Yar uwa, qwaqwalwar ki ba wajen ajiye damuwa da matsaloli bace, a lokacin da kika shiga cikin damuwa ki dage da ibada kina fadawa Allah matsalolin ki. A mutanen da kike tare dasu ba zaki rasa wadda za ta zame miki abokiyar shawara ba.
Amman Idan kika riqe a ran ki saboda ba kya son a san halin da kike ciki, to idan qwaqwalwar ki ta gama daukar iya abin da zata dauka sai kuma ta fara tunkudowa waje ta yanda duk wanda kika samu kare da doki sai kin yi masa complain din halin da kike ciki, ko kuma ki zama psychotic (masifaffiya) saboda kin gama tolerating iya abin da zaki iya dauka.Karshe kuma mutanen da bakya son su san matsalolin ki zasu sani, gulmar ki da baki son ayi za ayi, har a qarshe a dinga cewa baki da hakuri baki da godiyar Allah, duk hakurin da kika yi a baya ba a gani ba.
Sannan kuma masu bata miki rai din da kike rufa musu asiri a qarshe zaki fahimci basu tantanci rufin asirin ba (they are not worth it)
YOU ARE READING
Aure bautar Ubangiji
Randomnasiha akan zamantakewar aure A lokacin da mukayi niyyar yin aure yana da kyau mu san mene ne dalilin yin auren. Da farko ma dai mu fara sanin mene dalilin zuwan mu duniya? Allah Ya fada a cikin al-qur'an mai girma cewa " Ya halicce mu ne don mu ba...