Zaman Yara

91 16 5
                                    

Kuskure ne kice kina zaman yaran ki ne a gidan aure haka zalika Kuskure ne ka hana mace saki saboda ta zauna tayi maka rainon ƴaƴa.

Shi aure ibada ne, kuma ana son duk abin da mutum zai yi yayi don neman yardar Allah ne kawai.

A lokacin da kika zauna saboda yara kina ƙunsar baƙin Cikin mahaifin su, kwance tashi za a zo lokacin da zaki tsani yaran saboda sune musabbabin hana miki jin daɗin rayuwa. Sai kizo kina zagin su da hantarar su da dukan su akan laifin da bai kai ya kawo ba. A dalilin haka su ma yaran sai su fara tantamar anya ke ce Uwar su, su fara fatan dama tattarawa kikai kika bar musu gidan su. Har idan akai rashin sa'a su iya kallon ki suce su babu wata kulawa ta tsakanin ɗa da uwa da ta shiga tsakanin ki da su.

A ɗaya ɓangaren kuma shi ma mijin daman tuni ya fice miki a rai, sai ki fara yi masa fatan mutuwa idan da tsautsayi kece sanadin mutuwar shi kuma sai ki faɗa tarkon shedan ki kashe shi.

Babban abin lura a rayuwa, akwai perspective (yadda ake kallon abu). To mu dauki aure ibada, sannan hakuri dole ne a rayuwa, kuma Idan muka dogara kacokan ga Allah tare da kiyaye dokokin Allah to insha Allah babu wanda ya isa ya cutar da mu.

Muyi zaman aure saboda muna fatan ya zama sanadin shigar mu aljannah. Tarbiyya da kulawa da zamu yi ga yaran mu zamuyi ne don inganta rayuwar su, su zama masu amfani ga al'umma bai daya ba don mu kaɗai ba.

Da wasa kar mu dora expectations akan yaran mu wai su girma su cigaba da dawainiya da mu. Mu nema na kanmu, neman da zamu yi ta roqon Allah Ya sa albarka a Cikin shi ya zama me yalwa Ko bayan bamu da karfi ya zamana sai dai yaran mu su dora akan kulawa da harkokin mu, ba wai mu yanke ba su kuma su fara sabon nema.

Allah ne kadai Ya san gawar fari, zaki iya mutuwa ki bar su kuma dole wata tazo ta kula dasu, zaki iya kuma zama ki kula dasu sai bayan sun kawo ƙarfi sai kum Allah Ya dauke abin sa.

Shiriya ta Allah ce, arziqi na Allah ne, Kulawa da Kariya duka na Allah ne, kuma addu'ar mahaifiya a duk inda take mai riskar ƴaƴan ta ce.

Hakuri, tawakkali da kyakkyawar mu'amala su ne jigon jin dadi da nasarar Dan Adam!!!

Aure bautar UbangijiWhere stories live. Discover now