First impression (abinda kika sa wa zuciyar ki tun a farko) yana da matukar tasiri a rayuwar ki.
Saboda haka tun kafin ki aure ki sa wa zuciyar ki zaki samu dangin miji na gari, ko da bayan kinyi aure sai kika riski akasin haka, ki zama mai yawan uzuri.
Duk Wanda yazo miki da halayya mara kyau ki masa uzurin rashin lafiya a tattare da zuciyar sa.
Ki masa addua Allah Ya shirya shi kuma Allah Ya Kare ki daga sharrin sa.
Babu abinda addu'a ta bari a rayuwa, matukar zaki daga hannu ki roki Allah to tabbas ko ba dade ko ba jima Allah zai amsa miki.
Ki dauka dangin mijinki tamkar dangin ki ne ''yan uwanki.
Ki zauna da su tsakanin ki da Allah, ki kyautata musu iya kyautatawa. Da wasa kar ki zamo mai rowa a gare su, shi abin duniya a nan duniya za a barshi.
Idan sabani ya shiga tsakanin mijinki da yan uwanshi ko yan uba, babu ruwanki a ciki, idan baza ki iya hada kansu ba to kiyi musu addua.
Amman da wasa kar ki fara shiga fadan da ba ruwanki, ko haduwa kukai a hanya ki gaishe su idan basu amsa miki ba ne sai ki Dena gaishe su ko idan ran mijinki zai baci sai ki bari sai baya gurin ku gaisa.
Babu ruwanki da yi musu kallon banza ballantana akai ga sa'insa.
Ki dage da yawan rokon Allah akan Ya Kare ki daga sharrin masu hassada, bakin ciki da kambun baka.
Ga addu'o'i zan bayar :
A inda aka ce a ambaci Suna sai ki ambaci sunan duk wani Wanda ya sa ki a gaba: miji ne mai takurawa, ko mahaifiyar shi, ko yan uwanshi ne, ko makociyar ki ce, ko mahaifiyar ki ce ma.
Saboda shi sharri aikin shedan ne, wani baya sanin ma yana yi, to amman ai Allah Yafi karfin komai kuma shine kadai Yake Maganin cututtukan zuciya!!!!
YOU ARE READING
Aure bautar Ubangiji
De Todonasiha akan zamantakewar aure A lokacin da mukayi niyyar yin aure yana da kyau mu san mene ne dalilin yin auren. Da farko ma dai mu fara sanin mene dalilin zuwan mu duniya? Allah Ya fada a cikin al-qur'an mai girma cewa " Ya halicce mu ne don mu ba...