*RUGAR SAJE*
BY NUSAIBA AYUBA SULEIMAN
WATTPAD@NUSYSA
I.G@NUSAIBA A.S.SARKIN ZANGO⚖
*HOME OF QUALITIE'S WRITER'S ASSO📚*
_(The Home Of Qualitative Writers That Are Educate Humanities)._
https://www.facebook.com/100495222137315/posts/100496042137233/?substory_index=1&sfnsn=mo*[📝I.W.A📝]*
بسم الله الرحمن الر حيم
_Deducated to my sweet Mamah😍_.
_36_
Sanda ta sauka amota, abakin get bugawa tayi mai gadi ya bude, kallon rashin sani yq mara, sannan yace mata wa take nema, jim tadanyi ko dai ta fadi sunan mai gidan ko matar gidan, ganin yana shirin komawa yasa ta yi saurin cewa mai gidan take nema.
Kallon tsaf ya.mata sannan ya ce ta jira, kamar mintuna biyar sai ga Saddiqu ya fito, kallonta yake cike da mamaki, dan kamar bata cikin nutsuwarta ne, rusunawa tayi zata gaidasa, ya dakatar da ita yace su shiga ciki tukun.
Sai daya bari tadan sami nutsuwa sannan suka gaisa, kallonta yake cike da neman karin bayani, ita kuma saita rasa ma ta inda zata fara, kame kame ta fara mai, ya tsaidata yace,
"Ina maigidan naki?, ina yaran na ganki ke daya?."
Kamar wadda aka daka, ta fashe mai da kuka, hankalinsa ne ya tashi yace "subhanallah Maryam mai yayi zafi haka, mai aka miki?."
Cikin shesshekar kuka tace "Ya Saddiqu ni dai na gaji da auren Ya Malik, kawai arabamu kowa ya kama gabansa, ni yanzu ma na fara tsanarsa, dan Allah ka saka baki su Abbah su raba auren."
Kai ya dafe yana ambatar 'innalillahi waenna ilairajioun, hasbunallahu waniemal wakeel'.
Kallonta yayi yace "Malik din yana can tare da yaran ne, ko tar koka zo kasar?".
Idonta ta goge tace" ah ah, ni kadai nazo, ba wanda yasan na taho ma acikinsu, kuma ni bana son susan ina nan."
"Kenan har yarannaki ma bakya so?."
Ya tambayeta cike da fargaba, kada kai tayi tace"ah'ah, ni ina son yarana dukansu, kawai shi ne bana son zama dashi, kawai ni dai ku raba auren, idan ba haka ba wllh daga nan ma gaba zan kara."
Shiru yayi yana kallonta, yama rasa mai ya kamata yayi, kayan nata ya dauka ya kai dakin Ummie, sannan tace ta shiga ciki ta huta, zai san abunyi.
Waje ya fita, nan ya kira Abbah ya sanar dashi duk abun dake faruwa, salati Abbah keyi wanda yaja hankalin Mamah take tambayarsa lfy, bai bata amsaba bayan su gama magana da Saddiqu, Ahmad ya kira ya sanar dashi komai, sannan ya kira Daddyn Yusra ya fada masa shima, nan suka tsaida magana akan zasu hadu anan Dutse washe gari dukansu, Ahmad ne dai saboda yanayin aikinsa sai dai yana tabasu awaya yana jin meke faruwa.
juyowa Abbah yayi yanawa Mamah bayani, zaman dabas tayi tana sakin kuka, mai hade da salati, da kyar ya samu ya lallabata akan karta bari yaran gidan su sani, baran Ummie sai abun yai mata yawa, fita yai daga gidan yama rasa ina zai dosa, bangare Malam Saje ya shiga, ya tarar dasu Khausar suna tare da Goggoji shi kuma Malam din yana dakinsa, kai tsaye dakin nasa ya wuce ya same rike da wani littafin addini yana dubawa, gaidasa yayi sannan anutse ya masa bayanin duk abubuwan dake faruwa, murmushi yayi kawai sannan ya janyo wani allonsa na karfe dake can gefe ya janyo tawwada da alkalami, gyara zama yayi ya fara rubutu, sai daya gama tsaf, sannan ya kalli Abbah yace,
"Yaran yanzu suna sakaci da addu'a, sun riki ilimin zamani kamar na zuwa lahira, su suna ganin basu da matsala da wani, amman mai fakonsu yana can yana zuba musu aikin da ba zasu iya maganceshi ba, ku tashe tsaye akansu, ku nuna musu muhimmancin addu'a, amman sakacin gaskiya yai yawa, duk da wani zubin akwai laifin ku iyaye, maganin baki, maganin mayu, duk bakwa nemawa yaranku, sannan idan aka hado yaro da asiri bakusan ku masa ayatusshafa ba, sai fmdai ku fara dana asibiti saboda kunfi yarda dashi, ba dole sammu ya samu waje zama ba, ya kamata dai ku kiyaye."
YOU ARE READING
*RUGAR SAJE*
Non-Fictionsarkakiyar soyayya da zumunta mai hade da cin amana, shiga ciki ka karanta tsantsar soyayya, da tarin sadaukarwa.