A Alqur'ani Allah Ya siffanta duniya da mataa' a wurare da dama, wani shararren malami (na manta sunan) ya tashi ya shiga cikin kauyukan larabawa don neman asalin fassarar mataa' dinnan, a Cikin wani kauyen kayayau sai yaji wata yarinya tana cewa kunga karen can ya dauki mataa' a bakin shi, yayi ta bin Karen nan har ya same shi, ko da ya riske shi sai ya tarar da qunzugun tsumma na mata a bakin Karen nan!!!
A wajen Allah, duniya ba komai bace face qazanta.
Idan kana buqatar alkhairin duniya da lahira ka nema a wajen Allah madaukakin Sarki.Allah Yace bai dorawa kowacce rai abin da yafi karfin ta ba, to kenan duk wani abu da kika ga yana neman ya baki wahala, ki yi iya kokarin ki kuma ki duqufa wajen neman taimakon Allah.
Rayuwa ta na zuwa ma bawa ne daidai yanda ya dauke ta, in da zafi zafi, in da sanyi sanyi, in ya tsaya kuma a tsakiya hakan shi yafi.
YOU ARE READING
Aure bautar Ubangiji
Sonstigesnasiha akan zamantakewar aure A lokacin da mukayi niyyar yin aure yana da kyau mu san mene ne dalilin yin auren. Da farko ma dai mu fara sanin mene dalilin zuwan mu duniya? Allah Ya fada a cikin al-qur'an mai girma cewa " Ya halicce mu ne don mu ba...