*RUGAR SAJE*By Nusaiba Ayuba Suleiman
Wattpad@nusysa
IG@Nusaiba A.S.Sarkin zango.*FITTATU 18📚 2 0 2 1💥*
⚖
*HOME OF QUALITIE'S WRITER'S ASSO📚*
'''{{The Home Of Qualitative Writers That Are Educate Humanities}}'''
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=106249334371950&substory_index=0&id=106248871038663&sfnsn=mo
*⚜️{{H.Q.W.A📚}}✍️*بسم الله الرحمن الر حيم.
_Deducated to my sweet Mamah😍_.
_13_
Bayan fitar ta ne sannan aka shiga bawa juna labarin bayan rabuwa, kiran sallahr la'asar ne ya tada su, matan bangaren Mama aka kaisu, yan matan kuma dakunan su Ummie, Laure yar rawar kai har ta samu abokiya dan tuni suka dinke da Sakeena, samarin ma bangarensu Malik aka kaisu, kowa dai da inda aka kaisa dan ya huta.
Bayan isha aka kuma haduwa, dan zuwa lokacin su Haj Tako sun zo, Mairoji da Ummie suna dakin Mamah dan can maman tace ta koma, shira suke cike da kewar juna, wayarta ne yai kara tana dubawa taga bakuwar lamba, kin dagawa tayi har kusan miss call biyar, sannan aka hakura da kiran, bayan kamar mintuna uku sai ga Mamah ta shigo kallon yanda sukayi baja baja akna gadon tayi ta girgiza kai tace"an hadu kuma, ba sauki sai na Allah, kije yayanku na kiranki, yace ki hada masa shayi da abu mara nauyi yunwa yake ji".
Kamar zatayi kuka haka ta tashi, ta daura hijab akan kayan baccin data saka, kicin ta shiga ta na tunanin me ya kamata tayi masa to, taliya tadauka, bayan ta dauko kifi a frige ta gyarasa ta dora akan gas, tana gama tafasashi ta dauko kabbage da yakan spieces, nan danan ta hada mai miyan kifi da kabbage, bayan ta dafa mai taliyar fara, tana juyewa taji an shigo, dubawa tayi taga Sakeena ce da Laure, dauke kai tayi dan tasan halinsu ba kai ne da su ba, yanzu zasu nemi yi mata tijara.
Ashe wai suma sun je nemantane dan Sakeena nason karban wannan card din na Malik, shi ne Mamah tace musu tana kicin.
Kallonta sukayi awulakance, Laure ta fara bude flaks din data gani arufe, kamshi miyarne ya daki hancinta, ta hadiyi wani mugun yawun kwadayi, dayan ta kuma budewa taga faran taliyace, wani faranti dake gefe ta dauka zata diba, dan bata bi takan Sakeena dake titsiye Mairoji ina katin yake ba, burinta kawai ta dibi abincin dan da gani miyarnan zatayi dadi.Dagowa tayi zatawa Sakeena tayin diban abincin, karaf idansu ya hadu yana aika musu da wani kallon idan na kama ku, da sauri ta ajiye farantin tana sunkui da kai.Sakeena ce itama ta kalli sashen da yake, cikin inda inda ta fara neman kare kanta, dan ya ganta ne dumudumu ta murdewa Mairoji hannu.
Bai musu magana ba, illa farantan daya diba da abin dazai bukata, fita yayi bayan yawa Mairoji kallo daya, ya dauke kai.Itama babban faranti ta dauka ta jera komai akai har da flaks din shayi haka ta raba ta gefensu ta fita.
Sai bayan fitar ta ne, sannan Sakeena ta sauke gwauron numfashi tace wa Laure"wllh gayennan karshene, ya gama tafiya dani, amman waccen shegiyar yarinyar da alama kanta na rawa, kuma zan saita mata shi, Malik ai mijin manyan yara ne ba, irinta kwailaye ba, ni fa kinga ko da bazai aureni ba, zan iya basa kaina, dan da gani zai bada wuta, Allah ya basa irin zubin da nake so ajikin namiji, wllh ko zan rasa komai na bazan yarda na rasa wannan hajar ba".
Baki Laure ta tabe tace"ai wllh duk haduwarsa bai kai yayan saba, tab....ke kinga Ya Ahmad kuwa, karshen kyau da haduwa".
"Au daman yana da yaya, amman ba'a nan yake ba ko, dan tunda muka zo ban gansa ba".
" yana da wa, wanda suke uba daya, babarsa kanwar Hajiyarmu ce, auren zumunci aka musu, amman ta rasu tun bayan ta yaye sa, sai dai fa yafi kanin nasa dadin sha'ani, yanada da dadin zama".
YOU ARE READING
*RUGAR SAJE*
Non-Fictionsarkakiyar soyayya da zumunta mai hade da cin amana, shiga ciki ka karanta tsantsar soyayya, da tarin sadaukarwa.