Mijin ki

83 21 3
                                    

Yar uwa mijin ki daban yake da mijin wance ko Wacce. A shekarar farko da kukai aure ki yi hakuri ki ajiye I know my right ki nutsu ki fahimci waye mijin ki tukunna.

Maza kala kala ne kowanne da irin halayen sa (determined by environment) Wanda suka ginu daga irin alqaryar da ya tashi, gidan su, nasabar su, da kuma sanin ilimin addinin shi da sanin darajar dan Adam.

Nakan ji mata da yawa suna complain me yasa sai dai ayi ta ma mata wa'azin zamantakewa amman ba a yiwa maza? To babban dalili shi ne, mukullin zuciyar mijin ki a hannun ki yake, matukar zaki kasance mai kiyaye abubuwan da ya kamata ki kiyaye, ki nunawa mijin ki shi Sarki ne a fadar gidan shi to insha Allah zai mayar dake sarauniyar zuciyar shi.

Babu namiji mai cikakken hankali da zai kasance yana gujewa nauyin da Allah Ya dora masa. A farkon aure kowanne namiji yana kokari ya ga ya riqe ragamar gidan shi daidai gwargwado iya qarfin shi, to a irin wannan lokacin ne ita kuma mace take koya masa wasu halayen a bisa rashin sanin ta.

Maza sun kasu gida uku a bangaren kashe kudi, Akwai matsolo, Akwai almubazzari, akwai kuma wanda yake a tsakiya.

Amman kuma duka Sun yi tarayya a wajen son a girmama su(respect), a gode musu akan abin da suka kawo ko yaya yake, sanann kuma a nuna musu tausayawa a kowanne lokaci.

Idan kika fahimci mijin ki matsolo ne, to ba raina shi za kiyi ba, godiya zaki koya yi koda yaushe, ki na zabga masa addu'o'in Allah Ya kara budi ya sa a fi haka. Sannan kiyi ta roqon Allah Ya shirya miki shi. Ko abu kike so ya siya miki sai kin koya dabaru da siyasa na roqon miji, idan abin ma ba ya zama dole bane gwara ki haqura. Misali, "Ka ga, daman abu kaza ya qare ko kuma muna buqatar abu kaza, idan Allah Ya hore maka Don Allah Ka siyo mana".

Idan kuma mijin ki almubazzari ne, to ba zuwa zaki ke ga holy holy ba kina masa wa'azi ba, Cikin wasa da dariya zaki dinga nusar da shi, misali, yanzu da ka sa kudi me yawan nan ka siyo wannan abun da ma wanda bai Kai shi tsada ka siyo ba, sai kayi Sadaqah da sauran kudin ka ga za ka samu lada sosai" kuma kar ki sa shi a gaba kullum sai kin yi qorafi akan Al'amuran shi, A'a, idan kina haka zai dena Bari ma ki San yanda yake kashe kudaden shi. Shi ma kuma sai ki dage da yi masa addu'a domin zuciyoyin mu a hannun Allah suke, Allah Shi ne kadai zai shirayar da zuciyar bayin Shi.

To sai shi kuma dan tsakatsakiya, shi zai siyo komai a wadace amman baya son ya ga ana almubazzaranci. Shi ma wani lokaci akan samu matsala dashi wajen yin Sadaqah, saboda yana ganin ya lissafa iya lokacin da kayan amfanin shi za suyi masa saboda haka kar ayi masa gibi, an fi samun irin wannan matsalar da yan albashi (salary). Shi ma dai da siyasa da fadakarwa da kuma addu'a zaki samu ya dinga yin abun da ya dace a lokacin da ya dace.

A bangaren tausayawa miji, mata da yawa a kayan lefe suke faduwa wannan jarrabawar. Maza da dama suna ganin Sun sha wahala sun hada miki lefe, saboda haka bayan aure sai suce baza su siya miki wasu kayan ba. Wani kuma babu ruwan shi zai iya siya Amman dai gaskiya masu qin siyan su suka fi yawa.

To nidai a bangare na ban ga laifi a yin hakan ba, idan kin bar kayan me zaki yi dasu, ko kuma Idan kika kwashe su duka kika dinka daidai jikin ki sai kika zo kika samu ciki kikai qiba, qibar da ba lallai ki koma kamar yanda kike da ba Kinga shikenan kin yi asarar kayan da har abada ba lallai ki samu kamar su ba (duba da yanda muke cikin wani lokaci da kaya suke tashi a kullum) Kuma tun daga nan mijin ki ya qulla a ran shi lallai ke ba mai tausayi bace ba a gare shi.

Zaki ga har wasu tsofin wofi ne suke ma amarya hudubar kar ki yarda da Sallah yace ba zai miki kayan Sallah ba wai ki yi a kayan lefen ki, gobe ake ji nan gaba bazai yi miki ba Idan lefen suka qare. Gobe dai ta Allah ce, kuma da ke da shi babu wanda aka bawa guarantee din kai wa wata shekarar.

Saboda haka a koda yaushe ki zama mai duba yau, Halayen ki na yau su ne ma'aunin abin da zaki samu gobe.

A taqaice dai Idan kina son zaman lafiya da samun kulawa a wajen mijin ki to ki kasance mai girmama shi, tausaya masa da kuma yawan gode masa. Da yi masa addu'a a kan duk wani hali nasa wanda ba kya so, ki roqi Allah Ya shirya miki shi.

Yawan ibada da dogara ga Allah, yin Sallah akan lokaci, karatun Qur'ani, azhkar din safiya da yamma su kasance su ne tsarin rayuwar ki.

Kar ku manta da vote, comment and share saboda yan uwa su amfana !!

Aure bautar UbangijiWhere stories live. Discover now