Matar Ka

65 15 0
                                    

Ya dan uwa, matar Ka sutura ce a gare ka kamar yanda kake sutura a gare ta. Kamata yayi ace kullum kana gode mata da sa mata albarka saboda dumbin ladan da kake samu a dalilin dawainiya da kake yi da ita, sabanin yanda kake daukar wannan dawainiyar tamkar takura ce a gare Ka.

Akwai stage mai matukar muhimmanci da maza suke tsallakewa a lokacin da akai aure, wani saboda yana gudun raini, wani kuma saboda ya riga da yayi generalizing kan cewa mata ko me kayi musu ba zasu gode maka ba, saboda haka sai ya dinga kumbure kumbure da muzurai shi a dole ga mai gida.

A lokacin da kuka tare da matar ka, yana da kyau ka zaunar da ita ka fahimtar da ita samun ka da kuma irin dawainiyar da zaka iya dauka, kuma a nan kaji tsoron Allah ka nunawa iyalin ka kulawa daidai gwargwadon arzikin da Allah Ya hore maka ba tare da matsolanci ba ko kuma almubazzaranci.

Idan akwai nauyin yan uwa a kan ka ka fahimtar da ita. Ka kasance mai yawan hakuri da yi mata bayani a duk lokacin da kake ganin ta baude daga hanyar da kake so ku bi. Duk da haka kuma matar ka ta kasance abokiyar shawarar ka, (she is your wife for a reason), ba yanda za ayi ace kai kadai ne zaka dinga kawo tsarin yanda komai zai tafi a rayuwa ita ba ta isa tace komai ba. Annabi Muhammad sallAllahu alaihi wa sallam ma yayi amfani da shawarar mace, kuma ba a iya abinda ya Shafi zamantakewar gida ba kadai hatta al'amuran da suka Shafi aikin ka ko Kasuwancin ka.

Ba daidai bane da zarar matar ka tazo maka da zancen abubuwan da ake bukata na amfanin gida, ka hayayyaqo mata da masifa Ko ka bawa banza ajiyar ta, idan bata fada maka ba wa za taje ta fada wa? Ka yi mata bayani na fahimta idan kana da kudin siya ko babu. Kowacce rai tana son kalami mai dadi.

Ka kiyaye dokokin Allah, ka riqe ibadah, Ka qara hakuri, ka yawaita neman taimakon Allah, Sallah akan lokaci, azumin nafila, qiyamul laili, istighfari da salatin Annabi da karatun Alqur'ani!!!

Kar ku manta da vote, comment and share saboda yan uwa su amfana !!

Aure bautar UbangijiWhere stories live. Discover now