Yar uwa komai masifar namiji komai bala'in shi bai cancanci ki dinga yi masa tsoron da ya kamata ace Allah kadai kike ma irin wannan tsoron ba.
Matukar zaki ji tsoron saɓawa mijin ki Amman kina saɓawa Allah mahallicin ki kina qetara dokokin Shi, to kuwa kullum kina Cikin fuskantar qunci daga wajen mijin ki.
Ke dai ki kiyaye dokokin Allah, ki yi ibada ki kyautatawa mijin ki daidai gwargwado iya qarfin ki.
Ki dena jin tsoron duk wata halitta a duniyar nan ki roqi Allah Ya kare ki daga sharrin duk wani me sharri mutum ne ko aljan.
Suratu Aal Imran, aya ta 189--194, ki qoqari ki haddace wannan ayoyin tare da fassarar ma'anar su, ki karanta da daddare kina kallon sama kina tsarkake izza da buwaya ta ubangiji, insha Allah zaki kubuta daga tsoro kowanne iri ne.
YOU ARE READING
Aure bautar Ubangiji
Sonstigesnasiha akan zamantakewar aure A lokacin da mukayi niyyar yin aure yana da kyau mu san mene ne dalilin yin auren. Da farko ma dai mu fara sanin mene dalilin zuwan mu duniya? Allah Ya fada a cikin al-qur'an mai girma cewa " Ya halicce mu ne don mu ba...