Allah maɗaukakin Sarki Ya faɗa a cikin Alƙur'ani mai girma "Allah bai ɗorawa kowacce rai ba face abinda zata iya"
Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi ya faɗa a cikin hadisi ingantacce "imanin ɗayan ku bazai cika ba har sai ya so wa ɗan uwansa abin da yake so wa kansa"
Da wannan nake son mata mu sani Allah Ya halicce mu da matuƙar daraja, sannan yayi mana sutura inda Allah Ya ƙaddara tsarin rayuwar mu a ƙarƙashin namiji.
Daga lokacin da aka haife ki har zuwa lokacin auren ki, kulawa da rayuwar ki ya rataya ne akan mahaifinki ko wani muharraminki (a yanayin da babu mahaifi).
Idan kikayi aure kuma sai wannan nauyin ya koma kan mijinki.
A yayin da girma ya kama ki ana fatan ragaramar kulawa da rayuwar ki ta koma hannun yaranki maza.
To a dalilin haka ya sa, a kowanne mataki na rayuwar ki ya kamata ki zama mai biyayya ga iyayenki da mijin ki sannan ki kare mutuncinki don ki zama abar alfahari ga yaranki.
Duk da haka Allah Ya jaddada nuna irin darajar da Yayi miki ta hanyar sanya ki a cikin kowace ibada da ɗa namiji zaiyi, hatta yaƙi Annabi (SAW) ya tafi da mata a lokacin sa.
Abinda nake so in nuna a nan shi ne, ƴar uwa ta duk abinda za kiyi a gidan auren ki kiyi don neman yardar Allah, kiyi saboda Allah Ya umarce ki da yin hakan.
Kowacce zuciya na san tana son a kyautata mata, tana son in tayi abun yabo a yaba mata. To amman sai ya zamana wasu mazan su ba haka suke ba, sunfi son a koda yaushe ke ki kasance mai kyautata musu ba tare da su sun kyautata miki ba, sannan basu iya yabo ba illa ma suna jiran laifi ƙalilan da zasu fara faɗa akai.
Saboda haka ƴar uwa duk wata biyayya da zaki wa mijin ki, ki masa tsakanin ki da Allah, kinga ko da bai yaba ba kin san ladan ki yana wurin Allah maɗaukakin Sarki.
Kar ki wa mijinki biyayya don neman tukuici, sai ki iya samun tukucin a nan duniya amman kuma baki da komai a lahira kinga anyi ba ayi ba kenan.
Indai kika tsarkake zuciyar ki kikai komai don Allah sai Allah Ya sa ki samu tudu biyu, mijinki ya nuna farin cikinsa har ya baki tukuicin, sannan kuma Allah Ya baki lada ninkin baninkin. Ga ladan yi don Allah sannan ga ladan sa mijinki farin ciki da kikayi.
Idan ranki ya ɓaci ki yawaita karanta a'uzhu billah, idan kina cikin farin ciki ki faɗi alhamdulillah, idan kanki ya kulle kin rasa abin yi ki dage da faɗin astaghfirullah.
Kiyi wanka ki kwalliya ki kalli kanki a mudubi kiyiwa Allah godiya da irin ƙirar da yayi miki, kar ki bari sheɗan ya zuga ki, ki fara tunanin ai dole mijinki ya rikice a kanki ko ai babu yake a cikin mata da sauran su. Ki wa kanki kwalliya don jin daɗin kanki, kinga ko da ya zo ya ganki bai tanka ba sai baza ki ji haushi ba.
Wasu mazan miskilancin su ya kai intaha, saboda haka wani fa sai kin masa magana, "wane baka ce nayi kyau ba. Wani zai tanka wani kuwa fa ko oho, duk da haka dai kar ki ji haushi kiyi imani Allah Ya baki ladan abinda kikayi.
Haka girki, da gyaran gida da kulawa da yara duk kiyi don Allah.
Duk abinda kika san zuciyar ki bata son shi kar kiyi shi don ƙoƙarin farantawa miji, ki bashi haƙuri kice baza ki iya ba.
Ƴar uwa darajar ki ta kai daraja, baki buƙatar neman soyayyar kowa sama da soyayyar Allah mai Girma da Ɗaukaka. Ki nemi soyayyar Allah sai Allah Ya sanya soyayyar ki a zuciyar mijinki.
Ƴan mata da basu da aure ku dinga yiwa kanku addu'ar Allah Ya baki miji na gari mai tsoron Allah wanda Ya san darajar ki da ta iyayenshi da naki.
"Rabbana aatina fiddunya hasanatan wa fil aakhirati hasanatan wa ƙina azhabannar" addu'a ce mai kyau wadda annabi (SAW) yace " hasanatan a duniya tana nufin mace ta gari/ miji na gari , saboda haka yana da kyau a dinga yinta kullum.
Aure ibada ne, rayuwa gaba ɗayan ta ibada ce, sheɗan kuma yana nan yana yawo don ƙoƙarin kawo mana cikas a cikin ibadunmu, sai mun dage, mun jure, mun cije, mun yi haƙuri da rayuwa sannan zamu samu farin ciki me ɗorewa.
Maza da mata mu dinga neman ilimin addini, har mutum ya koma ga mahaliccin shi ba ya gama sanin addinin shi. Musamman maza ku dinga zuwa karatun bayan maghrib da ake yi a masallatai, ku yawaita sauraron wa'azi.
A matsayin ki na mace ki ƙoƙarin sanyawa mijinki ra'ayin neman ilimin addini da yawan sauraron karatun alƙur'ani.
Ki kasance mai yi muku addu'a a koda yaushe, shashanci da jin kiɗa ba naki bane.
Wai wata ta taɓa faɗa min wai kallon finafinan da basu dace ba wai yana taimakawa wajen gyaran kwanciya, akuya da kaji da karnuka wa ya koya musu kwanciya???
Sheɗan yana samun wajen zama a gidajen da ake kallace kallace mara kyau da jin kiɗa da shigar banza.
Idan zaki cire sutura ki ce Bismillah.
Mata Allah Yayi mana sutura, don Allah mu dinga suturce jikinmu idan zamu fita. Kina tara wa kanki zunubai ne a ƙoƙarin burge maza da shigar banza.
Sannan a dena sa turare mai ƙarfin ƙamshi, zunubin zina fa ake rubutawa duk macen da ta sa turare ta fita dashi har wani namiji yaji ƙamshin yayi masa daɗi!!!
WALLAHU WA RASULUHU A'ALAM.
YOU ARE READING
Aure bautar Ubangiji
Randomnasiha akan zamantakewar aure A lokacin da mukayi niyyar yin aure yana da kyau mu san mene ne dalilin yin auren. Da farko ma dai mu fara sanin mene dalilin zuwan mu duniya? Allah Ya fada a cikin al-qur'an mai girma cewa " Ya halicce mu ne don mu ba...