsu ba wanda takewa kallon wanda zai iya da ita sai yar iwarta mace, dan Allah iyayen mu ku tashi tsaye akanmu, ku dage mana da addua, ku na sa mana albarka aduk inda muke, Allah ya kara karemu)_.Kai ta kawai dan ko kadan tsantsani abin yake bata, wai mace tana shan pp din yar uwarta, kai ina...ita kam ba zata iya wannan kazantar ba, jin ana shafa ta yasa ta juya ganin k2 ne sai shinshinarta yake dan kanshin nata yai masa, kafin ta ankare ya kwantar da ita ya bi kai yana aika mata da wasu mahaukatan romansi, da fari taso tirjewa sai daga baya taga abin bana wasa bane sai ta bada kai.
Ba ita ta dawo gida ba sai dayan dare, shi ma kuma ba wai dan ta ishi k2 dinba, sai dan yasan halin Malik, idan yasan suna tare tsaf zai iya aikashi lahira, kuma ba yanda za'ai dan yana da daurin kugu da manyan kasar dama wasu kasashen.
Irin wannan rayuwar Sakeena ta daukarwa kanta, tsakaninta da Malik kuwa sai suyi sati basu hadu ba, daman shi baya ta tata, ita ce ma wani zubin take kokarin taga ta sanya shi a idonta kafin ta kwanta, ko kuma kafin ta fita.
+++++
A Dutse kuwa Mamah ta samu baban Mairoji da maganar zamanta a Maid, tunda su basu nema mata makaranta taci gaba ba, ai basa hanata auren wanda take so ba, da ya duba yaga maganarta akan hanya take da kansa ya taka zuwa Maidugurin ya taho da ita duk da rashin mutuncin da Saddiqu yaso masa kuwa, hakan bai hana ya taho da ita ba, kwanan su uku da zuwa juma'a ta zagayo, bayan sakkowa daga masallaci aka daura auren ta da Malik, wanda babu wanda yasan da hakan sai Malam Saje da Abbah, sai Kawu dake kano da Ammy, dan ko Mamah bata sani ba, bare ita Maryam Malik din.
YOU ARE READING
*RUGAR SAJE*
Non-Fictionsarkakiyar soyayya da zumunta mai hade da cin amana, shiga ciki ka karanta tsantsar soyayya, da tarin sadaukarwa.