Matan attajirai da dama a qasar hausa suna fuskantar qalubale a wajen dangin miji har ma da nasu dangin, ana ganin su kamar marowata, wanda rijiya ta bayar amman guga ya hana.
Sai dai a cikin kusan kashi saba'in cikin dari abun ba haka yake ba.
Yawancin masu kudin nan da kuke gani zasu azurta iyalin su da ababen more rayuwa amman ba kasafai suke basu kudaden kashewa ba.
Wasu matan kuma ana basu amman saboda irin rayuwar da suka dauka ta almubazzaranci sai kudin ba zasu ishe su ba ballantana suyi kyauta.
Komai kudin dan uwanku ko mijin yar uwar ku don girman Allah kar ku zama masu matacciyar zuciya,ku tashi ku nema na kanku.
Dangin miji duk abin da kuke so a wajen dan uwan ku kusame shi kai tsaye ba sai kun jingina da matar shi ba. Idan kuma Allah Ya jarrabe shi da hatsabibiyar mata mai asiri har ta raba tsakanin ku to ku dage da yi masa adduoin neman tsari da karya sihiri.
Mata muji tsoron Allah, ki samu miji da haqoran shi talatin, iyayen shi sun gama shan wahala akan shi har ya zama mutum sai ke daga zuwan ki kice zaki shiga tsakanin su.
Komai nisan jifa qasa zai fado, shi sharri dan aike ne duk inda yaje zai dawo gida wajen wanda ya aike shi.
Allah Ka shirya mana zukatan mu.
YOU ARE READING
Aure bautar Ubangiji
Randomnasiha akan zamantakewar aure A lokacin da mukayi niyyar yin aure yana da kyau mu san mene ne dalilin yin auren. Da farko ma dai mu fara sanin mene dalilin zuwan mu duniya? Allah Ya fada a cikin al-qur'an mai girma cewa " Ya halicce mu ne don mu ba...