*RUGAR SAJE*By Nusaiba Ayuba Suleiman
Wattpad@nusysa
IG@Nusaiba A.S.Sarkin zango.*FITTATU 18📚 2 0 2 1💥*
⚖
*HOME OF QUALITIE'S WRITER'S ASSO📚*
'''{{The Home Of Qualitative Writers That Are Educate Humanities}}'''
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=106249334371950&substory_index=0&id=106248871038663&sfnsn=mo
*⚜️{{H.Q.W.A📚}}✍️*بسم الله الرحمن الر حيم.
_Deducated to my sweet Mamah😍_.
Ina jin dadin comment dinki Mmnsadeeq, wannan rashin jituwa dake tsakaninki da Sakeena yai yawa alkur'an😅ga Addarmu yar bangar Saddiqu😊.
_22_
Watansu daya da zuwa ya fara shirin komawa, sai dai yace kuma da Maryam zasu koma, da fari Mamah taso hanawa don gani take babu abinda zata tsinta azamansu sai takura tunda duk sun girme mata, tasan kuma ayanda maryam din take da zurfin ciki ba lallai idan sun mata wani abun ba ta iya fada, Abbah ne tai magana dole yasa Mamah ta hakura ta fara mata shiri na musamman, ga bangaren Khausar da take tsumata da wasu kayayyaki, sannan Inna Ya kulo ma tazo garin, da kayayyakinta, haka suka sata agaba da gyararraki na ciki dana waje, wani abin ma idan aka bata, bata sha, sai ta faki idonsu ta boye idan ta samu sarari ta zubar.
Ranar laraba ya kama washe gari zasu tafi, tana kichen ita da Mamah suna suyar cincin da tace tana son zata tafi dashi, shigowa yai da sallama, freezer ya bude ya dau goran ruwa ya juya zai fita, kamar ance ta dago karaf suka hada ido, alama yai mata akan ta taso ta biyo sa, make kafada tayi tana tura baki, gani haka yasa shi yin gyaran murya yace"Mamah akawo min wannan kayan fulawan ahadon da shayi da wani abun dai mara nauyi"yana gama fada ya fice yana mata kallon zan kama ki ne.
Kallon Maryam din Mamah tayi tace"tashi to haka ki wanke hannunki ki hada mai abinda yake so, Allah ina kara tunasar dake ki yiwa mijinki biyayya kina kula da duk wani abu dayake so da wanda baya so, ina takaicin naga mace bata damu da sha'anin mijinta ba, walau bangaren cima, ko ban garen mu'amala, karki zama irin wadannan matan dan Allah dota, ki zamana ko kallonki yai kin fahinci mai yake mufi, yanzu kusan daya saura na rana amman ace tun karin safe, baki kuma kulawa da me mijiki ke bukata ba, ko yana dan sha'awar cin wani abun haka mara nauyi kamar yanda ya bukata, kema fa kin sani, dan kwallo ne, ko kadan basa rabo da ciyeciye, dan Allah ki kula kinji, bana son ina yawan shiga sabgarku ne kar aga wautata, amman yau kin sani dole nayi magana".
Kanta yana kasa haka ta tashi ta hada mai duk abin data san yana so, ta dora shi saman tire sannan ta nugi bangarensu, dai dai lokacin Sakeena da Laura sun taho kenan, su sun ganta amman ita bata gansu ba dan hankalinta nakan magamnganun Mamah, hankadeta da akayi shi ya sata dawowa hankalinta, gaba daga kayan hannunta sun tarwatse akasa, hatta flaks din shayin ya fashe komai dai ya gama bajewa akan tyles, dago idon ta tayi ta kallesu da murmushi akan fuskarsu ta bude baki zatayi magana, aka rigata da fadi,
"Bacewa mutane da gani, kina tafe kai asama kamar na dan tayin rakuma, ba dole ki zubarwa mutum abinci ba, ke komai ba kyayi cikin kula".Sim sim ta wuce tana jin hawaye na cika mata idonta, ta wutsiyar ido ya kalli Sakeena yadda take wani kayataccen mirmushi, kai ya dauke ya na kallon bayan Maryma da take shiga corridor din dazai kaita dakin Mamah, da gani kasan kuka take, ajiyar zuciya ya sauke sannan ya kalli Laura cikin tsare gida yace" ki hada kayanki yau dinnan basai gobe ba, ki kumo Rugar Na-Ma'u, na baki awa daya ki gama duk wani shirinki ki tafi, idan na kuma shigowa na ganki tabbas zaki tafi da karyayyun kafafu, wawiya kawai ballagaza".
Simsim itama ta wuce tana gunguni, tana fadin babu wanda ya isa korarta, dan tazo kenan sai dai azo batun aurenta da ya Ahmad, amman ita da Ruga sai ziyara idan tayi aure, dawo da kallonsa yai kan Sakeena data saki baki tana kallonsa, gyara tsaiwa yayi yace"me da meye aciki kwanukan da suka zube?".
YOU ARE READING
*RUGAR SAJE*
Non-Fictionsarkakiyar soyayya da zumunta mai hade da cin amana, shiga ciki ka karanta tsantsar soyayya, da tarin sadaukarwa.