Matsalolin Aure

664 35 0
                                    

Haƙiƙa mun samu kanmu a cikin wani yanayi na rayuwa wanda gidajen aure suke fuskantar matsaloli da dama.

Maza sun mai da zina ado, namiji bai san ya sauke haƙƙoƙin matar sa da suka rataya a wuyan shi ba. Sai hantara da zagi da cin mutunci.

Mata basu da godiyar Allah, sai raini, rashin kunya, gaasa, hassada da munafurci.

Kowa ba Allah a ran shi/ta.

Ya ke matar aure, daga ranar da kika shiga gidan miji, ki sawa ranki kin shigo ne domin ki samu aljannar ki ta hanyar bautawa Allah yanda ya kamata tare da kiyaye dokokin Sa.

Mafarin matsala

Ke ce baki san ki tashi kiyi sallah a kan kari ba, asubah sai ƙarfe bakwai zaki yi ta. Idan ma'aikaciya ce ki shirya ki fita, idan me zaman gida ce ki shirya ƴan makaranta su tafi ke kuma ki kunna TV ko ki jawo waya, ba karatun alƙur'ani, babu azhkar ɗin safe.

Sallar azahar da la'asar kuwa daman sai ƙarfe biyar zaki haɗa su kiyi ƙara'i.

Maghrib da isha sai kin zo kwanciya ƙarfe sha biyu.

Kwatakwata kin shagala da rayuwar duniya burin ki kawai ki sa latest kayan yayi, a ce ke wance ce ko matar wane ce.

Daman ita rayuwa cike take da jarrabwa, sheɗan kuma yayi alƙawarin sai ya kwashi abokan tafiya wuta.

Dole sai mutum ya kasance mai yin ibadah yanda ya kamata da yawan neman tsari daga sharrin sheɗan.

To kinje kin zauna sakaka, sai sheɗan ya samu dama akan gidan auren ku, ya jefa mijin ki a halin bin mata ko karayar arziƙi (misali), ko ke ki faɗa bin mallamai, a haka a haka har rayuwar ta lalace ayi ta yinta cikin ƙunci.

Shi kuma sheɗan buƙatar sa ta biya, kun yi two zero, duniya babu daɗi, sannan baku gina abin arziƙi da zai cece ku ba ranar lahira!!!

A kiyaye sallah a kan lokacin ta, kowacce a bata haƙƙin ta.

Babu wani abun daɗi a rayuwar duniya duk abinda ki ka samu sai ya gushe, ko kina tsaka da jin daɗin ke ki gushe ki bar duniyar.

Mu kau da kanmu daga ƙyaleƙyalen duniya muyi ƙoƙarin gina lahirar mu.....

Aure bautar UbangijiWhere stories live. Discover now