*RUGAR SAJE*BY NUSAIBA AYUBA SULEIMAN
WATTPAD@NUSYSA
I.G@NUSAIBA A.S.SARKIN ZANGO⚖
*HOME OF QUALITIE'S WRITER'S ASSO📚*
_(The Home Of Qualitative Writers That Are Educate Humanities)._
https://www.facebook.com/100495222137315/posts/100496042137233/?substory_index=1&sfnsn=mo*[📝I.W.A📝]*
بسم الله الرحمن الر حيم
_Deducated to my sweet Mamah😍_.
_28_
_MashaAllah, Alhmdllh barkan mu da karamar sallah,barkan mu da shan ruwa, Allah ya karbi ibadunmu, yasa muna daga cikin yantattun bayi_.Babu wanda yasan da dawowarsu sai Ahmad, sai suka bar abun amatsayin zasu musu ba zata ne, sati biyu dayin sallah suka tattaro gaba dayansu har yaran uncle din suka taho 9ja.
Ba tsammani kawai sai ganinsu akayi, Abbah ne ya fara yin tozali da kaninsa Malik, yayin da suka shigo gidan shi kuma yana niyyar fita, tsayawa yai yana kallon d'ansa malik da kuma kaninsa dako bayan daruruwan shekaru ne suka shude bazai manta dashi ba, bai dawo daga mamakin ganisa ba sai ji yai an rungume sa an fashe da wani irin kuka, cikin muryar da duk wanda yaji yasan mai ita dauriya yake kawai ya ce"Abdulmalik, kai ne yau agaba na, bayan tsawon shekaru yau gani gaka, na godewa Allah daya dawo mana dakai lfy, kuma iyayenmu zasu ganka kafin su koma ga mahaliccinsu."
Dagosa yai yana goge masa hawayen, yai dan murmushi yace"to kuma kai kana kuka, idan yaranka suka gani suma suyi ko, share hawayen mu shoga ciki ko?."
Gaba daya suka yi masauki ababban falo, nan danan aka fara bugawa yan uwan nesa dana kusa, ana sanar dasu dawowat Abdulmalik, kan kace kwabo tuni har jama'a sun taru sosai, Hajiya Tako ma tazo da nata tawagar, sosai ake cikin farin ciki baran ga dattijan su agefen su.
Cikin kwanaki kadan yan uwa duk sun zozzo an hadu an gaisa bayan kwana biyu suka shiryawa zuwa Maiduguri, sai dai banda Maryam , dan kamar cikinta jira yake suzo gida ya bayyana kansa, laulayi take sosai, to sai Mamah ta hana tafiya da ita, ba haka Malik yaso ba dan yana matukar bukatar matarsa akusa dashi, haka dai akayi tafiyar harda Khausar matar Ahmad.
Satinsu daya suka dawo, wanda ya rage sauran sati uku bikin Laura da Ahmad, sosai acan Rugar Na-ma'u Hajiya take shiri, gashi sun samu yanda suke so da Ahmad din, tatsarsa kudi suke kamar shi ne masarrafar kanta, abangaren Khausar kuwa Maryam da Mamah ne ke kwantar mata da hankali dan da fari taso daga hankalin nata, sai daga baya da suka mata nasiha da nuna mata muhimmancin karbar kaddara sannan ta samu ta nutsu, Sakeena kam dama bata dawo ba sai gab da bikinsu Laura sannan zata dawo.
Kwana uku ya rage afara shagalun biki yan Maid suka iso, harda Sakeena da mamanta, da yan dakinsu Saddiqu, sai dai shi bai zo ba sai ran daurin aure, sai dai tunda suka dawo Malik bai sanya Sakeena a idonsa ba, sai dai bai damu ba tunda shima yasan ba ta gabansa ne, matarsa da abin cikinta sune yanzu damuwarsa.
RANAR DAURIN AURE/BAKAR RANA.
Tun safe na tashi gabana na wata irin faduwa, kasa daurewa nayi na samu Mamah adaki ita da ummie suna shirya wasu kaya acikin kwalaye, zama nayi kusa da ita idona taf da kwalla nace " Mamah kamar bani da lfy, zuciya ta bugu take kamar zata fashe."
Juyowa tayi ta kallen, sannan ta zauna kusa dani tace"kina matsayin yar musulmai, wadda tasan addini, mai yasa ba zaki lazinci addua ba, ki tashi maza kina sakaci kwannan, na kula walhar da kike kinja baya da yinta, maza lkc na kurewa tashi kiyi sallah ki mikawa mai duka kukanki."
Ayanda naga tana magana, sai na kula kamar itama tana cikin yar damuwa ne, dan haka sai na tashi na nufi bandakinta nayo alwala, nazo na gabatar da walhar, sannan na zauna ina mika lamurana ga Allah tare da adduar samun sassaucin abunda ke shirin kusantoni.
YOU ARE READING
*RUGAR SAJE*
Non-Fictionsarkakiyar soyayya da zumunta mai hade da cin amana, shiga ciki ka karanta tsantsar soyayya, da tarin sadaukarwa.