Haƙuri wata baiwa ce da Allah Yake bawa wasu zaɓaɓɓin bayi a cikin halittun Shi. Sai dai amman ko da mutum ya kasance mai zafin zuciya akwai hanyoyin da zai bi domin ya kasance mai haƙuri.
Babbar hanya ta farko ita ce addu'a, a ko da yaushe mutum ya kasance mai roƙon Allah Ya sassauta masa zuciyar shi ya rage saurin fushi. Mutum ya roƙi Allah Ya sa ya kasance mai haƙuri mai kyau (sabrun jamil) ba wanda za a dinga cutar dashi ba, haƙurin da mutum zai san haƙƙin sa ya kiyaye shi, haƙurin da mutum zai san darajar sa da martabar sa ta ɗan Adam, ya kare su ba tare da ya cutar da wani ba.
Haƙuri yana nufin idan an fi ƙarfin ka, ka kau da kanka ka roƙi Allah ya bi maka haƙƙin ka. Ka tsira da sauran mutuncin ka da ya rage ba tare da kaje kana ƙoƙarin yin faɗa ba har a kai ga wulaƙanta ka.
Haka zalika idan aka ce haƙuri, to ana nufin duk yanda ka kai ga son abu amman ka ga samun abun nan yana da matuƙar wahala to kai iya ƙoƙarin da zaka iya ka koma gefe ka zubawa sarautar Allah ido kana addu'a, matuƙar Allah Ya ƙaddara za ka samun wannan abun to fa zaka same shi ba tare da ka wahalar da kan ka ba.
Tsakanin haƙuri da rashin haƙuri tafiya ce ƙanƙanuwa ko ince lokaci ne ƙanƙani wanda da kayi haƙurin komai zai zo ya wuce.
Abu na biyu da zai sa zuciyar ka ta kasance mai haƙuri, a kullum ka/ki dinga faɗawa zuciyar ki/ka rayuwar kwatakwata guda nawa ce, duniyar ba matabbata bace. Saboda haka babu wani abun da zai ɗaga maka hankali a rayuwar duniyar nan.
Duk abin da zai samu ɗan Adam Muƙaddari ne daga Allah wanda mutum bai isa ya tsallake ba.
Komai yayi zafi maganin sa Allah, addu'a na da matuƙar tasiri a cikin rayuwar ɗan Adam, Wallahi kamar yanda Ma'aiki SallAllahu Alaihi wa sallam Ya faɗa "Addu'a ita ce takobin mumini" ya ɗan uwa ko ƴar uwa ki riƙe addu'a, kiyi imani da Allah duk rintsi duk wuya Allah ba zai taɓa mantawa dake ba, Kuma Allah zai amsa miki addu'ar ki a daidai lokacin da ya kamata ki samu biyan buƙata.
Babban ƙalubale shi ne haƙurin jiran lokacin da Allah zai biya miki buƙatun ki, sai ki dage da roƙon Allah Ya sanya miki haƙurin jure jiran.
Sannan yana daga cikin siffofin haƙuri kame baki daga yawan ƙorafi (complain) akan halin da mutum yake ciki. Mu koya wa harsunan mu yawan yi wa Allah godiya a duk halin da muka tsinci kanmu.
YA ALLAH KA AZURTA MU DA SABRUN JAMIIL!!!
YOU ARE READING
Aure bautar Ubangiji
De Todonasiha akan zamantakewar aure A lokacin da mukayi niyyar yin aure yana da kyau mu san mene ne dalilin yin auren. Da farko ma dai mu fara sanin mene dalilin zuwan mu duniya? Allah Ya fada a cikin al-qur'an mai girma cewa " Ya halicce mu ne don mu ba...